Mai Nasara 135-140

1.2K 61 1
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 135 ➡ 140

Koda Hajjo ta dawo daga aiken ta k'ofar gidan su Maina ta biyo ko Allah zai sa ta ganshi. Aikuwa tana shawo kwana ta ganshi zaune saman farar kujera yana latsa waya. Murmushi ta saki tayi tsaye ta hard'e hannuwa tana kallonshi.

Haka kawai yaji kamar ana kallonshi,  d'ago kai yayi karaf suka had'a ido da Hajjo,  a zabure ya mik'e dan ya d'auka gizo take masa. Ganin taki koda motsi ne ba shiri ya shige gida cike da tsoro. Ajiyar zuciya ta saki ta nufi gida cike da farin ciki.

Da Baffajo Maina ya had'u,  Baffajo yana ganinsa yace Maina lafiyar ka kuwa?  Shagwab'e fuska Maina yayi yana fad'in ni kam makaranta zan koma Baffajo. Matsowa yayi yana fad'in kai da kace sati hud'u zakayi ko sati d'aya bakayi ba zaka ce zaka koma?  Maina yace Allah Baffajo d'azu na had'u da wata aljana.

Dariya Baffajo yayi yace wace irin aljana kuma?  Nan Maina ya fad'a masa abinda ya had'ashi da Hajjo. Sosai Baffajo yake dariya, Maina yace haba ya jna fad'a maka magana kana mani dariya?  Baffajo yace ai dole nayi dariya,  kai idan aljana ce taya zata tsaya fad'a maka sunan ta?  Kawai dai kila na kusa samun surika.


Maina yace Allah ya kyauta,  nifa har yanzu banga macen data burgeni ba,  nafison na auri yarinyar da naji zuciyata ta kamu da matsanancin sonta,  nasan zan samu duk abinda nake so. Baffajo yace babbar magana,  to Allah ya had'aka da macen da zaka so sosai. Maina yace amin Baffajo,  karik'a taya ni addu'a.

**** ****

Tun daga ranar Hajjo ta kasa sukuni,  kullum soyayyar Maina yawa take k'arawa a zuciyar ta,  kuma kullum sai ta je k'ofar gidansu dan kawai ta ganshi amma abun mamaki tun had'uwar farko bata sake ganinsa ba.

Yau dai ta shiga damuwa,  zuwa tayi wajen Kaka tace wai Kaka bazaki aike ni wajen Inna Dije na gaishe maki ita ba?  Murmushi Kaka tayi tace ke dai kice kina son kije kiga Maina kawai,  idan na aike ki wajen Dije ai bata sanki ba.

Turo baki Dije tayi tace to dan Allah kitashi muje kuyi zumunci kinga kin jima baki motsa k'afarki ba. Kaka tace ni k'afata lafiyarta k'alau,  ai kullum ina motsata a cikin gida.

Hajjo tace dan Allah fa nace Kaka,  kinga idan mukaje da ke zatafi saurin ganeni kinga daga ranar sai na rik'a zuwa mata fira. Girgiza kai Kaka tayi cike da tausayin jikarta tace shikenan tashi muje. Tsalle Hajjo tayi tana fad'in nagode Kaka.

Kaka tace Oh!  ni Tabawa,  wai yanzu zamani yazo kunya tayi k'aranci a wajen fulani?  Kai wannan zamani ba muji dad'in shi ba,  da muna zaune hankali kwance wannan mai jan kunnan ( Bature)  ya kawo mana ilimin waye wa,  haka kawai ya b'ata mana yara,  dan duk a makaranta suke koyo wannan rashin kunyar. Hajjo tace Kaka ga mayafinki tashi mu tafi. Tashi tayi tana sababi suka fita tare da kulle gidan.

**** ****

Sosai Inna Dije taji dad'in ganin Kaka,  dan k'awarta ce tun ta yarinta. Inna Dije tace Tabawa munyi wuyar had'uwa. Kaka tace wallahi kuwa,  k'afa ce take hanani fita,  dama kuma ke baki da son fita. Inna Dije tace wallahi abubuwan ne.

Kallon Hajjo tayi tace Tabawa ina kika samu 'yan mata kuma haka?  Kaka tace jika tace Hajjo wadda marigayi 'Da na Alami ya mutu ya bari,  kinsa da acan wajen dangin mahaifiyar ta take a Mayo Belwa,  to da mahaifiyarta ta rasu shine fa naga tana cikin takura,  kinsan yanzu duniya ta lalace,  komai na ganin ido akeyi,  mahaifiyarta tana rasuwa danginta suka fara canza mata.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now