page 33

109 6 0
                                    

_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_.

https://m.facebook.com/Zamaniwritersassociation?

----------------------------------
*DEDUCTED TO*:
OL BAKAR NADAMA FANS🤝🏻

*komai yayi farko,to zaiyi karshe yaudai allah yakawomu an gama bakar,nadama kuma naji matukar,farinci akan sakwannin ku duka masoyan bakar nadama nagode muku sosai sai mun hadu wani sabon littafin😘😘😍*

--------------------------------------

*NA*
*Real shaxeeee🍒*

zeenatdeenshaxee@gmail.com

🔚

*page 33*

--------------------------------------

Tun suna gudu da karfi har suka fara faed'uwa suna tashi amma da sun juya bayansu sai suga,har yanzu basu dena binsuba,ba 'karamun gala baita sukayi ba sanadiyyar haka,suka yanke jiki suka fad'i acikin yashi suna maida nun fashin wahala,ko ido basa iya bud'ewa sosai.

Sunda d'e a wannan halin zuwa,can suka bud'e idonsu ganin su sukayi a cikin wannan kurkukun azaune gefe kuma abinci ne an ajiyemu su, aikwa cikin hanzari suka jan yoshi suka hau yimasa wa wa, suna gama ci,suka kora da ruwa, suka fara maida nunfashi.

Cikin waha lalliyar murya Kamal yace. ‘’ Nayi dana sanin kasan kasan cewa ta d'anku ina ma ace nazo agun iyaye masu tsoran Allah wa d'anda zasu saka ni a hanya mai kyau da yau ban kasan ce acikin wannan halin ba, kujibi halin da muke ciki ko agidan yari bazamu yi wannan waha lar ba gaskiya kun cuci rayuwa ta kun sani a hanya mara 'bulle wa.‘’ wata gun tuwar 'kwalla daddy ya goge sannan yace. ‘’ Duk lefun a guna yake da naji maganar iyaye na ban auri wannan ala 'ka 'kai din ba da ban ban shinga wannan halin ba da tunu ina gaban iya yena ko yanzu suna raye ko sun mutu ban saniba gashi ban nemi yafiyar su ba, kai cona na shiga uku.‘’ hannu ya d'ora aka yana sabon kuka.

‘’ Wai ni zaku d'orawa lefun duka nima nadamar guduwa,nakeyi daga gun iyaye na sun bani tarbiya mai kyau amma son abun duniya da kuma zigar 'kawaye yasa nagudo daga gida yanzu ta ka mai-mai ma ban san inda suke ba yan zu ina zan sa rayuwa ta.‘’ kowa acikin su kuka yake da dana sanin abunda sukayi wadda za ace bata da amfani.

Watan su uku ana azaba tar dasu sun rame sosai ga wasu 'kuraje da suka fesowa momy ajikin ta kota ina shikuwa,daddy 'kananun tsutsa ce take futowa daga gaban sa da wani ruwa mai doyi ga rashin rike fitsari da kashi Kamal kuwa gaban sa ya kunbura ya yi ja ga masifar ciwo yake yimasa.Soyayya kuwa ta  'bar ke tsakanin yarima Shubbar da gimbiya Muzaina  har sarki yasan da wannan zan can dan haka yau ya tarasu a fadar sa. ‘’ Gimbiya naji ance soyayya kuke da yarima shin da gaske ne.‘’ ‘’ Hakane ya baba na wannan zancen gaskiya ne amma abunda ya ke tsaya mun arai shine wanene shi har yanzu nakasa sani.‘’ wani lallau san murmushi sarki yayi sannan ya kalli gimbiya yace.‘’ Yarima ba kowa banr face d'an gidan abokina Nafsul - Muluk sarkin garin Fudal yabu kaci yana sonki nikuma,bazan ta'ba miki auren doleba shiya sa nasashi ya zo miki ta wannan siffar, kuma mun sami nasara awannan lamarin  duk wata hanya da zaki gane na toshe ta dan haka mum fara shirye shiryen aurenku.‘’

Wani farin cikine ya lullu'be ta tashi tayi ta,bar fadar mahaifin nata zuwa,d'akin ta.

Biki akeyi na kece raini ko ina na garin aljanu sunsan ana wannan biki.

Yaune,daurin aure sannan adau amar ya zuwa garin Fudal dan haka gimbiya taje gun da akaaji ye su momy saida,ta 'kare musu kallo tas in ba wanda yayi musu mugun gani ba bazai ta'ba gane suba saida,tayi dariya,sannan tace.‘’ Ayan zu burina ya,gama,cika jibi yadda kuka dawo kai Hashimu jibi yadda ka koma kana bun yara 'kana na kuma lala ta kuma 'yan uwanka maza jibi yadda tsutsa take zuna ajikin ka ga doyi mai ribar abunda ka aikata kekuma jibi jikin ki duk 'kuraje ga,gudawa to saka makon bin mazan ki kin kwaso cutar 'Kanjamau kai kuma Kamal nasa an maka hakane domun har,duniya ta nad'e bakai ba sake kusan tar wata mace zan cire maka zafun da kakeji amma daga yau ko mace ka gani guduwa zakayi, dan haka yau za a mai da ku gobe ma,kwa sake abun da,kukayi.‘’ kuka kawai suke yi fucewa tagi daga gun, sukuma suka ji wata iska basu san mai yakumma faruwa ba sai ganin su sukayi awannan gidan da aka d'au kesu.

Haka suka cihaba,da rayuwa cikin 'kunci da nadama ga wahalar abunda zasu ci ga momy ta kwanta,ciwo ba 'kudin asibiti duk wanda suka sansu sunje,sun 'ki tai maka musu, haka sunaji suna gani  momy ta mutu da 'kar aka samu liman ya,hada mutun biyat suka kaita kabar aka barta,da abunda ta aikata ba mai cecenta, daddy ma ya kwanta ciyo sosai tsutsar ta'ki daina futa ba wanda yake zama akusa da shi saboda wari.

Bayan sati uku shima ya mutu aka kai hi Kamal yayi kuka iya kuka nadama yayi ta sosai haka yaci gaba da rayuwa yana naiman afuwa agun Allah.

Shikenan fa duniyar abunda kayi shizaka tarar a karshen rayuwar ka mene ne amfanun abunda,sukayi yau ina kudin da matsayi duk babu.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 15, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BAKAR NADAMAWhere stories live. Discover now