page 16

54 3 1
                                    

*DEDICATED TO*
*zamani writers association ana mugun tare🤝🏻*

*page 16*

Da gyare gyare aka tashi agidan su Kamal yan aiki ne kawai suke aiki wasu kuma suna ta girke girke kala - kala ita kuma momy tana zaune akan kujera tana basu umarni.“har yanzu  Kamal baidawo ba bara in fada masa,gashi na kira wayar sa wata mace ta dauka tace yana barci.‘’ momy ce taketa surunta,tana danna waya.Sai misalin 10:15mn sannan Kamal yadawo gidan.“Lafiya dai momy naga anata gyaran gida maga kuma sababbun ma aikata agidan.” cikin fara a momy ta jawo hanunsa ta zaunar da shi akusa da ita tace.“Jiya da daddare daddyn ka yakirani a waya yake cemun yau zasu dawo, nata kiran wayar ka baka daga ba daga baya wata yarinya ta dauka tace mun kana barci, ganin aikin dayawa ne shiyasa nabugawa hajiya Rabi waya, nace ta sa akawo mun wasu yan aikin shine fa suketa aikin.” “Kai amma najin dadin wannan labarin kice yau akwai  chasu, bara inje inshirya nima kan muje d'akkoshi momy.” “Yauwa my son maza jeka” tashi yayi ya shige cikin dakinsa wata yarinya yagani tana goge masa kan mudubi daga gani tana daga cikin sababbun yan aikin da aka kawo yaune bata fi shekar 16 ba tsugunnawa tayi cikin girma mawa.“Ina kwana yallabai.” hannu kawai yadaga mata, tashi tayi tafuce daga dakin harta futa yana kallonta.“Kai amna yarinyar nan tanada kayan aiki masu kyau.” ya fada yana shafa fuskar ta shiru yayi sai kuma ya gyada kai, yayi murmushi, kayansa ya cire yashiga ban dakin sa.

………………………………………………

Farida ce atsaye akofar gidan su ita wata kawar ta mai suna Zara, hanya kawai farida take kalla, cikin 'kagu wa Farida tace.“Har yanzu su goje basu kara soba.” kallon hanyaZara tayi sannan ta dawo da hankalinta kan Farida tace.“Kikwan tar da han kalinki 'kawa ta nasan suna hanya tayu wani abu suka tsaya yi.” “Kedai bari yau iyayen wata yarinya da yarinya zasu gane,basu da wayo dan nace su goje su hado kayan aiki da yawa dan yau ba mutunci kawata.” Tafawa sukayi cikin dariya.

…………………………………………

Karfe shabiyu a filin jirgi tayiwa Kamal da momyn sa, iyanzu fasinjoji sunfara saukowa daga cikin jirgi, can Kamal ya,hango daddyn sa.“Momy ga daddy can yasakko.” da sauri Kamal yaje ya rungume shi.“My son nayi kewar ka sosai.” “nima haka daddy na.” “Watakan ni kun manta dani agun ko.”“Haba uwar gidana ni na isa yanzu muje gida koma menene ayi acan.” dungu mawa sukayi zuwa gun motar su suka hau, Kamal ne me jan motar.

…………………………………………

“Goje meyasa kuka dade haka tun dazu nake jiran ku.” “Wallayi hada kayan aikin muka tsaya yi shiyasa muka dade haka.” wani murmushin mugunta Farida tayi tace.“Ga gidan can muje kawai.” Farida da kawar ta Zara sai goje da yaransa guda uku, gidan su Muzaina suka nufa suna zuwa suka fada cikin gidan bako sallama, Muzaina suka gani tana wanke - wanke sa wanta yana jan ruwa arijiya umman ta tana girki akicin abban ta kuma yana kan dadduma yana lazimi, cikin daga murya Farida ta fara magana.“Watakan ansami mai kudi za a aura masa 'ya ko to ba adace ba ke har kin isa ki hada saurayi da ni to yau zaki gane nafi karfinki, goje mekaje jira kuyi musu dukan da sai sun kasa tashi.” duk wannan abunda takeyi kallonta kawai suke suna murmushi.goje ne suka zazzaro sanduna da takobi sukayo kansu cikin hanzari, dufff hasken gidan yadauke gidan yadawo bakikkirin ko tafun hannun su basa gani duk da cewa ranace misalin karfe uku ne.

BAKAR NADAMAWhere stories live. Discover now