Mai Nasara 5-10

1.7K 109 2
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 5 ➡ 10

Suna cikin gudu Majidad'i yayi tun-tub'e da wani dutse nan ya zube kasa Mairoji tayi gefe guda shi kuma ya faad'a cikin wani rami kanshi ya doki wani abu,  k'ara ya saki saboda zafin da yaji ya ratsa shi. A gigice Mai Nasara ya juyo jin ihun Majidad'i.

Gashi baya ganin koda gabansa ne bare yaga inda suke,  wasu hawayen tausayin kansu ne suka zubo mashi,  gashi yana tsoron yayi magana mutanan su jisu.

Komawa yayi da baya ya fara kiran sunan Majidad'i a hankali,  jin shiru bai amsa ba hankalinsa ya k'ara tashi,  zubewa yayi a wajen ya saki wani irin kuka. Majidad'i kuwa yana can ya sume.

Kuka sosai Mai Nasara yakeyi,  saurin tashi yayi ya fara lalube,  jikinsa gaba d'aya kyarma yakeyi,  ya dad'e yana dubasu can yaji yayi tun-tunb'e da wani abu,  saurin duk'awa yayi yana shafa wajen.

Alamun mutun yaji haka yasa da sauri ya duk'a tare da kamo abinda yaji,  yana shafawa ya gane Mairoji ce,  saurin d'aukarta yayi yaja ta gefe guda suka zube kasa ya rungumeta yana wani irin kuka.

Dan Allah Mairoji kada ki mutu,  mun rasa su Baffa ki daure ki rayu domin na rik'a ganin fuskar mutanan da suka taimaki rayuwar mu. Jijjigata ya cigaba dayi yana kuka.

Jin jikinta babu riga dan daga ita sai 'yar shimin data kwanta da ita sai kuma zanin da yake ajikinta kanta ko d'an kwali babu gashi wajen da suke akwai sanyi. Saurin ajeta yayi ya cire rigarsa ya zura mata da yake doguwa ce.

Zanin jikinta ya yaga ya maida sauran ya d'aura mata sai ya d'auki guntun da ya yaga ya d'aura mata akanta. Jawota yayi ya k'ara rungumeta yana fad'in babu inda zamuje,  ko da zasu zo su kama mu bazan tafi na bar Majidad'i ba.

Zamu zauna anan har gari ya waye sannan na dubashi,  koda gawarsa ce insha Allahu sai na kaita gida. Bawan Allah saboda ni rayuwarsa tashiga had'ari,  gashi yanzu yana neman rasa ransa.

Mai yasa?  WAYE NE (littafi na mai zuwa maku nan gaba insha Allah, ).  Mai nayi maku kuka aikata mani haka?  Waye yayi mani haka?  Ashe dama ina da makiyi ban sani ba?  Yaushe na samu makiyi ban sani ba? Nasan babu wanda na  zalinta da za'ayi mani irin haka?  "Falmata" wayyo Allah.

Ko wane hali kike ayanzu?  Ko tana tare da aure na?  Runtse ido yayi hawaye suna zubo masa suna sauka a fuskar Mairoji wadda farkawarta kenan taji yana wannan sambatun.

Runtse ido tayi wani irin bakin ciki ya ziyarci zuciyarta,  duk da ta kasa gane a inda take amma tabbas muryar Mai Nasara takeji akusa da ita,  ko dai mafarkin data sabayi ne?  K'ara runtse ido tayi jin kanta yana wani irin sarawa.

Jin an k'ara matse ta ne yasa tayi saurin bud'e ido,  tabbas ba mafarki takeyi ba,  to mai ya kawo Mai Nasara d'akin ta?  Ko dai shima yana sonta kamar yanda take sonshi?  Amma mai yasa zaizo d'akinta bayan yasan su Baffa zasu iya ganin sa?  Gashi yazo ya rungumeta kuma yana ambaton sunan Matarsa.

To kodai makuwa yayi yazo d'akin ta ya d'auka matarsa ce?  K'ara runtse ido tayi a hankali wasu siraran hawaye suka zubo mata na bakin ciki. Gashi tana dakon soyayyar sa amma shi yana tunanin wata. Allah kasa idan ya koma ya iske an raba auren har ta sake aure,  nasan zai dawo domin ya aure ni.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now