pahe 22

4.8K 299 10
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
_BILKISU ALIYU KANKIA_
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼






🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S ((Z.A.W))🖊*
{Gidan   zaman   lafiya  da amana   insha   Allah 🤜🤛}





PEOPLE CLOSE TO MY HEART❤ ALWAYS GET MY FIRST MESSAGE! AM SOO SORRY DEAR FOR D LATE MESSAGE, YOU ARE NOT CLOSE TO MY HEART WALLAH YOU ARE INSIDE, FELICITATION ON YOUR Q'URANIC MEMORIZATION DURLING😘 MAY ALMIGHTY ALLAH SHOWER U WITH LOT OF HIS BARAKA, NOOR, RAHAMA, TAWAKKAL, HIDAYA, KHAIR AND MANY MANY MORE OF HIS BLESSINGS, XOO SORRY FOR NOT COMING *HAWA'U MA'AJI* CNGRTX ONCE AGAIN DEAR LOL. Allah baki ikon aiki da karatun, ya d'ayyaba mana M.H 😁 musha biki aradu💃🏻💃🏻💃🏻 wanan page naki ne ki wataya abunki.










Page2⃣2⃣









Asmah ce zaune kan sallaya bayan ta gama sallah tana addu'ointa, yau da mamakin mafarkin da tayi ta tashi, don tunda ta baro *RUGAR* *NAGGE*  bata kuma mafarkin d'an mahukacin mutumin taba sai yau, kuma na yau d'in yasha banban da sauran, yana ta mata magiya akan wani abu ne wanda ta kasa fahimtar komai, take mafarkin ya fara dawo mata _"Asmah kar ki cuce ni, da ina ta maki magiyar kizo gareni don ki taimakeni sai kuma da kika zo kike son juya mun baya? miyasa?"_ 

_Wallah bangane me kake nufi ba? waye kai? me kake son na taimaka maka dashi? wane irin juya baya ne kake gudun in maka? kuma yaushe nazo gareka? nifa bansan ka ba! ban tab'a ganin kaba! dan Allah kabar yaudarata kana sani tunani kullum, in kana son nasan da kai ka bayyanar mun da kanka! in kuma Aljani ne kai ka taimaka ka rabu dani kar ka cutar dani dan giman Allah!_

_hmmmm, Asmah kenan ni mutum ne kamar ki, kuma kar ki tab'a kawowa zan iya cutar ki, domin ina matuk'ar k'aunar ki, kuma duk tambayoyin da kika mun amsar su na gare ki!_

_taya zakace amsar su na gareni, bansan komai ba kar ka rikita mun k'wak'wallwa._

_kiyi tunani ku........._

dai dai lokacin Mimi ta tashe ta na fad'in "ohhhh Asmah yau kece har an tada sallah baki tashi ba."

kuma kwata kwata hausar ta bai kawo mata ta had'a mafarkinta dana ya Abdallah ba ta samu ansa, ita dai tai addu'a ta fidda tunanin a ranta.


******"**********

Ta tashi ta linke abun sallar bayan ta shafa addo'ointa na safe, kicin ta nufa ta tarar uwar talle har ta iso, nan suka shiga girka brakefast, kunun gyada suka dama, sukai k'osai da honey pancakes, suna kammala girkin Asmah ta tafi don yin wanka ta bar uwar talle na kintsa kitchen d'in, ta fito cikin wata bubu gown d'in material royal blue me touchings d'in maroon colour, taje ta gaida Ammie ta amsan cikin sakin fuska tare da tambayarta ya ta kwana?
"lafiya lau Ammie" cewar Asmah

"d'iyata wai ni yaushe ne kike karyawa ne?"

"k'arfe sha biyu ne Ammie"

"tab k'arfe sha biyu sai kace cin abincin rana? to ban yadda da wannan sakacin ba sam, kina kai mashi ki dawo ke ma ki karya kuma kullum haka zakina yi kinji ni?"

"Eh Ammie naji zan kiyaye insha Allah bazan k'ara ba"

"To gwanda dai yafi, haka kawai za kija ma kanki ulcer!"


**      **     **

Tana zuwa ta tarar da Ya Abdallah a falo, yau kuma an tashi da wuri kenan ta fad'a a ranta, a fili kam tace "ina kwana ya Abdallah" had'e da durk'usawa, wata irin harara ya watsa mata tare da jan wani tsaki mai sukun, kana ya kawar da kanshi gefe, a ranta tace "tooo yau y'an rashin mutunci sun iso kenan"

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now