Mai Nasara 160-165

1K 61 3
                                    

🙋🏻‍♂MAI NASARA 🙋🏻‍♂
   (A book of true love story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

Page 160 ➡ 165

Da sauri Maina ya d'auki lambar ya danna kira,  sai da tayi k'ara har ta katse ba'a d'auka ba,  sake kira yayi yana fad'in d'auka mana MANGAL. Ta kusa katsewa aka d'auka.

Da sauri Maina yace haba Mangal ina kashige haka ne?  To Maina Fufore ne. Dariya Mangal yayi yana fad'in Maina Fufore ashe kana tunawa damu? Maina yace Mangal nasan kadawo tunda naji wayar ka ta shiga,  kana ina yanzu?  Mangal yace naje Abuja wani aiki lafiya dai?  Dafe kai Maina yayi yana fad'in ina cikin matsala Mangal,  yaushe zaka dawo?  Mangal yace bazan wuce sati biyu ba.

Iska Maina ya nausa yana fad'in sati biyu yayi yawa Mangal,  nan da sati biyun zan rasa abinda nake so. Yanzu dai ina yaranka suke?  Dariya Mangal yayi yace Maina da alama kana cikin damuwa,  ashe dai akwai ranar da zanyi maka amfani amma kake wulak'anta ni.

Maina yace dan Allah kabar wannan maganar,  to kayi hak'uri yanzu ina neman taimakon ka. Mangal yace akan menene matsalar ka?  Maina yace akan Mace ne,  ina matuk'ar sonta,  zan iya rasa raina idan ban sameta ba kataimaka mani dan Allah,  bani da wani wanda zanje ya taimakeni sai kai,  sanin kanka ne bana harka da kowa,  kaima Allah ne yasa zamu sake had'uwa shiyasa har kace na baka lambata.

Mangal yace lallai kam Maina dole na taimaka maka,  domin nasan halinka,  tunda muke makaranta ba'a tab'a samunka da wata mace amatsayin budurwar ka ba,  hakan ya nuna mani kana matsanancin son wannan yarinyar.

Maina yace yanzu nan da sati biyu za'a d'aura mata aure gashi kace a lokacin zaka dawo dan Allah ka rage. Mangal yace kada ka damu,  nan da kwana goma zan dawo,  akwai yarana da suke nan zamuyi waya dasu,  zan shirya duk yanda komai zai kasance,  dan haka sai ka bani labarin yanda komai yake.

Maina yace bana so ka kalli wanda zan fad'a maka amatsayin komai nawa,  ka d'aukeshi wani can daban,  nasanka Mangal,  nasan ka iya duk wani aiki,  tunda har ka iya aikatar da shed'anci a Sudan nasan zaka iyayin komai a nigeria.

Mangal yace shikenan yanzu dai bani labarin........ Gaba d'aya abinda yake faruwa ya fad'a mashi,  anan Maina yace dan haka na baka zab'i,  duk abinda ka yanke akan wannan abun bani da damuwa,  nidai koma menene kada ya shafi Falmata ta,  daga ba ita ba koma waye idan zai kawo mani cikas akan samun Falmata ka d'auki mataki akanshi. Dariya Mangal yasa yana fad'in ashe haka kake Maina?  Ni dama irinku nake so,  bana son harka da masu sanyin zuciya,  dan haka duk abinda zan yanke dole kasa mani ido,  zanyi abinda naga zan iya,  kasan aikina babu tausayi.

Maina yace zuwa yanzu babu sauran wani tausayi a zuciyata idan har zan samu Falmata,  zan iya kauda kowa akanta,  idan nace kowa to ina nufin kowa. Mangal yace baka da damuwa,  tunda kace haka zakaga aiki mai kyau,  sauran kuma ya rage naka domin kasan bazamu saka soyayyarka a zuciyarta ba.

Maina yace kota sone ko kada ta soni idan zata zama tawa bani da matsala,  kasan mace wuyarta baka aureta ba,  dan haka ku barni da ita ku dai kuyi aikin ku,  kuma dan Allah bana son kuyi aiki abar sheda. Mangal yace a aikina bana barin sahu,  kai dai kawai naji shegun. Maina yace ka turo mani da account d'inka. Mangal yace shikenan sai ka jini.

Kashe wayar Maina yayi yana sakin murmushi,  a fili yake furta wannan karon Yazeed sai dai kayi hak'uri,  bazan tab'a barinka ka mallaki Falmata ba. Ke kuma Falmata ayanzu zan nuna maki irin son da nake maki. Baffajo sai dai kayi hak'uri,  a wannan karon ka kasa cika mani burina,  tunda ka raineni a haka ni kuma zan k'arasa sauran,  wannan yakin nawa ne ni d'aya,  rayuwata zan gyara dan haka ban damu ka tayani ba.

Mai NasaraWhere stories live. Discover now