page 29

3.6K 219 1
                                    

[15/01 7:05 am] 👸🏼Queen bk👸🏼:🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨





💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )







Ina godiya da soyayya da kuma kulawa da kuke ban, inayinku irin totally, Ubangiji Allah ya biya maku buk'atunku na alkhairi ameen💝💞💋

Halima zakari.
Golden babe. ((Queen bk novels group)).
Momin sultan. ((Bk fans group))
Momin khadijah. ((Bk fans group)).
Murjanatu d'an rima. ((mijina sirrina group)).
Maman maryam ((mijina sirrina group)).
Maman abdul ((Raheenat fans group)).
Umman radeeyah((matan alkhairi group)).
Maman twices ((matan alkhairi)).
  
Duka ina mik'o sak'on gaisuwata a duk inda kuke a fad'in duniyar nan ina kuma maku fatan alkhairi. 💞💝💋💘💕








Page2⃣9⃣



Asmah taba aminiyarta zarah labarinta, kuma labarim ya girgiza Zarah sosai, duk taji tana tausayin k'awarta ta, sannan tace wannan duk ba matsala bane dan danginsu basu k'yamar talaka, zata sanar ma Ya Aliyu, haka kuwa akai ta fad'a mashi ba abunda ya ragu cikin son da yake ma Asmah sai ma dai wanda ya k'aru ta sanadin tausayin da yake mata, kuma komai ya daidaita tsakanin masoya biyun, kullum da wuri ya ke zuwa makarantar tasu tun kan a tashi, ana tashi za suyi ta fira da Asmah har sai diraban su yazo d'aukarsu, nanne kad'ai lokacin da suke samun yin hira tsakaninsu, domin duk yadda Aliyu yai kan ta karb'a wayar da ya siya mata k'iyawa tayi, a cewarta bai dace ace su Ammie sun d'auke ta kamar d'iyar su ta cikinsu ba, sannan ace ita ta karya masu dokar gida ba, don dokar gidan ce ba mai rik'e waya sai ya kai SS class tukun, dole ya hak'ura da d'an lokacin da suke samu tare domin ba damar zuwa gida, yanzu ma zaune suke cikin mota Asmah na gaba, itako Zarah nacan baya tana buga game a tab d'in ya Aliyu, Aliyu ne ya k'ara kallon Asmah kana yace,

"Asmah, meye burinki, konace meye kike so ki karanta, anan gaba"

"ya Aliyu ni wlh burina bai wuce na zama malamar asibiti ba wato likita, in Allah ya tabbatar mun"

"Baki son course d'inmu kenan? "

"wai tab Engineering, ai saiku ya Aliyu, wannan ba course d'in mata bane"

"waya gaya maki? Abun ra'ayi ne kawai, kuma insha Allah ba zaki gama karatuba za'a aura mun ke, kya ida shi a gidana, dan ni bazan iya jira ba"

Taffin hannunta tasa ta rufe fuska, murmushi Aliyu yayi yanyin jin kunyar ta na burge shi, a zahiri yana son mace mai kunya, sai gashi ya had'u da wacce kunyar ta har tai yawa, don Asmah fulani sak, yace "to meye na kunya kuma dan kawai na fad'i wannan maganar?"

Bata cire hannunta a fuska ba ta cigaba da fad'in " kai ya Aliyu ba kai bane kake magana sai kace nid'in wata babba ce"

"hmmmm Asmah kenan b........ "

Da sauri ta bud'e marfin motar tana fad'in "sai an jima, gayanan anzo d'aukarmu"

A tare suka kwashe da dariya shida zarah, sai da zarah ta koma gaba kana ya jasu suka tafi gida.
a haka suke b'arzar soyayyarsu a hankali a hankali tana k'arfi suna k'ara shak'uwa da juna.



****  ****.*****.**** *****
Cikin gungurawar rayuwa  su asmah an gama jss3, a shekarar mak'erin budurci ya fara k'erata, yanzu an zama cikakkiyar budurwa, daka ganta kaga yaran hutu,  jikinta kullum cikin shek'i yake, kamar ka tab'ata jini yazubo, Asmah fara ce wadda har farin nata yaso yayi yawa, kyakyawa doguwa in maku na hausawa kowa yayi tsawo yayi rabin kyau, tana da manyan idanu (lulu eyes) sai dai tana lumshe su kamar mai jin bacci, barin ma in ta gaji ko tana jin bacci ko yunwa, sannan in taga abun mamaki, ko tsoro ko aka gaya mata wata maganar data bata hakan, sai ta zaro idon tana jujjuya su, tare da kad'a harshenta, tana da dogon hanci daidai misali, ga d'an k'aramin bakinta, sai dimple d'inta da yafi k'awata fuskarta wanda ko batayi dariya ba suna lotsawa, tana da yalwataccen gashin gira, sannan gashin kanta ba'a maganarshi don har gadon baya yake gashi bak'i sud'uk gashi virgin hair, tana da diri sosai,  duk kuwa da tsawonta, sama da k'asa komai zoizoi, barin ma k'ugunta tana da hips sosai, a tak'aice dai Asmah ta had'u in and out, up and down, firt class ce, yanzu maza ko ta ina kwararowa suke y'an set d'insu ne, in ta fito waje ne, kai hadda malaman su, ita abun har isarta yake, wasu dayawa ma ba son gaskiya bane duk k'ugunta ke yaudarar su, yanzu bata da aiki addu'a safe da rana, ga Aliyu akwai d'an banzan kishi, duk yadda yaso ya turo a san da zamanshi tak'i, yace to ko kwatance tamai yaje su gaisa, daya nace mata dole ta bashi adireshin gidan Auntyn nafy, shida abokinshi suka shirya suka je gaida Aunty Nafy, sun gaisa lafiya sun kuma fad'i manufar zuwansu sai dai ba k'aramin girgiza sukai ba jin cewa an ma Asmah miji, duk inda hankalin Aliyu yake to a tashe yake, nan ya fara mata magiya akan cewa wlh yana son Asmah so kuma mai tsanani, bai tunanin za iya rayuwa bata, sai da tace ita ba zata ma y'arta auren dole ba,  sai wanda take so a cikinsu, shi zata ba, kana hankalinshi yad'an kwanta sun mata alheri mai yawa kana suka tafi cike da k'warin gwiwar ai Asmah shi take so duk da wani bangare na zuciyar shi na cike da shakkun wani abun, in kuma ya tuna da cewa Asmah bata tab'a mai k'arya ba, kuma ta riga da tace mai bata tab'a soyyayya ba sai akan shi dan lokacin dasukai da jauro duk yarinta tayi dan lokacin bata san meye so ba, duk da haka dai ya k'agara su had'u dan yaji ko tasan da batun mijin da akai mata.

