Mai Nasara 1-5

4.4K 207 10
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

      1st JANUARY,  2019.

    
   Bismillahir rahmanirrahim.

Ina rokon Allah yasa yanda zan fara wannan rubutu lafiya na gamashi lafiya. Wannan littafi k'ageggen labari ne,  darasin da yake ciki Allah ya bamu ikon d'aukar sa amin.

    SADAUKARWA

  Na sadaukar da wannan littafi ga Mahaifiyata Allah ya k'ara mata lafiya da tsawon kwana,  ina matukar alfahari da ita,  Allah ya jikan Mahaifina da rahma amin.

Ina mika godiya ga dukkanin masoyana na kusa dana nesa,  wad'an da na sani da wad'an da ban sani ba,  Allah ya bar zumunci amin

Page 1 ➡ 5

Mairoji!  Mairoji!

Wai baki ga kwaryar maganin bane? Da sauri wadda aka kira da Mairoji ta shigo d'akin hannunta d'auke da kwarya tana fad'in Inna wuro gashi. Amsar kwaryar Inna Wuro tayi tana fad'in baki d'auko d'ayan  d'aurin maganin ba,  tare suke a cikin ragayar fa.

Zama Mairoji tayi tana fad'in baya ciki Inna Wuro. Tashi Inna Wuro tayi tana fad'in bari na duba ko fad'owa yayi,  ko kuma kece baki duba da kyau ba. Turo baki Mairoji tayi tana fad'in aradu Inna Wuro na duba,  fita tayi tana fad'in bari dai na dubo.

Da sallama wasu matasa guda biyu suka shigo d'akin, murmushi ne ya bayyana a fuskar Mairoji lokacin da taji sallamar su. K'ara duk'ar da kanta kasa tayi tare da amsa sallamar. Zama sukayi d'aya daga cikinsu yace Mairoji ya jikin Baffan? Kauda kai tayi gefe tace da sauki.

'Dago kanta tayi a hankali tana kallon d'ayan saurayin wanda tun bayan sallama baice komai ba ya zauna kusa da Baffa yana kallon yanda numfashin sa yake fita sama-sama.

Saurin d'auke idonta tayi ganin yana shirin d'ago kai. Inna Wuro ce tashigo tana fad'in Mai Nasara  da Bamanga har kun dawo? Murmushi Mai Nasara yayi yace Inna Wuro sannu da gida. Bamanga yace wallahi har mun dawo mun d'an tsaya fira a waje ne ma. Zama tayi tana fad'in sannun ku,  Allah yasa an dace?  Bamanga yace an dace,  amma sai zuwa jibi zamu tafi,  domin ance akwai wani wanda yake zuwa NAMTARI amma sai jibi zai tafi, idan muka isa sai mu nemi motar da zata kaimu garin mu can FUFORE.

Inna Wuro tace to Alhamdulillahi, ai komai yazo da sauki tunda tafiya ta tabbata,  sai fatan Allah ya kai ku lafiya kuma ya tsare gaba. Mai Nasara yace amin,  insha Allahu da munje muka huta bayan kwana biyu zamu zo da mutanan gidan mu domin suyi maku godiya, Allah ya bama Baffa lafiya.

Inna Wuro ta goge kwallar data tarar mata a ido tace amin. Mairoji ma k'ara dukar da kai tayi tana kok'arin maida kwallar da ta cika mata ido. Tana matuk'ar  jin son Mai Nasara kamar zai fasa kirjinta ya fito. Gashi zai tafi ya barta,  anya son Mai Nasara ba shine ajalin ta ba? Dama ana maida hannun agogo baya data maida kodan kada lokacin rabuwarsu yazo.

Tarin da Baffa yayi ne ya maidota daga tunanin da takeyi. Bamanga ne yayi saurin amsar kwaryar maganin da Inna Wuro ta gama motsawa,  Mai Nasara kuma ya d'agoshi suka bashi maganin. Bayan tarin ya lafa Baffa yace sannun ku da kok'ari,  Allah yayi maku albarka.

Suka ce amin sannu Baffa. Gyara jiginar yayi yana fad'in ban tab'a had'uwa da mutane masu kirki irin ku ba,  duk da mun kasance ba cikin gari muke ba,  asali ma bamu saba da mutane sosai ba,  kuna ganin yanda wajen namu yake ba wasu gidajen mutane ne da yawa ba,  amma had'uwata da ku sai nake jin tamkar nine na haife ku.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now