page 25

71 6 2
                                    

page 25*

-----------------------------------

Yana gamawa yayiwa momy sallah ya fuce,wani mugun murmushi tayi. “ A gaskiya aikin boka yana yi jibi ba musu ya amunce yarinya zaki gane baki da wayo sai kin gudu da kanki dan wahala sannan in aurawa dana yarinya yar gidan madu arziki.” kujera ta koma ta zauna ta kunna kallo tana jiran ba'kon ta.

Yana shiga pat din ya tarar ba kowa d'akinta tashiga nan ma bata nan ko ina ya duba be ganta ba wayar sa ya dakko ya hau kira tana cikin ringin yaji an daga. “ hello wanene.” wani dummm ya ji muryar namiji a wayar matar sa cikin bacin rai yace. “ Mijin me wayar ne ina take.” wata,muguwar dariya akayi sannan akace. “ Wannan kuma matsalar kace barci takeyi inta tashi za a gaya mata.” kafun yayi magana har ankashe kara kira yayi yaji wayar a kulle, duk inda tashin hankali yake ya bayyana a fuskar sa safa da marwa kawai yakeyi. "dama haka halin yarin yar nan yake, inahh baze yuhuba bara ta dawo ta gani." sai zagaye daki yakeyi bini bin ya kalli bakin kofa duk abunnnan dayake yi Muzaina tana kallonsa akan kujera, tun yana tsaye harya zauna kai harya kwanta besan sanda barci ya daukeshi ba dama ga gajiya.

Misakin karfe tara ya farka daga barci ganin Muzaina yayi azaune rana kallo tashi yayi zaune." madam harkin tashi kenan." wani kallo tayi masa na hula kanci." tun dazu kake,barci uwa wanda ya mutu maza tashi kaje kamun abun kari." sum - sum,ya tashi ya huce kicin shi kanshi ma makin kanshi yaje yi,maiyasa baya yimata musu,me yasa yakasa yi mata maganar jiya, haka ya dafa mata shayi ya soya mata dankali ya kawo mat." Yauwa maza a gyaramun gida ko." haka ya hau shara da goge gogesaida ya gana tas yazo da zummar d'aukar ragor abun kari yaci saboda yunwar da yake ji, tas yaga faranti ancinye komai, haka ya shige dakinsa yayi wanka ya yi shirin futa office hutun sati biyu ya dauka dan cin amar,ci amma komawa zaiyi amarci yaki cihuwa, yana futowa ko takanta bebiba ya nufi pat din momy dan yaci abinci.

Yana shiga ya ga teburin wayam,ba komai, wata irin mutuwar tsaye yayi to ina abun karin, can saiga mimy ta sakko daga bene." momy yabaga ba abinci me yan aikin nan sukeyi da,basu gama ba." washe baki tayi. " Tun dazu na salla mesu dama yanzu nake cewa bara inkira ka ka turo matar ka tayi abun kari da gyaran gida." bunta da kallo kawai yake yi cikin zuciyar sa yace. " lallai ma momy dakin san na pat dinmu ma ninake gyarawa da bakiti wannan gaggan cinba." katse masa tuanin tayi. " Maza jeka kirata hunwa nakeji. wayar sa kawai ya dauka ya kirata tana d'agawa yace. " kizo pat din momy tana son ganin ki." bejira ansar taba ya kashe gu ya samu ya zauna dan ganin ikon Allah.

Kifa aka turo cikin kwalliyar tana taunar cingam." gani ko." eani kallo momy tayi mata sannan tace. " Dama 'yan aikina na sallama gaba daya daga yau kezaki dinga yin komai harda wankin mota girki da shara goge goge  harda wanki da guga." wani mala lacin murmushi tayi sannan ta kalli Kamal tace. " Tashi ka tafi office din ka ango." kalmar ango da ta fada ta bata masa rai haka ya tashi ya,fuce daga pat din.

*kowane hali momy zata kasance nidai harna fara tausaya mata😕*

BAKAR NADAMAWhere stories live. Discover now