Mai Nasara 115-120

978 59 1
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 115 ➡ 120


Tun bayan bikin su Barkind'o salon mulkin sarautar gidan ya canza,  domin Barkind'o duk abinda zaiyi to akan ilimi yake yinshi,  idan ta fannin boko ne bazaka k'ureshi ba,  idan akazo addini shima bazaka k'ureshi ba dan akan hadisi yayo degree d'inshi,  dan tun yana yaro yake da sha'awar yaga yasan hadisi,  hakan yasa Jibo ya shige masa gaba sai da ya sama masa university of Madina.

Duk wata seminer da za'ayi akan harkar addini to Barkind'o yana gaba,  shiyasa yake zuwa garuruwa yana bada lacca,  wannan abun yasa manyan mutane suka sanshi sosai,  gashi yana da kishin garin su,  duk wani abu na cigaba Barkind'o yana kok'ari yaga an kawoshi garin su.

Zuwa yanzu gidajen gonarshi sun hab'aka,  arzik'insa yayi yawa sosai,  domin har daga jihohi ana zuwa domin sayan madarar shanu,  k'wai da kaji. Sam bazaka had'a dukiyarshi data su Modibbo ba.

*** ****

Zaman matansu gwanin sha'awa,  sai dai anfi shiri tsakanin  Yabi da Zinatu,  Nanne sam bata son Yabi tafi shiri da Zinatu,  kuma ba komai bane yasa hakan sai haushin Barkind'o da sukeji musamman yayarta Khadee dan k'awar Karime ce,  duk da Karimen ta shiryu amma su suna jin haushin Barkind'o,  musamman da yanzu sunanshi ya d'aukaka ga arziki.

Sai dai sanin halin Modibbo yasa bata nuna jin haushin Yabi agabanshi,  asalima tafi yabonta idan yana wajen,  ko kuma idan zata bada wani abu akai mata bata badawa dole sai yana nan,  hakan da takeyi ba k'aramin dad'i Modibbo yakeji ba,  domin yana matuk'ar son Barkind'o ga kuma tausayinsa da yakeyi.

Duk abinda Nanne keyi Yabi tana sane da ita kawai ta kauda kai ne dan bata so ace ta fara fito da fitina,  haka kuma bata tab'a fad'ama Barkind'o ba,  acewarta idan tana tak'ama da duniyanci to ita ta fita.

Sanin halin yayar Nanne yasa Barkind'o yake yawan tambayar Yabi ko Nanne tana mata wani abu?  Yabi tace ba komai,  ai Nanne tana da kirki,  hakan yasa hankalin Barkind'o ya kwanta dan ya d'auki alk'awari bazai bari a cutar masa da mata ba kamar yanda akayi ma mahaifiyarsa dan kawai an aurota daga waje.

**** ***

A yanzu duk yaron daya taso cikin zuri'ar sarkin fulani dole asashi makarantar boko,  domin Barkind'o ya k'ara girman makarantar islamiyar da aka bud'e yanzu hada boko akeyi,  ana tashi kuma yara zasuyi sallah suci abinci a cigaba da islamiya,  shiyasa duk yaron da yazo da safe baya komawa gida sai k'arfe  shidda,  saboda kada yaran da suke cikin gidan surik'a guduwa kawai akaja katanga akasa gate.


Kuma kowane yaro ana kawo masa abinci,  babu abinda ba'asa na koyarwa ba,  sosai makarantar take da kyau,  hatta da computer an saka,  ga malamai isassu wad'an da suka san abinda sukeyi,  sannan gwamnati tana kawo coppers su koyar amakarantar dan sosai makarantar ta karb'u,  yara har daga kauyen kusa dasu suna zuwa.


Babu abinda ba'a koyawa,  hatta da fulatanci akwai malamin da yake koyawa,  shiyasa a k'aidar makarantar dole yaro yayi magana da turanci ko larabci. Barkind'o shine shugaban makarantar a fannin boko,  ta islamiya kuma Modibbo ne  shugaba Lamid'o mataimaki. Sosai suke girmama Barkind'o,  duk da arana d'aya aka haifi Barkind'o da Modibbo amma yana bashi girma,  shiyasa shima Barkind'o yake bashi girma.


Mai NasaraWhere stories live. Discover now