Page 72

3K 223 36
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨












💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼









🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))










_Itz_queenbk @ insta gram_











Page 72










Abdallah ne kwance a kan gado kamar mutum mutumi domin babu inda ke motsawa a jikinshi ita kuma Auntyn yara tana zagaye gadon da kaskon da ke fitar da wani irin yaji a hannunta babu wuta a ɗakin wani candle ne kawai dake kunne akan bedside drawer, cikin kiɗima Asmah ta isa bakin gadon ta tallafo kan Abdallah a hannunta tana girgiza shi tana faɗin,


"Ya Abdallana me ya faru da kai ne? me ta maka? dan Allah ka tashi kar ka tafi ka barni kamin magana kaji" ta faɗa tana ƙara girgiza shi ganin ko alamar tashi be yi ba nan ta zuciya tayi kukan kura ta faɗa ma Auntyn Yara dake tsaye tana kallonsu tun shigowar Asmai kuma babu alamun tsoro a tattare da ita ko kaɗan.











Wuyanta Asmah ta kama ta maƙureta sannan ta murɗe hannun dake riƙe da kaskon ta karɓe tare da buga shi ga bango tuni ya tarwatse, a haukace ta haɗa hannayenta biyu bisa wuyanta ta riƙe gam tuni idon Auntyn yara ya sauya kala zuwa ja dan ba kaɗan take jin zafin maƙurar ba kuma duk yadda taso ƙwatar kanta ta kasa, a haukace Asmah ke wujijjigata tana faɗin, "me kika mashi! nace uban me kika mashi sababba muguwa kawai ko an gaya maki duk wani makirci da kike ƙullawa a gidan nan ban sani ba to wallahi ƙaryarki ta sha ƙarya yau ko ni ko ke a gidan nan" nan ta ƙara ƙarfin riƙon da tayi mata a wuyan da ƙyar Auntyn yara tayi nasarar kamo nata wuyan ita ma ta shaƙeta a galabaice take faɗin,





"Ina sane da cewa kin san wasu kaɗan daga cikin abunda nake kuma bana tsoranki ba kuma na tsoron ki tona ni sai dai ina so ki rubuta ki aje ni shafa'atu nice ajalinki".








Cikin ƙaraji Asmah ke faɗin "ko kuma nice ajalinki ba, zan kuma shayar da ke ruwan mamaki mai ɗaci s........." wani wawan ƙulli Auntyn yara ta sakar ma Asmah a cikinta wanda ya haddasa ma Asmah sakin wata gigitattiyar ƙara tana dafe cikinta cikin jin zafi, Auntyn yara ta cigaba da faɗin "sai na fara ajalin abunda ke cikinki tukun" tana ƙara ƙoƙarin kai ma cikinta nushi, da sauri Asmah tai baya dafe da cikinta kwata kwata jiri ɗiɓar ta yake, Auntyn yara ko da keta huci kamar zaki tayo kanta a haukace muryar Ammie suka jiyo daga falo tana faɗin "wai meke faruwane?" take wani duhu ya mamaye idon Asmah luuuuu ta faɗi ƙasa.










***                  ***                     ***

A hankali ta fara buɗe idanunta, akan fankar da ke ta juyawa a ɗakin ta fara sauke su ji tai kanta yayi mata nauyi hannu ta ɗora bisa goshinta tana salati take duk abunda ya faru ya dawo mata tas a ƙwaƙwalwarta a hankali ta yunƙura ta tashi ta gane ɗakin Ammie ne take, a hankali ta fara karaɗe ɗakin da kallo ba kowa sai Abdallah dake kwance ɗayan gefen gadon hannunshi ɗaure da drip da sauri ta matsa gurinshi tare da kamo ɗayan hannunshi tuni ta fara zubar da hawaye tafin hannunshi tasa a fuskarta ta tallabe hannun da duka hanayenta cikin kuka take faɗin,






ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now