Mai Nasara 215-220

1.1K 70 3
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

Page 215 ➡ 220

Majidad'i ya dad'e yana  zagaye a d'akinshi yana tunanin mafita. Jin kiran sallah ne ya sashi shiga band'aki yayo alwala ya nufi masallaci. Har aka gama sallah baiga Mai Nasara yazo jam'i ba. Baffa Barkind'o ma sai da ya tambayeshi yace basa tare. Daga masallacin kai tsaye b'angaren Mai Nasara ya nufa.

*** ***

Mai Nassra kuwa da k'yar yayi sallah yayi wanka ya fito falo saboda kanshi da yake masa ciwo tsabar damuwa. Falmata ce ta fito goye da Bobbo,  ganin Mai Nasara yasa tayi saurin k'arasowa tana fad'in dear ka tashi ashe? 'Daure fuska Mai Nasara ya k'arayi.

Zama Falmata tayi tana fad'in wai wani abu yana damunka ne?  Tunda muke ban tab'a ganinka cikin irin wannan yanayin ba,  ya kamata koma menene ka fad'a mani,  idan nice keda laifi sai na baka hak'uri.

Murmushi yayi yace Allah Aku sarkin magana?  Cike da mamaki Falmata ta kalleshi. Mai Nasara yace tabbas ada kinyi wasa da tunanina,  amma zuwa yanzu na gama sanin ko ke wacece,  kin yaudareni abaya,  amma ina mai tabbatar maki ayanzu nasan komai.

Hawaye Falmata ta fara jin maganganun da suke fitowa abakinshi. Mai Nasara yace ba sai kin b'oye mani komai ba,  domin na riga da nasan komai,  idan dukiya kike so to zan baki,  domin na gajeta gaba da baya.

A firgice Falmata ta mik'e tare da daka mashi tsawa jin irin maganar da yake fad'a mata. Tashi yayi yana fad'in babu wata borin kunyar da zakiyi mani,  kin gama cuta ta sannan kizo kiyi mani jan ido. Idan Hamma ne ba sai kinyi haka zan bar masa ke ba,  domin tun kafin muyi aure kin tab'a tambayata ko zan iya bar masa ke,  ashe dama kina da wani k'udiri aranki.

Falmata kin bani kunya,  mai yasa tunda kikaga Hamma Maina kikaji kina sonshi baki fad'a mani gaskiya ba?  Idan shine yace na bar mashi ke bazan tab'a bar mashi ba,  amma idan kece kika ce mani kinfi son Hamma akai na tabbas zan bar maki shi,  domin arayuwata babu abinda na tsana irin son maso wani,  gashi abun bakin cikin ma har munyi aure hada k'aruwa.

Jikin Falmata ne ya fara rawa jin abinda Mai Nasara ya fad'a,  kanta ne ya fara juyawa,  tabbas yanzu kam ta gane inda ya dosa,  kuma ayanzu ta gano bakin zaren,  dama tasan Maina bazai tab'a hak'ura da ita ba,  kuma tasan wata rana dole ya nuna ma wani abinda ya shirya.

Zubewa tayi k'asa ta rik'e k'afafuwan Mai Nasara tana wani irin kuka,  jin hayaniya yasa Bobbo ya farka,  nan shima ya saki kuka. Saurin juya mata baya Mai Nasara yayi,  dan yayi alk'awarin a wannan karon bazai bari ta sake yaudararshi ba.

***

Majidad'i da yake ta faman buga k'ofa, jin shiru yasa kawai ya murd'a k'ofar yashiga. Tsaye yayi yana kallon abinda bai tab'a gani ba. Gyaran murya yayi tare da sallama. Falmata tana juyawa taga shine tayi saurin tashi ta shige d'aki da gudu tana kuka.

Juyowa Mai Nasara yayi yana amsa sallamar fuska cike da damuwa. Da sauri Majidad'i ya k'ara kusa dashi. Zama sukayi Majidad'i yana tambayarshi lafiya?  Tashi Mai Nasara yayi yaja hannun Majidad'i suka shige d'akinshi.

Suna zama Mai Nasara ya kifa kanshi saman cinyar Majidad'i had'e da sakin wani irin kuka. A rikice Majidad'i ya kama kafad'arshi yana tambayarshi abinda yake faruwa,  domin yasan matsala suka samu da Falmata tunda gashi ya ganta duk'e ak'asa tana kuka.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now