Mai Nasara 95-100

1.1K 59 2
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 95  ➡ 100

Shiru Malan Habu yayi lokacin daya gama sauraron bayanin Hassanu,  babu abinda kakeji a d'akin sai kukan Hassanu. Malan sosai yayi mamakin irin abubuwan dasu Kawu,  Jumare,  Baffajo da Hassanu suke kulla ma Jibo da matarshi. Lallai Allah abun godiya ne,  kuma duk zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shaho sai yayi.

Sun so su hana Jamee d'aukar ciki Allah bai nufa ba,  da suka gano tana da ciki kuma suka d'auki niyar lalatashi da sun dawo sai Allah yayi hukuncin sa akan su. Wato tun suna kok'arin hana Jibo sarauta har abun yazo kan matarshi.

Lallai wannan abun ya isa mutum yayi hankali,  kuma Allah kad'ai yasan abinda yake cikin Jamee da har yake kareta daga sharrinsu. Ajiyar zuciya Malan yayi yace ya isa haka Hassanu.

Ka godema Allah da yasa ka gane gaskiya har kake neman yafiyar wad'an da ka cuta,  su sauran da yake basu da rabo kaga sun mutu tare da mugun nufi a zuciyar su,  ka d'auka Allah ya k'ara ara maka rana ne dan yaga alamun tuba atare da kai.

Dan haka idan har zaka bi shawarata ka jefar da makaman yakin ka,  gaba d'aya duniyar nan ba matabbata bace, mutuwar su Sarki ta isheka ishara,  sunyi tafiya cike da burin dawowa amma sai Allah ya amshi ransu ba tare da sun shirya ba.

Hassanu ya kamata ka koma ka k'aro ilimin addini,  Jibo yayi maku wayau, bayan ilimin addini da yake dashi gashi yanzu ya samu ilimin zamani, duk da Kawu ne da Mahaifiyar ku suka hana ku ilimin zamani,  gashi yanzu ya shafi har 'Ya'Yan ku,  amma ina ganin da kabi ta d'an uwanka Jafaru da yanzu kaima kana da ilimin addini.

Hassanu yace wallahi Malan yanzu a shirye nake dana koyi ilimin addini,  tabbas nasan k'arancin ilimin addini shine yake sa yawancin mutane aikata abubuwa marasa kyau,  wasu kuma kawai son zuciyarsu ne.

Kamar Baffajo da Kawu na tabbata ba rashin ilimi bane yasa suke aikata abinda suka ga dama,  kawai son zuciya ne yasa suke aikata wannan abun. Amma nayi maka alk'awari daga yau bazan sake mai-maita abinda nayi abaya ba,  kuma Hamma Jibo yana dawowa zan nemi yafiyarsa.

Amma dan Allah Malan ka fassara mani mafarkin dana fad'a maka. Murmushi Malan yayi yace Hassanu kada ka damu,  babu wata fassara da mafarkin ka yake buk'ata,  domin ayanzu duk wanda yace maka zai fassara maka mafarki to yaso kanshi,  sai dai kawai zan iya baka k'arin haske agame da mafarkin da kayi.

Idan kayi duba da yanda kake mafarkin,  suna cewa kada kazo wajen su,  anan zan iya cewa kafin su rabu da kai kun shirya aikata wani abu,  idan har ka fasa aikata wannan abun da kukayi niya shikenan ka sila,  kuma idan ka koma ga Allah zai rabaka da wannan mafarki,  kuma karik'a addu'ar kwanciya bacci  insha Allahu bazaka sake wani mugun mafarki ba.

Jinjina kai Hassanu yayi yace nagode Malan,  kuma insha Allahu zanyi yadda kace,  ina neman alfarmar na kasance d'aya daga cikin d'aliban ka. Malan yace babu komai Hassanu,  kaima 'Dana ne,  dan haka kazo zan rik'a koya maka. Sosai Hassanu yaji dad'in abinda Malan yace,  anan yayi masa godiya ya tafi.


**** ****

Tun daga lokacin Hassanu ya canza,  kullum yana tare da Malan,  hatta da gidan gonar Jibo tare suke zuwa yana tayashi aiki,  idan suka dawo kuma suyi karatu sannan ya wuce gida. Sosai Karime tashiga damuwa ganin Hassanu ya canza hali.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now