page 28

65 5 0
                                    

*masoya ina tayaku murnar sabuwar shekara allah yasa alherin daya ke cikin wannan sherar ya samemu*

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*HAPPY NEW YEAR 2019*

💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻

*saboda,murnar sabuwar shekara nayi muku page din me auki asha karatu lafiya*

*NA*
*zeenat deen (real shaxeeee)*

zeenatdeenshaxee@gmail.com

*page 28*

--------------------------------------

Kansa,sukayi aguje suna gurgiza shi ammako motsi beyi ba. '' Momy muje mukai shi asibiti karya mutu.'' kinki mar sa sukayi zasu futa dashi sukaci karo da Muzaina. '' Gidan uban wa,zakuje.'' cikin kuka momy tace. '' Alhj ne ya yanke jiki ya fad'i ko motsi bayayi shine zamu kaishi asibiti.'' ''Dalla can rufemun baki ku maida shi,ku yayyafa,masa ruwa,sannan kubashi shayi yasha ze,dawo dai dai.''
ijin rashin 'kwarin jiki suka maida shi,suka shimfud'e shi ruwa Kamal ya dakko ya yayya fa masa wata irin ajiyar,zuciya ya saki sannan ya bud'e idonsa, da sauri momy ta had'a masa ta bashi yashaYana gama sha suka kamashi suka jinginar da shi. '' To maza atashi acigaba da aiki shikuma inya warware zuwa anjima yayi nasa.'' jiki ba kwari haka suka cigaba da aiki seda suka gana tas sannan kowa ta bashi shayi rabun kofi da biredi yanka uku uku, haka suka amsa suka sha. '' To maza kuje kuyi shirin futa office ku tafi kuma karfe uku nakeso ku dawo gida.'' gyada mata kai sukayi suka shige dan yib abunda tasa su.

waje ta samu ta zauna tana karin kumallonta cikin kwanciyar hankali.

Zuwa yanzu sun rame sun fige sunyi baki dasu Abdull ba tambayar,da beyiwa Kamal akan ya fada masa abunda yake faruwa ba amma sedai kawai yasa masa kuka baya iya cewa komai.

Hatta gun aiki yanzu ba kullun take barin su sujeba kamfanin su yafara dur 'kushewa wasu daga cikin ma aikatan suna satar kudi ahankali batare da an ganeba.

gaba d'aya ma ta tattara su ta maida su 'bangaren da 'yan aiki suke zama suma can ta maida su gaba daya,ga ba suturar kirki duk ta 'kace ta bayar da su.

Momy ce zaune a'kofar dakin da suke tana yimusu wanki gefen ta kuma daddy ne yan yanke,fulawa da almakashi kamal kuma yana can gefe yana goge motar da ba acika hawan taba amma kullun se anwanke sau biyu.

Momy ta kalli daddy tace. '' Wai ni me yasa meka kwana biyun nan ne kullun kana hanyar band'aki.'' girgiza kai yayi sannan yace. '' Nima,ban saniba amma yanzu bana iya ri'ke kashi da futsari koyaya ne in banje nayiba seya zubo na rasa wannan dalilin.'' kyabe baki tayi tace. '' Nima kwanan nan bana jin dadin jikina ga tari ya sani agaba amma yanzu bamu da damar da zamuje asibiti eannan yarin yar ta samu a bala i duk kyawayena da abokanan harkata duk sun gujeni yanzu bamu da kowa dama tun shekarun baya mun bar garin dangin mu yan zu bama susan a inda mukeba bare wani yazo ya temaka mana.'' '' ke yanzu atu nanin ki ko sunsan inda muke zasuso kema kinsan hakan baze yuhuba.''shiru kawai tayi domun ta tuba abunda ya faru abaya.

----------------------------------

Muzaina,ce azaune apat dinta,tana hira da Gamzul mazaluni dazu ta kirashi. '' Ina so su shiga mummunan rayuwa yau da daddare nakeso kamfanin su guda uku na sarrafa lemo dana sarrafa fata dana sarraba karfe ayau nake so kaje ka kunna musu hutar da bazata ta'ba mutuwa ba har se komai ya 'kone 'kurumus ginin ma ya rushe sannan agobe nakeso bank suzo su 'kwace gidannan sannan ragowar,kasansu.'' sun kuyar da kansa yayi. '' Angama ran gimbiya ya dad'e.'' 'bat ya 'bace ita kuma gimbiya ta kwanta,tana sana ar ta ta ta tunanin yarima Shubbar.
Zuwa,can ta tashi tayo waje inda su Momy suke da zama ta zo. '' In kun gama wannan aikin da kukeyi maza,aje amun girki yau zanyi baki basu muhimman ci kuma dayawa zasukyi shi kunjini. '' gyada mata kai sukayi ida nuwan su yana kallin 'kasa dan ko kallonta basa iya yi.

Suna gamawa suka shiga aikin girki se sallar,magari ba suka gama suka jere komai akan tebur suka feshe dakin da turaren huta sannan suka tawo inda suke zaune.

Gimbiya Muzaina kuwa taci kwalliya iya kwalliya ta,hakimce a kan kujera, zuwa can sega yarima Shubbar ya bayyana cikin kwalliya shida wasu samari guda uku, cikin farin ciki ta tare su ta basu gurin zama can se ga mutane sunata bayyana yarima kuwa shida gimbiya se satar kallin juna sukeyi suna mayar wa da juna murmushi.

Misalin karfe biyun dare Gamzul mazaluni ya kunnawa kamfamin su Kamal huta,gaba daya sannan ya 'bace.

Se zuwa safiya,sannan daddy da su Kamal suka ji wannan mugun labarin, ba 'karamun hauka sukayi ba kasan cewarsunsan shine,madogarar su in banda kuka ba abunda sukeyi wasu mutane suka gani su uku da ba 'ka'ken kaya hannun su d'auke da littafi. '' Yauwa alhji Hashimu munji dadin samunka a gida.'' wani mugun yahu ya,hadiya,kasan cewar yasan meya kawo su shi kwata kwata ma ya manta . '' to jiya ne ranar,da alkawarin mu ya cika munji ka shiru shiyasa,buka biyo ka ina kudinmu.'' wani mugun hawaye ne yazubo masa. '' wallayi ranka ya dade nashiga wani haline kamfanina duka sunkone ku temaka mun ku rifa mun asiri. '' Kaga tsaya malan da kata ba a haka damu dan haka mun rike ta kaddun ka duka dan haka mun baka kwana uku kabar gidan kuma bazaka dau komai ba.'' kuka yake yana rokon su a mma ko ta kansa basu bi ba suka fuce.

'' Alhj dama baka biyasu kudin ba yan zu ina zamuje mun shiga uku dama haka duniya take abunda,muka aikata ne ya fara bibiyar,mu munshiga uku.'' gaba,dayan su kuka suke Kamal yakasa ma magana illa rike kansa da kawai yayi.

'' Yan zu har ku zaku fara nadama muta nen banza mura nen hofi jibi in rayuwar ku ta gama tagayyara zan fada mukudalilin daya sa na shigo rayuwar ku se kunyi BA'KAR NADAMA arayuwarku.'' ta sa kai ta fuce daga gidan zuruu sukayi suna kallonta.

BAKAR NADAMAWhere stories live. Discover now