Mai Nasara 155-160

892 58 2
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 155  ➡ 160

K'arar wayarshi ce ta maidoshi daga tunanin daya tafi na Falmata,  koda ba'a fad'a mashi ba ya gane itace saboda wayar da yaji tanayi. Ajiyar zuciya ya saki ya d'auki wayar.

Muryar Hajjo yaji tana fad'in Maina na kazo ga amaryar Mai Nasara tazo maka sannu da zuwa. "To" kawai yace mata ya kashe wayar. Runtse ido yayi yana jin wani irin yanayi yana ratsashi,  sosai zuciyarshi take bugawa,  ya dad'e a haka kafin ya tashi kamar mai jin bacci ya tafi.

Zaune suke suna ta fira,  Falmata sai tsokanar Hajjo take tana fad'in wallahi Diddi acikin sati d'aya har kin canza,  lallai Hamma yana ji dake. Hajjo tace sosai ma,  shiyasa a kullum nake k'ara son shi,  bani da wani haske da yake haske mani zuciyata kamarshi,  ina matuk'ar son Maina.

Motsin da sukaji ne yasa sukayi shiru,  Maina ne ya shigo idonshi akan Falmata,  tasowa Hajjo tayi tana fad'in Maina sannu da zuwa. Kai kawai ya d'aga ya wuce saman kujera ya zauna.

Duk'ar da kai Falmata tayi tana gaishe shi. Murmushi yayi yana k'are mata kallo yace kina lafiya Falmata?  Tace lafiya lau ya hanya?  Maina yace lafiya lau. Khalcume tace Hamma ina wuni?  Murmushi yayi yace lafiya lau k'anwata.

Tashi Falmata tayi tana fad'in Khalcume muje ko?  Da sauri Maina ya d'ago kai yana fad'in ai baki isa ba,  tunda kika zo dole kiyi mana wuni. Murmushi Hajjo tayi tace fad'a mata dai Maina,  sai wani jin kunya takeyi,  kema nan da lokaci kad'an zaki shigo gidan nan.

Rai ab'ace Maina yace babu wani lokaci kawai ta zauna anan. Saurin kallonshi sukayi jin abinda yace. Cikin tsarguwa yace emana,  tun daga yanzu ta zama 'yar gida. Dariya Hajjo tayi tace sosai ma.

Haka Falmata ta koma ta zauna,  anan suka cigaba da fira,  sai dai duk a takure take,  saboda data d'ago kai sai sun had'a ido da Maina,  shi kuwa yana ta latsa waya kuma ya kasa tashi daga wajen,  kallonta yake sosai kuma babu wanda yasan ita yake kallo,  sai itace jikinta yake bata.

Ganin kallon ya wuce na hankali kawai sai taji ranta ya fara b'aci,  da sauri ta mik'e tana fad'in gaskiya tafiya zanyi Inna Aljumma tana jirana. Hajjo tace kai Falmata,  sai kace ana korarki?  Falmata tace nidai tafiya zanyi. Bata jira abinda zasuce ba kawai tayi waje.

Da sauri Khalcume ta mik'e tana fad'in bari naje na rakata. Tashi Maina yayi yana fad'in bara naje inaso nada Baffajo. Hajjo tace to sai ka dawo.

Yana fita ya hangeta ta kusa gate,  da sauri Khalcume ta k'arasa wajenta tana fad'in haba Addah ko dai anyi maki wani abu ne?  Falmata tace bakomai kawai gida nake son zuwa.

Har wajen gate Khalcume ta rakata sukayi sallama akan sai gobe idan tazo islamiya. Da sauri Falmata ta bar wajen jikinta yana rawa,  tafiya taje tana tunanin irin kallon da taga Maina yana mata,  a zuciyarta tace to wannan ko dai haka halinsa yake?  Dama fa ance masu zuwa k'asar waje basu da kunya,  nikam bazan k'ara zuwa gidan Diddi ba,  Allah ma yasa bata kamashi ba. Haka Falmata tayi ta surutu har ta isa gida.

Maina kuwa a hankali yake binta sai murmushi yakeyi yana k'arema tafiyarta kallo da yanda jikinta yake motsawa duk da acikin hijab ne. Har sai da tashige gida sannan ya juya yana fad'in Yazeed mai yasa a komai sai naka yafi nawa?  Tunda muka taso kake fina da abubuwa.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now