Mai Nasara 15-20

1.4K 82 2
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 15 ➡ 20

Lokacin da suka isa cikin tashar da zasu hau mota basu isa da sa'a ba,  domin suna zuwa motar ta cika,  hakan yasa aka d'auki sunan su akace suje cikin rumfa su jira asa wata motar idan ta cika sai su tashi,  basuji dad'in haka ba,  haka suka nufi cikin rumfar suka zauna.

Mai Nasara yace Mairoji kina jin yunwa?  Kai ta girgiza tana wasa da hannunta kanta akasa. Majidad'i yace ki fad'i gaskiya dai,  murmushi tayi tace Allah bana jin yunwa. Mai Nasara yace shikenan,  kafin mu tafi sai muci abinci tunda naga azahar ta kusa.

Haka suka zauna har aka kira azahar,  mutanan cikin motar basu fi goma ba,  ga motar Bus ce,  tashi sukayi suka nufi inda aka keb'e domin yin alwala,  kud'in shiga band'aki suka biya,  bayan sun fito suka nufi wani waje da ake sallah.

Mai Nasara yace Mairoji muje sai ki tsaya daga gefe kiyi taki,  idan kin tashi raka'a hud'u zakiyi,  idan kikayi azahar biyu saiki sallame,  sai ki tashi kiyi la'asar itama raka'a biyu saiki sallame,  domin bamu san ko kafin mukai gida ba'ayi la'asar ba tunda babu wanda yasan tafiyar mu,  wannan sallah ita ake cema (K'ASARU)  Wato sallar matafiya.

Kai ta d'aga ta wuce domin ta gabatar da sallah. Bayan sun gama Majidad'i yaje ya siyo masu abinci,  anan suka zauna sukaci sannan suka cigaba da zaman jira. Sai wajen karfe ukku sannan motarsu ta cika,  godiya suka ma Allah suka tashi.

Tafiya suke kamar ba tafiya suke ba,  domin Allah ya had'asu da tsohuwar mota,  gashi direban motar kanshi ya manyan ta,  haka yake tuk'a motar kamar mai jin tsoronta,  bayan sun baro cin gari motar tayi zafi,  haka aka tsaya sai da aka zuba mata ruwa sannan suka cigaba da tafiya.

Sosai ran Mai Nasara ya fara b'aci saboda yanda direban motar yake tuk'a motar,  ji yake kamar ya amshi tukin. Mairoji kuwa tana daga baya kwanciya ma tayi da haka bacci ya d'auketa,  motsi kad'an Majidad'i sai ya juya ya kalleta har Mai Nasara ya lura dashi.

Juyawar da zai k'arayi Mai Nasara yasa hannu ya maido masa da kanshi. Murmushi Majidad'i yayi yana fad'in to 'yan sa ido,  Mai Nasara yace naga ba ita d'aya bace mace abaya,  akwai matan aure,  idan ka bari wani yaga kana waigawa sai ya d'auka matar sa kake kallo. Majidad'i yace to babu wacce nake kallo ina duba bayan hanya ne.

Mai Nasara yace naga alama. Majidad'i zaiyi magana suka ji motar tana cijewa. Tsaki Mai Nasara yayi yana fad'in an kuma. Gefen titi direban ya sauka yana fad'in kuyi hakuri wallahi bansan abinda ya samu motar yau ba.

Wani da yake gefe yace kaima dai Tsoho kamata yayi kafin ka hau mota ka rik'a sawa a duba ta,  yanzu tsayawar mu biyu kenan. Direba yace kuyi hakuri bansan da wannan matsalar ba shiyasa.

Fita yayi ya duba sai yaga motar ce ta k'ara d'aukar zafi,  dan yana bud'e gaban motar yaga injin motar yana hayaki. Hannu yasa ya dafe goshinsa,  komawa yayi cikin motar ya d'auko galan d'in da yake zuba ruwa,  yana d'aukowa yaji kwalam babu ruwa.

Salati yayi gashi a cikin daji suke sun baro gari sosai. Lek'awa yayi yana fad'in dan Allah kuyi hakuri wallahi motar ce take d'aukar zafi shiyasa ruwan cikin lagireton yake saurin konewa,  gashi yanzu ya k'are kuma na duba galan d'in ashe ruwan ciki baida yawa shine na juyo d'azu.

Gaba d'aya motar ta d'auki korafi,  haka suka fito daga motar kowa da abinda yake fad'a.  Gangarawa sukayi kowa ya samu kasan bishiya ya zauna suna jiran agama gyaran. Mai motar ne da yaron motar suka gangara cikin dajin domin su d'ebo ruwa.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now