***   ****   ***  *****  ****
Su Abdallah an k'ara manyanta cikin shud'ewar shekaru, yau asabar ba makaranta, Asmah tayi part d'in ya Abdallah sai dai tun bakin k'ofa take jin k'arar kwanoni da glass, da sauri ta k'arasa ciki,  kitchen tayi direct don anan ne take jin k'ararrakin, tana zuwa abunda ta tarar ya bata mamaki sosai, domin ya Abdallah ne keta kab'o da kaya daga ma'ajiyarsu, kuma har tamanta yaushe da rabon da yayi kallar wannan, gashi duk ya jima kanshi ciwo a hannu da glass, bai masan ta shigo ba don aikin shi kawai yake,  da k'arfi tace " Ya Abdallaaah" juyowa yayi yana fuskantarta sai dai yau taga akasin murmushin da yake mata a kullum, domin fuskar shi a d'aure take ba walwala ko kad'an, wani irin kallo yake binta dashi wanda har ta manta yaushe rabon da ya mata kallar wannan kallon, a hankali ta k'arasa inda yake sannan tace "ya Abdallah mai ya farune,  ka duba yadda duk kaji ma kanka rauni" kallabinta ta cire ta kamo hannun nashi tanaso ta d'aure mai inda taga jinin yafi zuba, sai dai ga mamakinta jitai ya ingizata da k'arfi, ta fad'i k'asa har ta fasa baki, wasu maganganu ya rink'ayi wanda basu da kai basu da k'afafu, don bakasan ma me yake cewa ba, shi a dole yana masifa, itako Asmah sarkin raki tuni ta fara matsar k'walla tana rik'e bakinta wai zafi, sai da yagama masifar shi tas sannan ya zube k'asa can d'an nesa da inda Asmah ke kwance, a hankali ya rink'a fitar ta numfashi d'ai d'ai can kuma ya natsu, dubanshi ya kai inda Asmah ke kwance tana ta kukanta, zaro idanu yayi yana fad'in "Asmah me ya faru? " ko kulashi bata bai dan bazata jura wannan halin na Ya Abdallah ba, ya gama mata abu kana kuma daga baya yazo yana cewa wa ya mata,  ohh shi bai masan shi ke mata ba ko, kawai mutum ya tai rikid'a kamar mahauniya, da jan gwiwa ya k'araso inda take, yana zuwa ya d'ago ta gaba d'aya ya rungumeta yana k'ara maimaitamata tambayar shi, tare da shafa mata baya alamun rarrashi, itako Asmah wani yanayi ta shiga, domin sai da taji wani abu ya tsirga mata tun daga kanta har k'afafunta, k'ok'arin ture shi tayi amman ta kasa, dan k'ara matseta ma yayi a k'irjinshi yana fad'in "Asmah garinya bakinki ya fashe ne? ", itako abun ya bata mamaki domin da can baya batajin komai in ya Abdallah ya rab'eta, amman ko mai yasa yanzu ko da d'an yatsanta ne ya tab'a sai taji wani abu na mata yawo a jiki oho, bata san amsar tambayar ta ba,  duk yadda tayi kokarin ta kwaci kanta hannun ya Abdallah ta kasa, can taji ya saki ajiyar zuciya tare da d'ago ta a hankali, da sauri ta fara jan baya, hannu yasa ya k'ara jawota yana goge mata jinin da ke bakinta, itama kallabinta tasa tana d'aure mashi hanunshi, nikam nace da walakin goro a miya, ba'a dade ba likitanshi ya k'araso domin duba shi yai kicib'is da ganin abunda ya faru, bayan ya gama ma Asmah dressing bakinta ta hau gyara kitchen d'in.









A/N

#################
Prophet Muhammad PBUH,  said: The souls are lyk an army joined in d world ov sprit, whichever souls knew each other in dat world are attracted towards each other in this world, nd which ever remained distant and indefferent dey re disintrested towards each other in dis world.

---------SAHIH AL-BUKHARI




👸🏼Queen bk🖊......

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now