page 58

5.1K 271 11
                                    

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )
















Page5⃣8⃣







Washe gari tunda sassafe Asmah ta gama shirya masu ita da Abdallah suka tafi gurin Ammie, a sashen Abbah suka taras da su duka hadda Auntyn yara, Abbah da Ammie sai washe baki suke kamar gonar auduga Auntyn yara ko kallo ɗaya zaka mata kasan yaƙe take, barin ma Asmah data san sirrinta ita kaɗai ke iya hango baƙin ciki kwance a ƙwayar idanunta, Abbah ba ƙaramin murna yayi ba da jin batun da Ammie ta zo mashi dashi, Auntyn yara ko da ta tsinkayi batun ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba gani take komai nata ya ƙara komawa baya lissafinta duk ya jagule, kallonsu kawai take tana yaƙe yadda suke murna.



Sun daɗe suna hira, su Abbah da Ammie na ta faɗa mata tarihinsu, ita ko Auntyn yara da baƙin ciki ya kai mata wuya tashi tayi tace kanta na ciwo shine Ammie ta bata magani tace taje ta kwanta, bayan sun mata sannu.



Yini zungur sukai suna celebration, wahsegari misalin ƙarfe ɗaya Mimi ta dawo daga hutu kasancewar hutu ya ƙare an kusa komawa makaranta ita ma da tsintar labarin ba ƙaramin farin ciki tayi ba yini tayi a part ɗin su Asmah, yanzu suka gano shaƙuwarsu dama ashe akwai ƴan uwantaka, sunji daɗi matuƙa, nan Ammie ta sanar da su Aunty Urwa amman ta masu gargaɗi akan kar su gaya ma su Naty da Aunty Nana tukun, haka sukai ta kiranta ana gaisuwa tsakanin ƴan uwa tare da jaddada mata kan cewa insha Allah suma suna nan zuwa zasu haɗe a maiduguri, ita ko ɓangaren Asmah ba ƙaramin murna take ba ganin yadda take da ƴan uwa birjik gasu da cikar haiba da kamala yanzu abu ɗaya idonta ke tsimaye shine ganin Ummanta wanda ji take kamar ta jawo sauran kwanakin da suka rage, ta sanar ma su Aunty Nafy suma ba ƙaramin farin ciki suka shiga ba har gida suka zo taya ta murna, su Marwan ma sun dawo gida haka suma har gida suka zo tayata murnar sabon farin cikin da take ciki da kuma na aurenta, tun Asmah na jin wani iri ganin Ya Marwan ya sake ya kawar da komai yasa ita ma sakewa ta cire duk wani abu a zuciyarta, sun ɗan sha hira kana suka tafi.





*BAYAN KWANA BIYU*

Shirye shiryen komawa makaranta ne gadan gadan ya barke tsakanin Mimi da Asmah ƴan Ss2 kenan domin hutun long vocation ya ƙare, su Ammie suka sanar ma da Asmah akan ta shirya zata koma makaranta domin Abbah har yayi ma principal magana yace ba wata matsala ta zo ta ida, duk ta gama shirya Uniform ɗinta kasan cewar gobe Monday kuma a goben ne zata koma duk ta goge kayan makarantar an shirya litittafai, shiko ɓangaren Abdallah bai san wainar da ake toyawa ba.





Washe gari da sassafe wajen karfe bakwai Asmah ta gama gyara ko ina ta shirya tsaf cikin kayan makarantar ta, zuwa tai ta kwanta jikin Abdallah da yake ta bacci hankalinshi kwance, tana kwanciya taji ya zagayeta da hannunshi yana mirginata ya koma shine a samanta, buɗa ido yayi yana kallonta, lakuce mashi hanci tayi tace "ashe dama ba abacci kake ba?".


Kiss ya mata a goshi yana goga kumatunshi a nata, tallafo fuskar shi tayi tace "Good morning my heart desire".


"Morning my beauty" ya faɗa yana cusa kanshi cikin wuyanta yana kissing yana shaƙar ƙamshinta.


ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now