page 30

49 5 0
                                    

*NA*
*zeenat deen (real shaxeeee)*

zeenatdeenshaxee@gmail.com

*facebook*
*zeenat deen*

*page 30*

-----------------------------------

‘’ Alhji muntari ya taso agidan marayu anan yayi rayuwar sa acikin gidan yasami wata yarinya me suna Binta sukayi aurensu cikin kwanciyar hankali suna matukar,son junan su ahaka suka haifi dan su na fari me suna Ahmad suna matukar sonsa Allah ya buda masa yazama me arziki ahaka suka haifi Salma sunbawa ya yanzu tarbiyya ta gari suntaso cikin kaunar juna haka suke rayuwar su ba bacin rai Salma ta hadu da wani saurayi agidan marayu kasan cewar suna zuwa ziyara sunan sa Huzaifa suka dara soyayya sanda mahaifin ta ya fuskan ci haka seya dakko Huzaifa daga gidan marayu ya dawo dashi gidansa ya dora shi akan dukiyarsa ya rike da amana ahaka aka saka musu rana bikin su saura wata uku rannan Alhji  Muntari ya kade ka kai Hashimu bayan ya kaika asibiti ya fuskanci kuna fama da talauci kaida matar ka da danka Kamal hakanbe yasa ya kaiku gidansa kuke zaune acan kuna cin arziki ya janyoka ajikin sa kaida danka ya kaiku,kamfanin sa, ashe kukuma muna fukaine kuka yi buncike akan dukiyar sa, alokacin be rage ku da komai ba kuna hawa mota kuci me dadi ku kwanta agu me dadi, kai kuma Kamal dayake dan bunsurune ka kullawa Salma amma baka samu dama,ba bikin ta saura,sati uku wata rana da daddare kuka hada baki da 'yan fashi kukazo gidan kuka tilas tawa baban Salma yasa hannu a takadda wacce take dauke da cewa ya bar maka dukiyar sa gaba daya, shikuma Kamal a ga ban iya yenta da mijin dazata aura da wanta kayi mata fyade wanda dalilin da yasa mahaifiyar ta zuciyar ta tabuga agun ta fadi matatciya Huzaifa yayi yunkurin kwatar ta amma kuka harbe shi ya mutu agun sanban kuka harbi ma haifinta ganin haka yasa Ahmad ya dauki Salma ya shige wani daki kuna kokarin balla kofar Alla ya temakeji ya dankawa salma wata karamar walet yana kuka yace mata Salma kiceci ranki ki gudu ki tsira nasan nima mutuwa zanyi duk da a nmiki tabon da baze taba warke waba amma kije tayu akwai abunda Allah ya tsara miki akau abu buwa da yawa acikin jakar nan rawa kiyi amfani da shi.‘’ tana zuwa nan ta tsaya da,magana idon ta yayi wani mugun ja wani kallo take yi musu su kansu hantar cikin su in banda dusko ba abunda ta keyi.

Ci gaba da cewa tayi. ‘’  Tana kuka tana rike masa riga tana girgiza kai amma ahaka ya kauda kai ya cillota ta tagar bayan gidan su ta fado suna kuka suna kallon juna amma haka yayi mata nuni da ta gudu duk da ta gala baita amma ahaka ta shige jejin bayan su Ahmad yasan shima ze iya fadawa ya bita amma indai yayi haka to yasan dole sesun bisu kuma zasu iya kamasu su kashe su gwara ita ta tsira haka kuka balla kofar dakin kuka shiga tambayar duniyar nan kunyimasa ina,Salma amma yaki fada muku haka kuka harbeshi ya mutu, Salma taji karar harbin wanda yasata kara sautin kukan ta domun tasan kuk kashe mata wanta kunyi ne manta amma baku samu ba dan ta buya awani haka kuka koma jakar da wanta ya bata ta bude takaddar wani tsohon shagone da ya siya wanda ajikin wani gida shagon yake amma gidan ya ruce yana shirye shirye gyarashi se mukullin shagon da kuma atm dinsa dama tasan code din se kudi aciki da hotonsu dukan su harda Huzaifa ma ajiki ahaka taje wannan gidan ta bude,shagon ba komai aciki gashi asuba tayi alokacin haka ta zauna tana kuka da tunanin abunda ya faru da ita, seda tayi kwa biyu a shagonnan baci ba sha se kuka da tunani gashi sabuwar unguwa ce ba gidaje se kanguna wadan da aka fara gini amma ba a kara saba, haka ta futo tana da yawo har Allah yasa ta samu shago tasiyi biredi da lemo,tasha ta koshi sannan ta tafi bank ta ciri kudi ta tafi kasuwa ba mayafi ajikin ta se dankalinta wanda ta cire ta yafatake yawo ahaka me adaidai ta tasamu take loda kayan aciki katifa 'karama da tabarma babba tukunya da rushi karami barko da kayan abinci se dogayen riguna da wanduna da riguna ta siya da hijjabai manya da daddama da kur'ani  da carbi, haka ta zo me adai dai tar nanne yate maka mata ya jera mata komai ganin halin datake ciki yasa bai anshi komai ba, haka ta samu kwalaye ta rube bandakin gidan da ya rushe akwai wata rijiya gaba da ita nan take zuwa tana dibar ruwa tayi wanka girki da alwala kullun cikin kuka da tunani da addu a take allah ya bi mata hakkinta kukuma kuka hau kan dukiya kuna sha aninku yadda kukeso Kamal kanayiwa mata fyade kuma ba wanda ya usa ya hana ka, bayan wani lokaci Salma ta fuskanci tana sa ciki tayi kuka iya kuka amma batayi yunkurin zubarwa ba haka take ratuwa in kudinhannun ta suk kare seta je ta kuma debowa kasan cewar kudin dayawa cikinta yakai wata bakai kullin sai tayi kuka haka taje kasuwa tase kayan baby ta ajiye tana tunanin ya haihuwar take waze temaketa amma bata fasa addu a ba.‘’ shiru ta kuma yi ta share hawaye wanda suma shi sukeyi.

*kuyi maleji da wannan bana jin dadi*

*shin ina salma ina dan data haifa ko ya muzaina zatayi dasu kamal zata barsu haka kuwa koza kuma yimusu wani abun*

*in naga comment da yawa to gobe zanyi type🤨🤑*

BAKAR NADAMAWhere stories live. Discover now