page 59

5.1K 284 49
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨








💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼









🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )















*WANNAN PAGE ƊIN SADAUKARWA NE GA ZAN SOKA A HAKA FANS GROUP GAƁA ƊAYA BAN GAJIYA DA MAKU KYAUTAR PAGE WALLAHI SABODA A KULLUM KUNA SANI NISHAƊI, KUSANI HAR ABDAN QUEEN BK BA ZATA DAINA YINKU BA, FATA DAI ALLAH YA BAR MU TARE YA KUMA HAƊA MU A GIDAN ALJANNAH, I LOVE U SO DEARLY GUYSS🤟🏼💋💋💋.*






Page5⃣9⃣



*SEEK WITH THE WEALTH ALLAH HAS BESTOWED ON US, THE HOME OF THE HEARAFTER, WE HAVE TO DO GOOD AS ALLAH HAS BEEN GOOD TO US.*






Asmah ce zaune tana shirya masu kaya a cikin ƙaton trolly ranta fari ƙal, Abdallah na gefenta ya kwantar da kanshi a kafaɗarta yana isar ta da surutai, cewa yayi "beauty kin ƙagara ki haɗu da habibtyta ne?".


"Ay baby ba ɗan ƙaramin ƙagara ba kuwa".

"Ai nima na ƙagara couz na daɗe ban ganta ba sai na riga ki ganinta".

"A'a sai na riga ka ganinta".

Abdallah yayi dariya yace "owk then lets bet to that" ya faɗa yana miƙo mata hanunshi da ya ɗunƙule itama dunƙule nata tayi ta buga mai.


Niko da naga yadda Asmah ke ta zubaba kaya a akwati nace to Asmah sai kace mai shirin hijira ko duk cikin ɗauki ganin Ummah ne😄.




#   #    #    #      #   #

Tun kan asuba Asmah ta nemi bacci ta rasa tashi tayi tayi sallah tana ƙara gode ma Allah akan agaji da yake kawo mata cikin lamuranta, haka tai ta salloli har aka kira asuba, ana kira Abdallah ya tashi da lalubenta dan shi daya tashi bacci ba wanda idanunshi suke so suyi tozali inba beautyn shi ba, ganin bai jita ba ya ƙyallara ido hango tan da yayi kan dadduma tana sallah murmushi kawai yayi ya faɗa toilet ya wanko bakinshi yayo alwalla kana ya fito ya shimfiɗa sallayar shi kusa da nata shima ya tada sallah da ta idar ta fara addu'oi, bayan ta gama ta shafa ta kalle shi da bai daɗe da gama sallame wa ba tace "Good morning hayati".



Tallafo fuskarta yayi ya riƙo leɓenta na ƙasa da haƙori yace "me yasa baki tashe ni ba nayi sallah?".


"Tuba nake ƴal laɓai naga bacin naka yayi ma daɗi kuma ma ban daɗe da tashi ba, na maka addu'a da yawa fa".

"To ni baki so inna maki addu'a ne?".

"Ina so sosai babyna".

Haka suka jera har kitchen yana taya ta aiki yau kam tsab yake tayata tana ta mamaki da sauyin shi kwana biyu tare sukai wanke wanke da goge goge shara da mopping suka gama komai Asmah ta kunna burner ɗinta nan da nan gida ya hau fitar da daddaɗan ƙamshi, sai da suka haɗa break fast suka jera sannan suka faɗa toilet tare sukai wanka suka shirya, kaya iri ɗaya suka sa, wata sky blue shadda ce aka ma Abdallah captan sai ita kuma doguwar riga da taji aiki tayi kyau sosai, tana gaban madubi tana zuba ƴan hannu a hannunta Abdallah dake zaune yana ta kallonta ya taso ya tsaya ta bayanta ya turo kanshi ta kafaɗarta yana zagaye mata ciki da hannayenshi yana faɗin "beauty kinyi kyau sosai".



ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now