Mai Nasara 150-155

1K 62 1
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 150 ➡ 155

Washe gari haka su Baffa Lamid'o suka nufi gidan Malan Garbati,  bayan da sukaje suka aika yaro yayi masu sallama da Malan Garbati. Bayan ya fito yayi saurin k'arasowa ganin zuri'ar sarkin fulani dan yasan akan maganar Mai Nasara ne.

Iso yayi masu har cikin gida,  tabarma ya shimfid'a masu a zaure. Bayan sun gama gaisawa sukayi masu bayani akan dalilin zuwan su. Malan Garbati yace Allah sarki,  ai jiya sunzo domin neman izini kuma na basu dama su nemi so a wajen Falmata,  bayan dana tambayeta tace ta amince.

Baffa Lamid'o yace wannan haka yake,  shiyasa muka zo domin manya su shigo ciki dan kusan da gaske akeyi,  sai dai muna da wata alfarma da muke buk'ata a wajen ku idan bazaku damu ba?  Malan Garbati yace to wace irin alfarma ce?  Baffa Lamid'o yace shi yaron da yake neman Falmata karatu yakeyi gaskiya.

Malan Garbati yace to yanzu mai kuke so?  Liman yace saura shekara d'aya su kammala karatun su,  shine muke son a saka rana bayan ya kammala sai ayi bikin.

Shiru Malan Garbati yayi,  can kuma yace to a gaskiya bani kad'ai nake da hakki akan Falmata ba,  idan ta nine babu matsala,  amma zanje nayi magana da mahaifiyata domin itace take da iko da Falmata.

Baffa Laimd'o yace wannan yana da kyau,  kaje ciki kuyi magana dan musan halin da ake ciki. Tashi Malan Garbati yayi ya koma ciki. A zabure Aljumma ta taso jin abinda Malan Garbati ya fad'a.

Duk'ar da kai Malan Garbati yayi yana fad'in hak'uri zakiyi Inna,  tunda dai Allah yasa ta samu mijin ina ganin lokacin auren ma kamar gobe ne. Aljumma tace anyi ba ayi ba dai,  taya yarinya zata samu miji kuma ace ta zauna tsawon shekara d'aya kafin tayi aure?  Malan Garbati yace Inna idan mukayi duba da dad'ewar da Falmata tayi babu ko saurayi,  ina ganin dan an jinkirta nan da shekara d'aya kamar gobe ne a wajen Allah.

Aljumma tace haka ne,  amma ina jinjina tsawon lokacin,  nida nakeso naga auren Falmata gashi yanzu an jashi da nisa,  bana so na mutu banga auren ta ba. Malan Garbati yace insha Allahu Inna zamuga aurenta,  ni na aminta da wannan yaro,  domin kowa yasan zuri'ar gidan Sarkin Fulani,  sannan wannan yaro kema sheda ce akanshi,  shine fa wanda ya tab'a ciyoma garin nan gasar Qur'ani da akayi ta k'asa baki d'aya,  kinga kuwa kowa zaiso ya had'a zuri'a dashi,  mugode Allah da yasa kaf garin nan baiga kowa ba sai Falmata,  ina tsoron kada mu hana auren nan kuma bamusan wanda Falmata zata aura ba.

Jinjina kai Aljumma tayi tace maganarka gaskiya ce Garbati,  tabbas nima nayi farin ciki alokacin da akace wannan yaro shine yake son Falmata,  domin na fiku sanin yanda ake fad'ar kyan halinsa. Bakomai kodan darajar Barkind'o da mahaifinsa marigayi Jibo bazan hana jininsu auren Falmata ba,  Allah ya nuna mana lokacin yasa muna raye.

Malan Garbati yace amin. Bari naje na fad'a masu yanda mukayi sai kawai a tsaida rana saboda a kareta daga sauran samarin da suke kawo mata hari. Aljumma tace to ka fad'ama Asabe?  Malan Garbati yace idan na dawo zan fad'a mata kinsan bata da matsala,  har su Kawu ma duk zanje nayi masu bayani. Aljumma tace toshikenan Allah yasa alkhairi.

Bayan yaje ya fad'a masu ta amince,  anan suka bada kud'in neman aure sukace za'a kawo kayan sa rana dan kowa ya sheda saboda kada wani ya shigar ma Mai Nasara gaba. Godiya sukayi mashi suka tafi.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now