Page 75

3.6K 282 51
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨












💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼














🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))












_Itz_queenbk @ insta gram_
















Page7⃣5⃣









A hankali na buɗa ido na wani irin yanayi naji da ban taɓa jinsa a jiki na ba, na rasa gane a mace nake ko a raye shin me ke faruwa dani ne ni Asmah, ji nayi na tashi zaune daga gadon da nake kwance dan kwata kwata ba niyar hakan a zuciyata in taƙaice maku ji nake jikina na aiki da kansa ba tare da na sashi ba, a cikin zuciyata nake faɗin "ko dai yau ne daren?" wani ƙarfine ya dirar mun sanadin yin wannan tunanin take kuma duk wani tsoro dake zuciyata ya ƙaura, da sauri na tashi na isa gaban wardrove inda na ɓoye kayan na buɗe wani farin wando ne dogo wanda bai da matsatsi na sanya, wata ƙatuwar ƙwarya wadda aka huda aka sa mata igiyoyi na ɗauka na sa ciki na a ciki tare da ɗaure igiyoyin a bayana, rigar dana sa ma fara ce sai wata dana ɗora a sama mai kamar alkyabba amman gabanta a ɗinki yake kuma tana da wajen fito da hannu, ina cikin ɗaure igiyar hular rigar naji muryar Abdallah na faɗin,




"Zan biki" da sauri na waigo ina kallonshi kamin in buɗa baki inyi magana wani abu ya faɗo man a rai tunowa nai sadda Baba yawale ke ce man,




"In har Abdallah ya tashi yace zai biki to ki barshi ya biki".




Da sauri na matso kusa dashi ina dafa kafaɗar shi ina kallonshi ido cikin ido, ce mashi nayi "zaka bini amman da sharaɗi".




Kunnen shi ya jamun alamar yana ji sannan na cigaba "duk abunda ka gani kar ka sake kayi magana kar kuma kaji tsoro ko kaɗan kar ka gudu kar kayi ihu abunda kawai za kayi shine ka rinƙa faɗin la haula wala ƙuwati illah billah Allahu akhbar sai ka buga mashi wannan bulalar" na faɗa tare da jawo wasu fararen dorunai ƙarƙashin gado waenda suka sha rubutu da adduo'i kala kala, miƙa mashi ɗaya nayi ya amsa yana ɗaga mun kai alamun ya fahimta, wadrove ɗin na ƙara komawa na jawo wasu kaya wando da riga suma fararene dama Baba yawale ya bani incase ko Abdallah ya tashi yace zashi to na bashi kayan ya saka, zuwa nayi na miƙa mashi da sauri ya zira, kallonshi nayi alamun ya shirya? jinjina mun kanshi yayi alamun eh, hannuna na dama na miƙa mai alamun ya kama, nashi yasa cikin nawa runtse wa nayi da ƙarfi sannan na kalleshi nace "kar ka sake ka sakin mun hannu" haka muka jero kowa ɗayan hannunshi riƙe da wannan bulalar, muna fitowa daga ɗaki gaba ɗaya ƙwan lantarkin dake ɓangaren ya mutu ba abunda kake iya gani tsabar duhu sai hasken kayan mu kawai, a tare muka ƙara ƙarfin riƙon da mu kayi ma juna a hannu tsabar tsoro, nice nayi ta maza naja Abdallah muka nufi ƙofar kitchen muna zuwa nasa makulli na buɗa na tura amman sam ƙofar taƙi buɗuwa nan muka shiga turawa nida shi amman ko gezau, nice nace mu koma ƙofar gaba muna zuwa nan ma ƙofar taƙi buɗewa duk kuwa da yadda muka dage muna turata, muryar Baba yawale ce ta fara dawo mun a cikin kaina,







ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now