page 17

57 4 1
                                    

*godiya mai tarin yawa,gareku masoyan bakar nadama Muzaina tana gaisheku dan naga masoyanta sunfi na kamal yawa da fatan zaku kaimata ziyara garinsu ammafa banda ni inkunje ku gaisheta🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀*

*page 17*



Ihu ne kawai yafara tashi acikin gidan, na mata da maza sautin dukane yake tashi tako ina,har tsawon mintina 40mn sannan sautin ya dauke, akofar gida su Farida suka tsinci kansu,cikin wahalalliyar murya Zara tace."Wai me yasa memune haka." jan jikinsa goje yayi da kyar ya jingina, sannan yace."Duk yadda akayi mala ikune suka kawo ziyara duniya, wannan irin duka haka mutun baxai iya yinsa ba ido na daya ahalin yanzu bana gani dashi allah isa ba makan cewa nayiba, wayyo Allah na."Farida kuwa ko magana bata iyayi.

Suna cikin wannan halin baban Farida ya futo ya gansu, cikin tashin hankali ya taro mutane akayi saurin dibarsu zuwa asibiti.

Suna zuwa aka amshesu cikin gaggawa, saboda Farida ta fara zubar da jini sosai, likitocine suka rufu a kansu suna basu temakon gaggawa.

Baban farida kuma yaje gun yan sanda domun likitoci sunce saida 'yan sanda zasu amshe su, ganin zubar da jinin da Farida takeyi ne yasa suka amshe su.

................................................

A Falo su Kamal suketa war ka jaminsu, sai hira ake ana abun dariya,can Kamal yace."Daddy nifa tashi zakayi ka bani tsarabar Muzaina in kai mata kuma wallayi ni gibe nakeso aje a tambayo mun aurenta harda kudin zance da sarana zaku tafi."Haba my son kabar baban naka yahuta mana in an kwana biyu sai yaje ko." "Haba dai momy sokike baban ta ya hanani itafa saida nayi masa alkawarin zanturo yana dawowa." "To amma my son ka......" "Kuda kata haka indai nine gobe zanje in tambayo maka auren, tun dazu ake bami labarinta nasan kana sonta sosai." " Sosai kuwa daddy nidai bani tsarabar in kai mata." tashi yayi ya haye saman benan sa jimawa kadan ya dawo d'auke da karamar akwati, mi'kawa Kamal yayi."Gashi a gaishe mun da ita." cikin hanzari ya tashi ya amshi jakar yafuce cikin sauri.

Momy ce ta dawo da han kalinta kan Daddy tace."Wai ni alhji meyasa zaka biyewa yaron nanne kar fa talakawa ce kanaso mu hada jini da talau cine karfa ka manta kin talau cine yasa muka aikata wannan abun abaya." "Na sani tass kuma nasan abunda nakeyi, babu ruwana da talaucin su tunda yarona yana son ta angama magana, kuma bana so ki 'kara tada maga nar nan." ko kallonsa bata kara yiba.

................................................

Kamal kuwa saida ya tsaya a ahagon saida waya yasai mata waya mai kyau da tsada sannan ya nufi gidan su, yana zuwa ya tura aka kira wota, jim kadan sai gata,cikin kyakykyawar shiga."Ina huni." "Lafiya kalau amar yata."sun kuyar da kanta tayi 'kasa."Kedai kin fiya kunya amma kunyar 'kara miki kyau takeyi, to albishirinki yau daddy na ya dawo kuma gobe zai zo ya nema mun aurenki." "Kace mun kusa mallakar junan mu amma na yi farin ciki sosai." "Ai duk farin cikin ki baki kainiba gama tsara barki yace in kawo miki kuma yana gaisheki." "Kai amma ina amsawa daga gani daddyn nan naka yana ji da kai." "Sosaima kuwa sai kinga yadda yake ji dani." "Bara in koma gida kasan abba ya hanani dadewa awaje." "Nasani ungo ki gaishe mun da yan gidan kinji tawan." Murmushi tayi ta amshi ja'kar ta shige,gida, mota ya koma ya ja ta aguje yabar unguwar.

Ana kiran sallar magariba ya koma gida, bega kowa a falon ba dan haka kai tsaye dakinsa ya huce, kwanciya yayi akan gadonsa yana tuna hirar sa da Muzaina yana murmushi shi kanshi yana mamakin irin son da yake yimata, wayar sa ce ta katse masa tunanin da yake yi,dakko wayar yayi daga aljihunsa, sunan Abdul ya gani dagawa yayi." Hello aboki ya akayi ne." daga can akace." Wai yau bazaka je clup bane." " Yau bazan sami damar zuwa ba saboda zan bude sabuwa aleda." "Shege kace zaka huta sai naji labari." wayar ya kashe ya ajiyeta, tashi yayi ya cire kayan jikinsa ya fada wanka.

Yana futowa ya dakko wayar sa nomber momy ya kira tana dagawa yace." Kituron wannan yarinyar sabuwar yar aikin ki ta kawo mun bakin shayi da shawar ma."

Besau rari abunda zata ce ba ya kashe wayar sa, tsawon mintina 50mn sannan aka turo kofar daki, dauke take da tire a hanun ta,a durowar kusa da gado ta ajiye masa, tsugunnawa tace." Yalla'bai gashi hajiya ce tace akawo maka." tashi yayi daga shi sai tahul a d'aure a kugunsa kofar ya mayar ya kulle ta sanban ya kashe hutar d'akin.

BAKAR NADAMAWhere stories live. Discover now