Mai Nasara 190-195

998 64 3
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 190 ➡ 195

Dariya Maina yasa shida abokinsa lokacin da suka gama had'a maganar Maina data Falmata a cikin computer. Maina yace gaskiya nagode abokina,  dole zan maka kyauta mai tsoka,  gaskiya ka k'ware wajen iya had'a abu,  sai kace alokaci guda akayi maganar,  gaskiya na jinjina maka Naseer.

Wanda aka kira da Naseer yace ai wannan ba wani abu bane,  kai duk yanda kake tunanin aikin computer wallahi ta wuce nan,  idan so kake a had'a hotonku kai da Falmata kuna kwance duk zan iya. Dariya Maina yayi yace a'a iskancina bai kai nan ba,  nida nake so kowa ya gane banida laifi itace mai laifin ai bazan so ayi haka ba,  kai dai wannan ma da kayi ya isa,  kuma duk wanda yaji wannan maganar dole ya yarda da ita,  domin ga muryarta nan ta fito sosai,  yanzu dai kunna mani naji yanda zaiyi a cikin wayata.

(DAN ALLAH HAMMA  KA RUFA MANI ASIRI, DAN ALLAH KADA KA FA'DAMA KOWA WANNAN MAGANAR,  NA ROK'EKA DA ALLAH KA RUFA MANI ASIRI. WALLAHI HAMMA NA YARDA NA HAK'URA DA ABINDA KAYI MANI,  DA DAI ACE MUTUNCINA YA ZUBE A GIDAN NAN GARA NA HAK'URA DA DUK WATA DAMUWATA, MAHAIFIN ABINDA YAKE CIKINA MA YA TAFI,  WALLAHI NA HAK'URA KA RUFA MANI ASIRI.

WALLAHI KIN BANI KUNYA FALMATA, NA 'DAUKA ABINDA KIKAYI TUN KINA BUDURWA YARINTA CE,  ASHE HAR YANZU WANNAN K'UDIRIN YANA RANKI, YANZU KE KO KUNYA BAKIJI BA WATA UKKU DA 'BACEWAR MIJINKI KIZO MANI DA WANNAN MAGANAR,  WAI IDAN BA' A GANSHI BA A RABA AUREN NA AURE KI.

TO KISANI IDAN HAR KIKA CIGABA DA TAKURA MANI AKAN WANNAN MAGANAR TABBAS ZAN FA SA WANAN MAGANAR KOWA YAJI, KINSAN DAI KUMA DOLE KIBAR GIDAN NAN, KUMA KI AJE MANA ABINDA ZAKI HAIFA.

WALLAHI NA YARDA BAZAN FA'DAMA KOWA BA DAN ALLAH KA RUFA MANI ASIRI.

SHIKENAN TASHI KIJE BAZAN FA'DAMA KOWA BA, AMMA DUK RANAR DA KIKA SAKE TADO DA WANNAN MAGANAR INA MAI TABBATAR MAKI SAINA FA'DA,  KO BAN FA'DAMA KOWA BA ZAN FA'DAMA HAJJO,  TASHI KIJE.)

Dariya suka kwashe da ita,  Maina yace shege Naseer,  lallai wannan abu ya hau,  maganar tayi dai-dai kamar alokaci d'aya akayi ta,  kaga an cire waccan tawa da nayi kuma ka d'ora wannan,  bani account number d'inka gara tun yanzu kaji dumus. Murmushi Naseer yayi yace to nagode,  kuma ina buk'atar zabbi da d'an kaji,  sai kuma wani gyara,  naji kace wata ukku,  bayan kuma anyi wata bakwai da b'acewar mijinta. Maina yace kada ka damu,  gara abarshi haka kowa zaiyi tunanin dama can tana sona ai. Naseer yace haka ne,  yanzu ya maganar zabbin,   Allah yasa akwai. 

Maina yace baka da matsala,  anjima zan bada akai maka gida hada k'wai ma duk zan aiko maka. Naseer yace to nagode. Maina yace amma ka goge wannan na cikin computer d'in yanzu,  kuma bana son naji wannan maganar a wajen wani,  na yarda da kai shiyasa na kawo maka wannan aikin,  badan haka ba wallahi da ba'a nan garin za'ayi mani aikin ba. Naseer yace baka da matsala,  haba Maina,  idan ban taimakeka ba wazan taimaka,  wallahi babu wanda zaiji wannan maganar, bari ma ka gani yanzu na goge.

Godiya Maina yayi mashi ya tashi ya tafi gida yana mai cike da farin ciki,  a yanzu kam yasan Falmata da taji wannan abun to bata da wani zab'i daya wuce ta amince masa. Dariya yayi ya nufi gida.

**** ****

Yawuro da take zaune taga shigowar Falmata,  sai dai bata shigo wajenta ba ta nufi d'akinta,  da sauri ta tashi tabi bayanta. Falmata tana zuwa ta faad'a saman gado tana wani irin kuka,  wace irin k'addara ce wannan kuma?  Mai yasa Hamma Maina zai b'ullo mata da wannan abun?  Sallamar Yawuro taji hakan yasa da sauri da fara goge idonta.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now