page 7

3.8K 256 2
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*NA*
BILKISU ALIYU KANKIA
_((QUEEN BK))._






🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITER'S*
( _Gidan   zaman  lafiya da   amana  insha    Allah)_🤜🤛





THE HEART DOES NOT FORGET, THE SPECIAL PPLE 4 WHOM IT CARES 4, U ARE INDEED REMEMBERED, *SEE SEE* *( ASIYA IMAM)*
U RE A VERY NYC FRIEND, NA GODE DA KARAMCI, QUEEN BK NAYIN KI SOSAI, THIS PAGE, IS YOURS DEAR, ALLAH K'ARA BASIRA.❤




Page0⃣7⃣




Haka kwanaki sukayi ta ja, Ma'u duk hankalinta a tashe yake, baffah nema yake kwantar mata da hankali, dan ta dage ta ida had'a sittin, ganin ta kusa, to cikin ikon Allah kuma, su ma'u an haddace, a ranar murna wajen ta, kar ku tona, baffah kam har ma ya fita murna, gani yake ya rik'e amana, tun da ya bata ilimin dako a lahira, shi zae taimake ta.

To rana bata k'arya sae dae uwar d'iya taji kunya, duk abun da aka samashi rana, hak'ik'a ranar tashi na nan zuwa, kamar yadda kowa an sama shi, ranar mutuwar shi, tun kafin a haife shi, kuma tana nan zuwa, tunda kullum k'ara matsowa ta ke, Allah kaba mu ikon aikata dae2, ka yafe mana kurakuren mu ameen,
yau za'ayi ma su Ma'u shadi.

Ma'u tun safe, ta kwashi kayan da zatasa, sabbin kayan da baffa ya suyo mata, ta d'auka ta gudu gidan su lamunde, don kar ma gwggo ta b'ata mata shirin ta, ta cab'a adon ta, tare da taemakon innah da lamunde, kayan fulani ne sak'i bak'i, kasancewar ta fara sae kallar ta k'ara haska fatar ta, ko ina ta zuba tsakiyoyi a jikinta, na wuya, na hannu, na kai, har ma da na k'afa, inar lamunde ta gyara mata gashinta, ba k'aramin kyau tayi ba su lamunde ,sae kod'a ta suke, haka suka jero ita da lamunde, da sauran k'awayenta, suka sata a tsakiyar su, suna tafiya, sae ta zamto tamkar zara a cikin taurari.

Suna isowa k'ofar fada, suka tarar da jama'a mak'il, maza da mata, duk anxo kallan shad'i, tauraruwar kawai ake jira dan kowa ya hallaru, gasu Jauro nan da Tanko a tsakiyar fili, sun sha wanduna 3- quater, basusa riga ba, kowa da y'ar sandar shi a hannu, sae Mal. Bala ( mai shela), dake tsakiyar su, su ma'u na shigowa, masu ganga suka saki kid'an k'oroso, mai nuna alamun sun iso.

Aiko kallo sae ya ko ma sama, wae b'era ya goyo giwa, kowa yana ta kallon Ma'u da tawagarta, nan waje ya d'auka da surutu caaaaa, kowa na fad'in albarkacin bakin sa, wasu kuma an saki baki, tana zuwa inda ya kamata, ta tsaya sae salon kid'a ya sauya, tanko ne ya taso daga inda yake tsaya, ya zo gabanta, k'asa2 yafad'a mata wani abu, ita kuma sae ta kauda kai, sae ya koma, jauro ma ya xo  daf da ita, a hankali yace, " kar ki yi kuka, ki ta murmushi, ta gyad'a mai kai tana murmushi, sannan ya koma wajen shi, a take mutane aka d'au sowa, saboda an gano wanda take so, da wanda bata so a cikin su, dama haka al'adar take.

Sae kid'i ya tsaya, bala yace, " to Allah ya kawo mu, ranar shad'in da muke ta jira ya zo sati biyu, da suka wace, to dan haka zamu gudanar da shad'i a al'adance, kamar yadda muka saba, to jauro ya yadda a fara dukanshi, don haka ta kanshi zamu fara, sai masu ganga, suka k'ara sakin sauti, wannan karan ma'u ce, ta taso daga inda take tsaye, tana karairaya da rausaya, kamar yadda taga manya matan nayi, in ana masu shad'i, ta zo dai2 gaban jauro, sukayi wata maganar kurame, sannan ta fuddo wani madubi mai kyau daga lalitarta, ta mik'a mashi.

Sanan ta koma wajen ta, shi kuma yayi akimbo, da hannu d'aya, sannan ya juya daga fuskantar ma'u , ya zamana cewa tana ta bayan shi, sannan da d'ayan hannun ya saito fuskar ta, ta madubin, ya tsince ta, tana mai murmushi, kamar yaddaya umarceta, shima murmushin yake, yana k'if2 ta idano, kar kafewar idanun yasa su fidda ruwa da kansu.

Aka ba Tanko izinin ya fara mashi bulalin, shiko tanko cikin zak'uwa ya shafa sandar tashi, wanda tasha tsibbace2, kala2, ya tako izuwa bayan jauro, sae da ya waiga, ya kalli ma'u, ya sakar mata wani murmushin mugunta, cikin rashin tausayi ya fara zuba ma jauro bulalar, wanda haka yasa kowa shiru, aka maido hankali gare su, ita ko ma'u har k'ok'on zaciyar ta, take jin bulalun, wanda har ya haddasa mata zubar hawaye, ta madubi jauro ke karkad'a mata kai.

Duk in anyi ukku sae an tsaya, bala yazo ya duba, ko idon jauro yayi ruwa ma'ana, ko yayi kuka, sae aga k'amas, saiyace aradu jauro bai yi kuka ba, sae ai ihu cikin murna, masu san shi kenan, a haka har akayi masa bulala 12, mutane dayawa sun yi mamakin kallar bulalar da Tanko, yayi ma Jauron, ganin yadda ya farfasa masa jiki sosai, gashi Jauro kamar ba shi aka daka ba, wasu make tausayin shi, ma'u ko ana gama dukan shi da gudu tak'araso gaban shi, ta zube a k'asa tana ta kuka, shi kema lalla shinta, shiko Tanko sae harararsu, yake ganin bai ci nasara sa Jauro kuka ba, duk da ya farfasa masa jiki bana wasa ba.

Bala yace, " to kamar yadda aka saba, yanxu za'a ba jauro sati biyu, ya warke ciwukan sa, sannan ya dawo ya rama bulalin shi, shima, daga nan zamu tantace gwanin ma'u a cikin su.
Da haka kowa ya watse,
yarorin jauro suka tallabo shi, suka nufi gida dashi, su ma'u  na biye da su, sai da suka shige gidan su dashi, sannan su ma'u suka juya suka nufi gida suma,
A haka takoma gida jikin ta duk a salub'e, ta tarar gwggo ta tafi yawan iskan ta, taji dad'i yau bazata fita kiwo ba, dan bafah bama ya nan, gashi ba tajin d'ad'in jikin nata, a haka ta kwanta ta shak'i baccinta.


A/N

****KEEP PRAYING, SMILE NO MATTER WHAT, AND STAY BLESSED.**
**

_QUEEN BK_

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now