Mai Nasara 120-125

1K 67 2
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey

Page 120  ➡ 125

Barkind'o yana isowa wajen shima ya zube dan yana zuwa idanuwanshi suka sauka akan fuskar Yabi wadda jini duk ya b'ata ta. Nan fa hankulan mutane ya k'ara tashi,  anan aka fara kok'arin d'aukar gawar mutanan akasa a mota. Wani ne yace ma sauran abokan ango suyi gaba da sauran mutanan zuwa can gidan su Barkind'o,  Lamid'o da wani suka d'auki su Modibbo domin su kaisu asibiti,  motar data d'auki gawarwakin tabi bayansu domin aje a tabbatar ko sun mutu.


Suna zuwa asibiti nan aka nufi wani d'aki dasu Barkind'o,  inda wani likita ya nufi wajen gawar su Yabi,  yana zuwa ya duba babu wanda yake da rai,  haka suka d'auke su aka nufi gida da su,  kafin su k'arasa tuni labari yaje gidan suna tsaye ana jiran suzo aji ko sun mutu.

Babu b'ata lokaci akayi waya zuwa Yola aka sanar dasu halin da ake ciki,  sosai hankalin mutane y tashi,  nan fa taro ya koma na bakin ciki,  anan Malan Sayyadi yakira Hassanu yace kawai suyi masu sutura a binne su tunda dare beyi ba kada ace za'a jirasu ko sunzo babu abinda zasuyi mutuwace aa riga anyita kawai zasuyi zaman makokinsu acan Allah yajikansu ya basu hak'urin rashi.

Sosai mutuwar su Yabi ta tab'a zukatan mutanan gidan,  Shabbak yasha kuka dan itace autarshi,  Dije da Zinatu kamar zasuyi hauka,  shikenan sun rasa Gwoggo Fatu da Yabi,  haka Dije ta rungume 'yan biyu tana kuka,  duk da basu san abinda yake faruwa ba suma kukan suka sa.

**** ****

Haka aka shirya gawar mutane biyar,  mata hud'u namiji d'aya aka yimasu sallah aka nufi makwancin su dasu,  Hassanu sosai yake tausayin Barkind'o,  bai san yanda zaiji ba idan ya farfad'o ya iske an rufe Yabi ba tare daya ganta ba,  hankalinshi biyu ya kasu,  yana tunanin halin dasu Modibbo suke ciki sannan kuma ga tausayin Barkind'o.

Bayan an gama rufesu Hassanu da Lamid'o tare da Shabbak suka nufi asibiti domin suga halin da suke ciki,  suna zuwa Barkind'o ya farfad'o,  nan ya farka da wani irin kuka mai ban tausayi.

Da sauri Hassanu yaje ya rungumeshi yana lallashin sa,  Lamid'o kuwa gefe guda ya samu yana kuka. Modibbo kuwa yana can ana ta fama da numfashin sa dan har yanzu yaki dawowa,  gaba d'aya likitoci suna kanshi.


Barkind'o cikin kuka yace Baffa shikenan na k'ara rasa Yabi?  Dan Allah kace mun bata mutu ba,  idan kuma ta mutu ka kaini naga fuskarta kafin a rufeta,  dan Allah kada ku rufeta ban ganta ba kamar yanda banga su Abbu ba.

Sosai Hassanu ya rik'eshi hawaye kawai suke zuba daga idonshi,  ya rasa bakin da zaiyi masa magana,  sun dad'e ahaka kafin yace Barkind'o kayi hak'uri,  haka Allah ya tsaro maka rayuwar ka,  Allah kad'ai yasan nufinshi akanka,  dan haka ka d'auki duk wata k'addara da Allah ya d'ora maka,   kai da Modibbo Allah yana jarabtar ku,  ka rasa iyayen ka,  yanzu kuma ka rasa matar ka,  shima ya rasa matarshi da d'iyarshi,  yanzu kuma ya rasa matar da ko tarewa batayi ba,  dan haka kuyi hak'uri insha Allahu alkhairi ne zai biyoku abaya.

Babu yanda zamu aje gawa har ku farfad'o,  hakan yasa kawai muka sallace su yanzu muka dawo daga kaisu,  sai dai kayi mata addu'a dan zataje mata har inda take,  Allah yajik'an su baki d'aya. Shiru Barkind'o yayi yana sauke numfashi hawaye suna zuba daga idanuwanshi.

Likita ne yashigo hankalinsa atashe,  tsayawa yayi ya dai-dai ta kanshi ganin halin da suke ciki,  shigowa yayi yana fad'in yallab'ai akwai maganar da nake so muyi. Sakin Barkind'o Hassanu yayi yana goge idonshi yace shikenan muje. Saurin sakkowa Barkind'o yayi yana fad'in Baffa nima kajirani,  ina Modibbo a wane hali yake ciki?  Likita yace ka koma ka kwanta jikinka babu k'wari,  Modibbo yana wancan d'akin bacci yakeyi.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now