Mai Nasara 180-185

1K 68 7
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 180 ➡ 185

Suna zuwa Inna Wuro ta taso tana tambayarsu mai ya faru?  Baffa yace kije ki d'ora ruwan zafi zakiji komai. Sauko dasu Mai Nasara yayi ya shimfid'esu a saman tabarma. Wucewa band'aki yayi domin yayi alwalar magriba.

Zama Mairoji tayi akusa dasu tana hawaye. Inna Wuro tace ke Mairoji zaman me kike anan?  Zoki mik'o mani ruwa. Tashi Mairoji tayi jiki a sanyaye. Bayan sun d'ora ruwan suka wuce ciki domin suyi sallah.

*** ***

Zaune suke a cikin wani d'aki wanda yake daga gefe a cikin tsakar gidan wanda shirgi ne da aciki,  zuwan su Mai Nasara yasa Baffa ya gyarashi aka kwantar dasu saboda waje akwai sanyi gashi sun fito daga ruwa.

Duk'awa Baffa yayi yana jiyo bugun zuciyarsu,  da sauri ya d'ago tare da tab'a wuyansu,  kallonsu Mairoji yayi yana fad'in suna da rai,  sai dai da alama sun bugu kuma ga ruwan da suka sha.

Saurin tashi yayi ya nufi d'akinshi,  bai jima ba sai gashi da wata jakar fata,  ruwan da Inna Wuro ta d'ora yasa ta kawo mashi,  nan yace su fita saboda zai canza masu kaya. Cikin kayanshi ya d'auko masu kala biyu,  haka ya canza masu kaya sannan ya fara duba jikinsu.

Mai Nasara ya samu karaya a k'afa,  inda Majidad'i ya karye a hannu,  sai kuma gaba d'ayansu sunji ciwo akawunan su,  sai kuma sauran k'urjewa a jiki.

Tsumma ya fara tsomawa a cikin ruwan zafin yana gasa masu jiki,  sai da ya gama sannan ya matso da jakarshi,  kasancewar yana d'ori yasa yake da kayan yin d'ori,  haka ya zauna gaba d'ayansu ya d'ora su.

Bayan ya gama ya shafe masu wajen da magani sannan ya jera kara yasa kyalle ya d'aure. Duk abinda yakeyi har ya gama basu sani ba,  saboda har yanzu basu farfad'o ba.

Bayan ya gama yace Inna Wuro ta kawo masu wuta asa a d'akin saboda yayi d'umi,  gaba d'ayansu ya rufesu da zani,  hatta da ciwukansu duk ya shafa masu magani,  idan ka gansu sai ka d'auka baccin lafiya sukeyi.

Kayanshi ya d'auko ya jawo masu k'ofar suka nufi d'akinsu. Zama sukayi Inna Wuro tana fad'in Baffan Mairoji ina kam lafiya lau?  Baffa yace to nayi masu abinda ya dace,  gaba d'ayansu suna da rai,  amma suna cikin wani hali,  addu'a zamuyi masu Allah ya tashe su ta hakan ne zamu san yanda akayi suka samu kansu a wannan halin.

Inna Wuro tace hai,  mutane babu tsoran Allah,  kai da ganin wannan ta'asar kasan wasu ne sukayi masu haka. Baffa yace tabbas wannan al'amarin wasu ne suka aikata masu,  kuma da niyar kashe su akayi koma menene,  Allah dai ne ya tsare su shiyasa ya jefosu wajen mu.

Inna Wuro tace ai dama ana yawan samun gawar mutane a cikin ruwan nan,  saboda kowa yasan idan ya wurgo mutum cikin ruwa dole ruwa zai korashi zuwa wani wajen,  kaga 'yan uwanshi baza su tab'a ganinshi ba.

Baffa yace tunda Allah yasa muka tsince su to zamu taimaka masu iyakar yin mu,  idan kuma mukaga abun yafi k'arfin mu tofa dole mushiga cikin gari mu sanar da mai gari.

Inna Wuro tace Baffan Mairoji nikam ina jin tsoro kada muje mu fad'a a gari kuma ya kasance wad'an da sukayi masu abun acan suke,  kaga idan suka samu labarin basu mutu ba zasu iya binsu. Baffa yace to Allah yasa su tashi hakan ne zaisa mu zauna dasu ba tare da kowa yaji ba.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now