page 69

3.4K 235 46
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨








💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼









🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))







_Itz_queenbk @ insta gram_





RAISE YOUR WORDS NOT YOUR VOICE, IT IS RAIN THAT GROW FLOWERS NOT THUNDER.
                   QUEENBK.....









Page 69





Asmah kam da duk ilahirin jikinta ke kyarma upon jin lamarin da Mahmud ya sani tarasa me ke d'awainiya da ita ne shin dad'i ne ko akasinshi dama ba ita kadai tasan wannan sirrin b'oyen ba, a lokaci guda kuma ta fara hango nasara na tare dasu, samun kanta tayi tana sujudul shukuru godiya sosai ta mik'a ma ubangiji Allah tuni ta fara zubar da k'wallan dad'i, Mahmud ta kalla tana murmushi tare da share k'wallanta a hankali ta fara fad'in,






"Alhamdulillah Masha Allah godiya ta tabbata ga ubangiji mai kowa mai komai hak'ik'a naji dad'i k'warai da gaske da kasan wannan batun ya Mahmud kamar yadda ka kwance mun sirrinka haka zalika nima yanzu zan kwance maka nawa sirrin mai cike da zallar tausayi, da dana sani dan wani abun ni na aikata shi da kaina amman a rashin sani, bazance al'ajabi ba saboda ka riga kasan wacece Auntyn yara.............".










A haka Asmah ta fid'e ma Mahmud biri har wutsiya dan gane da abunda ta sani tun zuwanta gidan daga k'arshe ta d'auko mashi system d'inta ta nuna mashi dukkan abunda tayi saving na munafincin da Auntyn yara ta ringa kitsawa, mamaki ne da al'ajabi suka cika zuciyar Mahmud fam, sai yanzu yake gani kyan shawarar shi ta fayyace ma Asmah batun dan ta fishi sani game da ala'marin kuma ma da da information d'in da kawai yake dashi zai yi amfani wajen yak'ar Auntyn Yara shi kad'ai to da tabbas zai fad'i k'asa warwas ne, dan ba zai iya cin galaba akan abokiyar hamayyar tasu ba, sai yanzu yake k'ara yabawa da basira, k'wazo da jarumta irinta Asmah lallai ba ko wacce mace zata iya abunda tayi ba, Kuma tabbas ya san yanzu ba ya da
d'ar ko shakku akan Asmah ko zata gaza yasan zata iya fiya ma da yadda yake zato, shima gode ma Allah yayi sannan ya kalle Asmah cike da yabawa da k'ok'arinta yace,











"Madallah da gimbiyar mata hakika himma, k'wazo da jarumtakarki sun birge ni, yanzu na tabbatar da samun irinki sai an tona lallai aminina yayi dacen mata wanda ya cancanci ya shimfid'a tabarma a waje a zo ana taya shi murna, bana da d'ar ko shakku akanki na yadda dake d'ari bisa d'ari Kuma tabbas najiyo k'anshin nasara a tare damu kuma yanzu ba tare da b'ata lokaciba za musa k'aimi akan inda muke so mu Sara dan da zafi zafi ake tank'wasa k'arfi, yanzu dai wannan evidence d'in dake cikin system d'inki dole zamuyi duplicating d'inshi zan kawo flash in kwasa nima in kuma sa a system d'ina yadda in an rasa a nan to akwai a nan, abu na biyu kuma zan gaya maki me na gani a zuwannan,













"Wannan matar da ki kai magana akai wanda take yawan zarya wajen Auntyn Yara kamar yadda kika zargeta haka nima na dasa mata ayar tambaya, a hankalce nake bin duk wani takunsu, in zaki tuna ranar alhamis d'in da ta wuce sun fita tare a cewar Auntyn yara zata je gidan matar wadda take kira da k'awarta ko, to na fakaici idon kowa nabi bayansu dan gani ko wani abu suke k'ullawa sai ko na jiyo babban sirri wanda ba k'aramin taimaka Mana zaiyi ba kuma na gama sarewa akan Auntyn yara dan ina da yak'inin bata da sauran imani a tattare da ita .................."
















ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now