Mai Nasara 235-240

1.1K 86 7
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

Page 235 ➡ 240

Gaba d'aya wajen akayi shiru kowa yana sauraron abinda Baffa Barkind'o zai fad'a. Gyaran murya yayi yace Malan Liman a bud'e mana taro da addu'a........ Bayan Malan Liman ya gama addu'a aka shafa sannan Baffa Barkind'o ya gyara zama yana fad'in.....

Alhamdulillahi ina mai farin cikin sake had'uwar mu awannan taron wanda yazo mana a bazata. Hakika tunda Allah ya d'orani a wannan sarauta ban tab'a zama a taron da yake na bakin ciki ba sai wannan wanda zamu gabatar ayanzu.

Kuma ina fatan Allah yasa wannan taro ya zamo na farko kuma na k'arshe a wannan zuri'a tamu mai albarka. Gaba d'aya aka amsa da amin...... Cikin su Maina,  Baffajo da Laure gaba d'ayan su saida yayi wani irin k'ara.

Baffa Barkind'o yace da farko ina mai baku hak'uri abisa abinda zaku ji kuma zaku gani da idanuwan ku,  abun ya zama dole kowa ya sani ne shiyasa aka had'a wanna taron,  domin ba zaiyu ace arik'a aikata b'arna sannan ana lullub'eta ba saboda kawai a rufa ma masu aikatawa asiri.

Idan akayi haka ba taimakonsu akayi ba an zalince su,  domin duk wanda yaga wani yana aikata b'arna matuk'ar bai tsawatar mashi ba to tabbas shima yana da kamasho acikin b'arnar da yake aikatawa.

Ba sai na sake mai-maita maku abubuwan da suka faru a gidan nan ba na b'acewar su Mai Nasara da Bamanga ba, domin babu wanda bai san da wannan labari ba,  munso tun a wancan lokacin mu gabatar da bincike sai kuma na bada shawarar ayi hak'uri a barma Allah komai,  nayi hakan ne saboda bamu da wata madafa da zamu fara dafawa wajen yin bincike,  ganin koda an fara bincikin wahala za'asha yasa nace kawai abarshi.

Bayan dawowar su Mai Nasara wasu daga cikin mu sun so ayi bincike anan ma nace abarshi,  domin Allah baya barci,  kuma mun mik'a al'amuran mu agareshi na tabbata wata rana zaiyi mana maganin komai.

Bayan dawowar su Mai Nasara an rik'a samun abubuwa da yawa,  wanda wasu sun sani wasu kuma basu sani ba,  aciki hada abinda ya faru yau da safe. To Alhamdulillahi cikin hukuncin Allah komai yazo k'arshe,  kamar yanda na fad'a maku mun kai kukan mu wajen Allah,  to gashi nan Allah ya amsa mana addu'ar mu,  dan haka ina buk'atar kowa ya nutsu domin yaji abinda zan fad'a,  kuma bana buk'atar wani tashin hankali bare kuma wata hayaniya,  koma menene inaso ajira aji irin hukuncin dazan yanke.

Duk'ewa k'asa Maina yayi yana wani irin kuka,  gaba d'aya mutanan wajen suka juya suna kallonshi cike da mamakin dalilin kukanshi. Inna Yawuro kuwa gaba d'aya jikinta ne yayi sanyi,  nan take idanuwanta suka fara fitar da hawaye,  domin ta tabbata asirin Baffajo da Maina ne ya tonu.

Baffajo kuwa rufe ido yayi shima hawaye suna zubo mashi,  gaba d'aya jikinshi yayi sanyi,  jiyake kamar ya tashi yabar wajen dan baya fatan a fad'i wani abu yana zaune.

Gyaran murya Baffa Barkind'o yayi yana fad'in zan fara da kai Baffajo..... Saurin d'ago kai Baffajo yayi yayin da cikinshi ya bada wani irin sauti...... Baffa Barkind'o yacigaba da fad'in kafin nace wani abu zan fara cewa kaci amanar zumunci,  kuma kaci amanar d'an uwanka wanda ya bar maka amanar 'Danshi a hannunka.

Baka dace da zama Uba nagari ba,  idan ko haka Uba yake tabbas da kowa yayi asarar samun Uba,  da ace haka ake rik'on maraya da yanzu baka kawo wannan lokacin ba,  domin kaima maraya ne,  ka girma ba tare da kasan wacece mahaifiyar ka ba,  baka san waye Mahaifinka ba.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now