page 9-10

53 7 1
                                    

BA'KAR NADAMA*

NA*
*zeenat deen(SHAXEE)*

*PAGE 9 and 10*

*Dedicated to*
*classic feeydo*


"Kitashi kitafi nace bazan iyayin komai akai ba saidai ki kawo wata bukatar yanzu abiya miki ita." cikin rawar jiki tace."ba bu wata,bukatar sai,dai nan gaba." cikin sauri ta tashi ta futa daga wajan, sauri ta dinga yi harta zo inda tabar motar ta,shiga tayi ta jata aguje.

Gudu kawai takeyi tana tunanin mafutarda zata yiwa kanta.

Tana,zuwa gida ta shige dakin ta,waya ta dakko ta kira aminiyar ta hajiya Rabi wadda suke koman su tare."Hello hajiya Rabi akwai matsala fa." daga can akace."wace irin matsala kuma." duk abunda yafaru ta fada mata,sannan ta dora da cewa" kin san ko me za ayi bazan barshi ya auri yar tala kawa ba." shiru tayi tana sauraran abunda take cewa.Wata irin dariya ta kwashe da ita. "Gaskiya kin iya bada shawara hajiya Rabi yadda kika fada haka zanyi, ai ni nama samu dabara."

"Ok karki damu insha Allah sai ya auri yar ki Jamila ita nake so ta zama siri kata saikin jini." wayar ta kashe tare da yin wani mala lacin murmushi.

Sakkowa tayi daga benan ta,kai tsaye ta wuce kan teburin cin abinci ta zuba masa a faran ti ta dau masa lemo guda daya, dakinsa ta nufa tana zuwa ta tura kofa cikin sa'a ta tarar a bude take, tana shiga ta hango shi akan gado yayi ruf da ciki, kara sawa tayi kan gadon tazauna a kusa da shi.Cikin taushin murya ta fara magana."Daga wannan maganar shine zaka saka damuwa a cikin ranka indai nice na amince ka aureta."

Zabura yayi ya tashi zaune."Da gaske momy kike." " kasan duk abinda kake so ina sonsa dan haka karka damu na yarda ka aureta" "kai amma momy na ji dadi Allah ya barmu tare." "ameen my son ni ko sunan 'yar tawa ban sani ba."

Cikin farin ciki yace."sunanta Muzaina kuma a unguwar su farida take, ko magana ban mata ba amma gobe zanje gidan su." "hakan yayi kyau yanzu tashi ka ci abinci nasan baka ci komai ba."

Amsar faran tin hannunta yayi." yan zumakuwa zan cinye duka in baki kwanan." "yauwa my son bara inje falo."

Tana zuwa falon ta dauki wayar ta ta danna wata nomber."Hello 'baure daga yanzu ka dinga kular mun da duk inda Kamal zai je musammam ma unguwar nasa rawa "Shiru tayi ta na saurarar abunda yace." karka damu da batun kudi kasan baka da matsa saina jika." wayar ta kashe tare dayin murmushi." Zaka gane baka da wayo yaro."Shikuwa Kamal yana gama cin abin cinsa ya bude wani karamun furinji ya dakko kwalbar giyar sa ya dora akai, yana gama sha ya samu gu ya fara barci.

................................................

Musalin karfe takwas na safe Kamal ya tashi, ba batun sallah bare salati wanka yayi yayi shirin futa office, jakar sa ya dauka ya rataya sannan ya futo falo.

Benan momy ya haura dan yaga ya take besame ta adakin taba sakko wa yayi yaci karo da yar,aikin gidan." ke ina momy take." cikin rawar jiki ta zube tace." yallabai tun jiya da daddare ta futa bata dawo ba"

kan tebur ya huce yadibi abinci yaci, sannan ya ta shi yafuce zuwa harabar gidan." kai Edi ka wanke mun motar ne." " na wanke maka tun asuba ma." " Allah ya te makeka da yau ka gane baka da wayo." kara sawa gun motar yayi ya shiga mai,gadi yana rawar jiki ya bude masa get ya fuce.

Kai tsaye office ya huce, yana zuwa ya,futo daga motar ya shige cikin office dinda ya zauna yafara duba ta kaddu,kofa aka turo dago kai yayi yaga Abdull ne. Dan iska tun jiya,nake nemanka a waya ban same kaba akwai labari wallayi." "haba dai nawan wallayi jiya,wata byba na samu muka huta waya ta ma kashe ta nayi shiya sa baka same ni me yafaru." " kai dai zauna,kaji."

" wallahi jiya naje gurin Farida dan inci mata mutun ci in gaya maka sai ga wata byba hadaddiya ga mugun kyau gata yarin ya karama yar gidan tarbiya, kai in takai ce maka na samu matar aure." wani ihu Abdull yayi suka tafa." kace ka kusa shiga daga ciki mun kusa ra'ka shewa yanzu ta amun ce da kai." " ina ko magana ban mata ba amma yau muna tashi daga office can zamuyi mu dai dai ta komai tukunna." " ok ba da muwa bara inje office dina in kara sa aikida huri." fuce wa yayi daga office din Kamal yaci gaba da aikin sa.

Sai misalin karde biyar na yamma suka tashi, nasarawa suka zarce suna zuwa suka kara sa kofar gidan da Kamal yaga ta shiga jiya, wani yaro ya kira yace." kai dan shiga nan gidan kace ana sallama da mai gidan." da gudu yaron ya shige cikin gidan.

Daga can nesa da su wata mota ce baka a tsaye wani mutun ne daga ganinsa kasan dan daba ne ya futo daga cikin motar wayar sa ya dakko daga cikin aljihu ya kira wata nomber.

Ana dagawa yace." hajiya mun biyo shi zuwa wata,unguwar nasarawa daga office ya huce, naga ya tura wani yaro zuwa gidan. " daga can momy tace." na tabbata gidan ne karku bar wajan har sai kun tabbatar gidan su yarin yar ne in shine ku tafi da daddare ku zo ku bankawa gidan huta yakone harda su." " an gama hajiya sai kinji saka mako"

*🤔ko ya zata,kaya su muzaina za a sha huta🤭🤣*

BAKAR NADAMAWhere stories live. Discover now