Mai Nasara 240-245

1.4K 66 0
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

Page 240 ➡ 245

Kafin wani lokaci kamannin Maina sun canza,  idanuwanshi kamar garwashi,  fuskarshi lokaci guda ta kumbura,  hannuwanshi duka rik'e da kanshi haka yayi ta juyi saboda bai tab'a shan k'waya irin haka ba,  a hankali jikinshi ya fara saki nan take bacci mai nauyi ya d'aukeshi.

****

A b'angaren Hajjo kuwa tun tana kuka da hawaye har ta koma shashsheka,  gaba d'aya ta rasa abinda yake mata dad'i,  ta rasa ta ina ma zata fara kallon Falmata da Mairoji,  har gara Mairoji ma batayi mata rashin mutunci kamar Falmata ba.

Ashe duk wannan abun da take akan Maina ashe shine babban munafuki,  ya rusa mata rayuwa,  yanzu idan mahaifarta ta lalace shikenan ya gama da rayuwarta.

Kwanciya tayi tana tunanin hukuncin daya kamata ta yanke akan Maina. Tana matuk'ar ganin girman Baffa Barkind'o da Inna Yawuro bazata iya tafiya tabar gidan su ba,  domin tasan tana tafiya zasuyi zargin dole ta fad'ama Kaka Tabawa dalilin komawar ta gida.

Tasan halin Kaka Tabawa dole ta tsareta sai ta fad'a mata dalili,  idan tayi k'arya tasan dole ta maidota,  ita kuma ayanzu bata jin zata k'ara zama da Maina a matsayin miji.

Saurin tashi tayi dan jitayi gaba d'aya gidan ya fita ranta,  akwati ta d'auko ta shiga shirya kayanta aciki, duk wani abu da zata buk'ata sai da ta zuba kafin ta saka hijabinta ta bud'e dakin ta fito.

Tsaye tayi afalo tana kallon d'akin Maina,  wani bakin ciki ne taji ya k'ara rufeta,  da sauri ta bud'e k'ofar falo ta fita. Tsaye tayi awaje jin gaba d'aya gidan yayi tsit saboda dare yayi. A hankali ta fara tafiya zuwa b'angaren Inna Yawuro.

A bakin k'ofar gidan ta tsaya ta dad'e kafin tayi k'arfin halin bugawa. Inna Yawuro tana d'aki tana jimamin abinda ya faru ta jiyo k'arar buga k'ofa,  saurin tashi tayi ta fito tana tunani waye yanzu kuma.

Tana bud'e k'ofar taga Hajjo tsaye da akwati. Hajjo tana ganinta sai kuma taji wata irin kunya ta rufeta,  wannan ai abun kunya ne,  ta guji d'anta kuma tazo wajenta ta bata makafa.

Saurin duk'ar da kanta tayi hawaye suna zubo mata. Ajiyar zuciya Inna Yawuro ta saki kafin tace Hajjo lafiya ina zakije a wannan daren?  Shiru Hajjo tayi sai kawai tasa kuka. Inna Yawuro tace shikenan ya isa kiyi hak'uri shigo daga ciki.

Kunya ce ta k'ara kama Hajjo sai kawai taji bazata iya shiga ba,  d'ago kai tayi tana fad'in dama wajen Inna Dije zanje shine nace bara nazo na fad'a maki. Murmushi Inna Yawuro tayi tace bazaki shigo nan ba kenan,  ko nima haushina kikeji?  Da sauri ta girgiza kai.

Inna Yawuro tace kiyi hak'uri kinji Hajjo,  nasan an b'ata maki,  kuma bazan hanaki d'aukar kowane mataki kikayi niya ba,  domin ko wace mace akayima irin abinda akayi maki dole ta d'auki mataki,  kada ki damu kije wajen Inna Dijen kinji.

Kai Hajjo ta d'aga tayi saurin juyawa tana kuka. Inna Yawuro sosai take tausayin Hajjo,  domin ita sheda ce akan irin son da take ma Maina,  juyawa tayi ta rufe gidan dan ko kad'an bataji tausayin Maina ba,  domin ya can-canci fiye da haka,  gara kowa ya k'yaleshi har saiya gane rayuwa.

Hajjo tana zuwa ta bugama Inna Dije,  ba'a jima ba aka bud'e,  mamaki Inna Dije tayi ganin Hajjo da akwati,  da sauri ta kamota suka shiga ciki ta rufe gidan.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now