Mai Nasara 185-190

1K 60 4
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 185 ➡ 190

Sosai Maina ya tashi hankalinsa,  rik'eshi likita yayi yana fad'in haba Maina ka nutsu mana,  kada fa garin kishi ka tona kan ka,  arayuwa komai a hankali ake binshi,  hanzari ba naka bane,  ni dama tunda kace mani wai sai ya kwana ad'akinta sannan zasu aikata masa nasan kayi kuskure,  kasan kowace mace da irin yanayinta,  kaga daga yi so d'aya gashi har ciki ya shiga.

A fitar dashi likita!  Da sauri likitan ya kalli Maina jin abinda yace. Jinjina kai Maina yayi yana fad'in bazan iya zaman jiran sai nan da fin shekara kafin na mallaki Falmata ba,  kasan yanda nakeji a zuciya ta?  Rabon dana samu baccin kirki tun ranar dana d'ora idanuwana akan fuskarta.

Likita yace kayi hak'uri Maina,  taya kake tunanin zan iya zubar da jinin zuri'ar ku?  Marigayi sarki Jibo shine silar tafiyata karatu,  ta silar shi ne na samu aiki,  Baffa Barkind'o ya tsaya mani,  saboda shi na samu k'arain matsayi cikin lokaci kad'an,  idan har nasa hannuna cikin lalata abinda zai faranta zuk'atan zuri'ar ku hakika Allah bazai barni ba.

Maina yace kana goya mani baya akan komai,  mai yasa a wannan karon bazaka taimakeni ba?  Likita yace ada can ma ban tab'a taimakonka saboda ka aikata b'arna ba,  abu d'aya kanemi ni da nayi maka kuma nayi maka shi,  dan haka ina mai baka shawara da kayi hak'uri,  tunda har ka samu nasarar kawar da Mai Nasara auren Falmata bazai maka wahala ba,  shekara d'aya kamar kwana ce,  yanzu idan aka zubar da cikin dole za'a zargeni.

Shiru Maina yayi yana hawaye. Likita yace kayi hak'uri dan Allah Maina,  ina mai tabbatar maka itama Falmata zuwa yanzu tana jin tausayinka yanda taga ka damu da mijinta,  kaga bazaka sha wahalar shawo kanta ba.

Murmushi Maina yayi yace kana ganin zata amince da aure na cikin sauki?  Likita yace sosai ma,  kaga yanzu zaka samu  kusanci da ita saboda wannan cikin,  idan kuma ta haihu sai ka nuna matsananci so ga abinda ta haifa,  ina mai tabbatar maka lokaci guda zaka saye zuciyarta,  kana fitowa da zumar aurenta zata amince.

Hannu Maina yasa ya goge fuskarshi yace nagode abokina,  naji dad'in shawarar ka,  kuma yanzu ne zanyi kok'arin nuna mata kulawa sosai. Likita yace babu damuwa muje na baku sallama dan ta farfad'o,  dama jiri ne ya d'ebeta,  sai an rik'a kula da yanayin cin abincin ta. Maina yace insha Allah.


Fitowa sukayi murmushi d'auke a fuskar Maina,  yana shiga d'akin Inna Dije tace Maina kaji abun farin ciki ko?  Murmushi yayi yace har na rasa inda zansa raina,  Allah shine abun godiya,  ina ma ace Yazeed yana nan yaji wannan labarin mai dad'i.

Duk'ar da kai Falmata tayi tana jin dad'i a cikin ranta,  ganin yanda Maina yake farin ciki sai ta k'ara ganin girmanshi. Nan Maina yace Inna zamu iya tafiya. Wayarshi ce tayi k'ara,  yana dubawa yaga Baffa Barkind'o ne,  yana d'auka ya fad'a mashi gasu nan dawowa ta samu lafiya. Haka suka nufi mota sukayi gida cike da farin ciki.

Suna zuwa Maina ya fita ya nufi b'angaren Baffa Barkind'o,  yana zuwa ya rungume Baffa Barkind'o yana dariya. Da kallo suka bishi ganin yana dariya wadda rabon da yayita tun b'atan su Mai Nasara.

Baffajo yace kai kada ka karya manashi. Sakin Baffa yayi yana fad'in dole nayi farin ciki,  domin mun kusa samun jinin Yazeed a gidan nan. Dammm...  Gaban Baffajo ya faad'i jin abinda Maina ya fad'a,  shikenan duk auren da yayi mashi da wuri dan yariga haihuwa ashe Mai Nasara ne zai rigashi?  Kai amma wannan abu da ban haushi yake.🤔

Mai NasaraWhere stories live. Discover now