page 21

67 6 0
                                    

*zeenat deen (real shaxeeee)*

shaxee81@gmail.com
------------------------------------------

*kuyi hakuri da rashin yin type dina jiya wani dan abune ya tsayar dani.*

*duniya bata da tabbas kuma bakasan tsawon kwanan da zakayi aduniyaba, amma mutane muna manta haka muna aikata abunda mukeso ina tsiya ina harkar madigo ga 'kazanta ga jahilci ga rashin jin tsoran allah uwa uba jahannama da kabari suna nan suna jiranka to ina ribar aikata haka allah ka tsaremu da tsarewar ka.*

PAGE 21*

----------------------------------

Biki ya,ma tso sosai yau ake kamun amarya, gidan amarya ya cika ma'kil da mutane ana bidiri suma gidan ango anata budiri domun biki ake nakece raini, amar ya har ta gaji da had'uwa inda ya kwashi abokanan sa yakaisu dan su ga amarya kowa sai fadar kyan amarya yake shikuma,ana 'kara fasa masa kai.

Cikin ikon Allah Hassana anyi mata aiki cikin nasara kuma andace, zuwa yanzu tasamu sau'ki ana saka ran nanda jibu za a iya sallamar ta sha 'kuwa sosai tashi ga tsakanin Hasana da wani likita dector Hashim sosai yake basu kulawa tun umma bata gano shiba harta fahimceshi, kuma tayi murna sosai.

............................................................

A yaune ranar lahidi misalin 'karfe goma na safe aka d'aura,auren Kamal da Muzaina ango anata washe bakiana yin hotuna ana gaisawa,da abokai, daga nan aka huce gidan su amarya aka gaishe da iyayen amarya sannan akayi hotuna daga nan kuma aka huce wajen walima,amma banda su amarya dan tace bazata jeba.gunzul mazaluni ne azaune cikin shigar d'aurin aure gefansa kuma yarima Shubbar ne azaune yana tunani, Gunzul mazalunine ya kalli yarima Shubbar yace." Har yaushe zaka kai kana 'boyewa gimbiya son da kake yimata yanzu wata damace da ka samu kafun mukoma gida ka cusa mata sonka kaga muna komawa sai asha biki." murmushi yayi yace." Abunda nake tunani kenan amna naga gaba daya hanka linta yana kan d'aukar fansa amma zan san hanyar,da zanbi, nabaro garinmu da matsayina duk don sonta nazama bawa ina fatan nima tasoni. " " Nasani yarima nasan komai akanka kuma nima zan baka tawa gudin mawar akan tasoka yanzu tashi muje cikin mutane ko." tashi sukayi suka shige cikin mutane aka cigaba da hada - hada.

Misalin 'karfe biyar na yamma motoci suka fara layi a bakin 'kofar gidan su amarya anata kwasar mutane ana kaiwa gidan su ango dan Muzaina da kanta tace wa kamai agidan su takeson zama dan haka aka gyara mata pat din gefe aka zuba kaya na alfarma.

Farida tana kallon bikin da akeyi amma ko ajikin ta danyanzu jitake duk duniya ba wanda ta tsana sama da Kamal domun yabada gudun mawa gurin lalacewar ta, amma yanzu alhamdulillah gidan su ya gyaru harta kima makaranta.

Ankai amarya gidan ta amma saida aka fara kaita gun momy aka bata ama narta momy bata nuna kimai ba saboda sabon 'kudirin data yi niyar aiwatar wa.

Bayan an bar gun momy kai tsaye kuma akayi pat din ta da ita misakin 'karfe tara na dare kowa ya watse aka bar amarya ita kad'ai, zuwa jimawa kuma saiga ango da abokanan sa an rakoshi anata yima sa tsiya yau zai angwance, sunata sha'kiyan cinsu kozan can addu'a bawanda yayi haka suka watse aka bar ango da,amarya, kulle musu pat din su yayi sannan ya shigo d'akin da amarya take." Yau kin 'ki magana sai wani 'kasa kikeyi da kanki nakusa cire kunyar nan ma gaba d'aya." ita dai ko 'kala bata ce masa ba ledar da ya shigo da ita ya dakko musu gashashshiyar kazace mai albasa sai kuma lemuka da yogot ajiye musu yayi yace." To sai ki sakko muci ko in d'akko ki da kaina." tashi tayi ta cire mayafinta ta sakko ta zauna abaki yake bata yana wani rawar kai ga ango murmushi kawai take yimasa.

Saida sukaci suka 'koshi yanata yimata surutu amma ko cas bata cemasa ba saidai tayi masa murmushi." Yan zu tashi ga kayan barcinan kisa kizo mu kwanta dan agajiye nake yau." gyada masa kai tayi ta tashi rigar da ya ajiye mata agefan gado ta d'auka tashige ban'daki, murmushi yayi yace." Yarinya duk abunki sai yau na lasaki dan bakisan duk zancan danake zuwa gunki kawar da kai kawai nakeyi amma yau zan kwashi gara." kayan jikinsa ya cire ya rage daga shi sai gajeran wando da singileti, zama yayi abakin gado yana jiran futowar ta.

Ita kuma tana shiga bayin ta d'aga rigar, rigace iya gwiywa mai bun jiki samanta kuma uwa bireziyya har ahnnun ma haka." Abun tau sayi yaro daga yau zaka fara 'kirga ranar nadamar ka, kaida mugayen iyayenka." kayan ta ta cire tasaka rigar sannan ta futo cikin yanga,tana wani jujjuya jiki,mutuwar,tsaye yayi a inda yake tundaga sama har 'kasa yaje kallonta yana wani lashe baki, tawowa yayi da niyar rungume ta amma sai jikake yi timmmm!ya fadi a 'kasa yadena motsi sai futar numfashi kawai yakeyi da munshari, wani murmushin mugunta tayi.

BAKAR NADAMAWhere stories live. Discover now