Mai Nasara 75-80

898 51 0
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 75  ➡ 80

Kasa kwanciya Jumare tayi,  Hassanu yana mata sallama tabi bayansa zuwa gidan Kawu dan bata jin zata iya bari har zuwa gobe sannan ta fad'a ma Gwoggo ba.

A zaune ta iske su tare da Kawu,  bayan sun gama gaisawa Kawu yace Jumare lafiya kuwa na ganki da wannan daren?  Murmushi Jumare tayi tace nazo wajen Gwoggo ne. Kallonta Kawu yayi yana fad'in Allah yasa ba wani abun kikazo dashi ba dan na fara tsorata da ke.

Jumare tace Kawu bakomai kawai nazo wajenta ne. Gwoggo tace to sirri zamuyi da d'iyata ko dole sai kaji?  Kawu yace to masu d'iya ayi sirri lafiya,  amma dai kubi ahankali kada allura ta tono galma.

Dariya suka sa suka shige d'aki. Cike da mamaki Gwoggo tace wai da gaske kike ko kuma wasa kike yi?  Jumare tace wallahi Gwoggo ciki na gani ajikin Jamee,  kuma ba k'arami bane babba ne kilama atare da Karime zata haihu.

Ajiyar zuciya Gwoggo ta saki tana fad'in jar uban can,  aiko abinda bazai yuwu bane,  taya zamu zauna shekara da shekaru agidan nan mu da mazajen mu ace lokaci guda sarautar gidan ta tafi wani waje.

Wallahi kinji na rantse maki matuk'ar ina numfashi bazan bari Jibo ya haihu da Jamee ba,  tabbas zamu lalata cikin jikinta,  kuma zamu hana ta d'aukar wani cikin,  kinga idan aka ga ta kasa haihuwa dole za'ace ya k'ara aure amatsayinsa na shugaba.

Murmushi Jumare tayi tana fad'in  ai nasan idan ina tare dake bazanyi kuka ba,  wallahi da ace ba gobe zamuyi tafiya ba da agoben cikin zai zube. Gwoggo tace ai akoda yaushe muna tare da ke.

Muryar Kawu sukaji yana fad'in wani lokacin tunanin ku gajere ne, saurin kallonsa sukayi. Shigowa yayi yana murmushi. Gwoggo tace gani tayi maganar ta mata ce shiyasa.

Zama yayi yana fad'in garin wannan k'aramin tunanin nata ne ai ta kusa jama kanta ita da Hassanu. Jumare tace Kawu kayi hak'uri bazan k'ara ba. Jinjina kai yayi yana fad'in ashe Jamee ciki gareta?  Gwoggo tace wallahi yanzu Jumare take fad'a mani.

Kawu yace aiko ba a gidan nan zata haihu ba,  ai dama tun farko da naji ance wai d'iyar Malan Habu zai aura nasan cewar shirin Malan Habu ne, ai dama badan Allah yake zaune da Sarki ba,  ina shi ina abota da Sarki,  tun farko ya gama shirinsa shiyasa ya had'a auren Jibo da Jamee.

Ko aikin da yakema Jibo na gidan gona da gonakinsa badan Allah yakeyi ba,  saboda yasan zai samu jika dashi shiyasa ya tsaya kai da fata sai da ya gina dukiyar Jibo ta yanda jikokinsa bazasuyi talauci ba.


Yanzu idan Jamee ta haifi namiji kunga shikenan nan gaba sai sarautar sarkin fulani ta koma a zuri'ar Malan Habu. Gwoggo tace aiko abinda bazasu samu ba kenan.

Kawu yace kubar mani komai a hannuna,  matuk'ar ina raye Jibo bazai haihu da jinin Malan Habu ba,  dole ko yana so ko baya so yazo cikin zuri'ar gidan nan ya k'ara aure,  to daga nan idan ta haihu bana bakin ciki dan an bama d'anta sarauta domin d'an dangi ne.

Idan muka dawo daga wannan tafiya akwai Jauro maharbi wanda nake karb'ar maganin tsari awajensa,  Jauro yasan duk wasu kalar magani na mugunta,  ina mai tabbatar maku daya bamu magani sau d'aya zata sha shikenan abinda yake cikinta zai fito kuma bazai zo da rai ba.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now