Haba shi sa naga ta shigo tsimi tsimi kaman Wanda Kwai ya fashe mata Ashe ta San mai tayi.
Malam ya naga kayi shiru?
Asabe tunani nake ta yi , na rasa mai nake ciki yaro nan dan kirki ne damuwa na daya tari dukiya shi kar yaga yana da arziki yazo ya wulakanta min Auta
Shine abin da nake ta zulumi.
Malam ai kai naka tunani da sauki damuwa na daya
Auta bata taba zuwa ko gombe ba bare Ashe yau ga Auta a Cameroon, gaskiya malam kace ma yaro nan an mata miji.
Haba Asabe kar ki ce haka ai matan mutum kabari sa
Ko kin manta aure na dauka mutum daga birni zuwa
Kauye? Daga kauye zuwa birni?
Idan matan shi ce Allah ya tabbatar mana idan ba matan shi ba Allah ya kawo mata mafi alheri.
Ai tunda kinga Auta ta turo yaro nan tofa tana so shi
Kuma ni kin sa tsari na bana ma yara na aure dole.
Haka ne malam Allah ya shige mana gaba.
Amin Amin, je ki ce ma Auta Ina mata magana.
Toh Malam.
Hali har kin kwanta ne?
Wallahi umma yanzu na gama nafilfilu na.
Allah maku albarka je ki Abba ku ke so gani ki.
Amin umma na.
Salamu alaikum !
Wa'a laikum mu salam... Auta shigo mana ya kika saya daga waje?
Ai Abba kai ka koya mana salama kafi mu shiga ko ina koma kace sai an ansa ma mutum kafi ya shigo.
Masha Allah wanan haka yake auta na, Allah maku
Albarka. Ku biyu Allah ya azirtani daku , ke da yar'uwa ki Aminatu Shisa koyau she nake alfahari da ku nake kuma gode ma Allah da ya bani ku.
Halimatu sadiya!!!
Na'am Abba.
Tunda na kira asali sunan ki kema kin San ba karamin magana zamu yi ba.
Hakene Abba.
Ina so ki bani dukkan hankali ki a nan.
Ki tattaro nitsuwa ki ki jini da kunne fasaha.
Nasan tsarai da izini ki Alh Audu.B yazo gidan nan.
Abin da nake so sani shine kina so shi kuma zaki iya zama dashi? Kuma kin San tsarai ba dan nan bane.
Duk a haka kinji kin gani kina so shi?
Ban San lokaci da na fara kuka Ina cewa Abba kayi
Hakuri in har nayi ma ba dai dai ba.
Abba ni mai biyayye ga dukkan umurni da zabi da zaku min, Abba ban turo shi da wata dalili ba illa in baku matsayi da hakki da Allah ya baku a kan mu.
Abba ka yafe min in har nayi ma ba dai dai ba.
Ya isa haka Auta, ya isa bar kuka nan haka,
Bani da baki ce komai sai dai na kara gode ma Allah da ya bani ku a matsayi yara gareni ke da yar'uwa ki Amina Allah maku albarka yasa kuma ku samu yara
Wanda zasu maku biyayya kaman yanda kuka mana
Jeki kuma kice ma Audu ya turo magabatar sa.
Murmushi da kuka dadi suka cika fuska Na ina ce nagode Abba Allah Kara girma da daukaka.
🇨🇲 CAMEROON 🇨🇲
An gai da mutane Adamawa, sauka ba sanarwa,
Ina yini Shukurah? Mun same ku lafiya?
Lafiya lau Audu, ya aiki da garin Adamawa? Yafi ka kawo mana mata a garin don na samu naje Adamawa.
Wallahi Shukurah abin da ya kawo ni kenan.
Mata na samu kuma mahaifi ta ya ce nazo da magabata na.
Aaah Masha Allah abu yazo mana da sauki ga nan
Kanne ka Alh na so ya auran kaga sai a hada da naka
Buki bidiri kenan zamu sha.
Kai ya Anty Shukurah Yanzu Ina babba a hada aure na da na yara?
Sai me ? Baku so a yi gaba ki daya mu huta?
To shikenan Anty don Allah ki tsanar dasu mama babba da mama karama.
Aiko yanzu kuwa, jeka Abinci karami palour.
To Alhamdulillah dukkan godiya tabbata ga Allah
Mai kowa mai komai dalili Tara ku a nan gaba ki daya ku shine. Ina so a sayar da lokac buki Wanda kowa zai masa sauki, musanma kai Audu. Inji Alhaji berema.
Ga kanne ka nan kowa ta fadi nata kuma su ce duk suna so a masu a lokaci daya mana su sa wata biyu mai zuwa in Allah ya kai mu.
Kai ya ka gani ya ma ko kuma kana da abin cewa?
Baba duk yanda kuka yi ni mai biyayya ne Allah sa mu dace.
Amin Amin Allah maku albarka, Alhamdulillah tunda haka kukace sai kuma iyaye ku mata ko kuna da abin cewa bismilla mama babba da mama karama Shukurah ko akwai abin da zaku ce?
Alhaji ai duk ko mai ka zantar muyi na'am da shi
Fatan mu Allah ya shige mana gaba.
Amin Amin.
Sai maganan siyayya na kayan lefe wanan kuma zan baku duk abin da kuke bukata.
Zaku iya tafiya inji Alh berema.
A sati shiri a ke ba kama kafa yaro duk abin da ya kamata anyi ba abin da ya raye sai kai kayan lefe garin Adamawa. , don saura yan'uwa Audu su an kawo nasu .
ADAMAWA
Alhamdulillah baki su iso inji Adda umma Asabe
Marhaba da zuwa yan Cameroon lalle jambama pon
Lale marhaba.
Anty Shukurah ce ke amsawa tana ce an gaida mutan Adamawa tana murmushi suka gaisa da saura danji
A nan ne tace da iyaye maza suka zo suna so a sa lokaci buki don gari ba daya ba kuma ga nisa.
Kowa yayi na'am da magana ta. A kama su isowa
Gun Abba.
Ganin Alh berema da wanshi ne da Abba su Halima suka zauna suka sa rana.
Kowa yayi na'am ansa rana 28 ga Wata December.
Taro yayi dadi anci an sha an gaida anyi barkwanci
Musan ma anty Shukurah ta masa sai ta ga umma a fadi ta wai ai ba diyar ta ta fari ba ce.
An rabu a mutumce kowa na kewa juna abin ba 'a iya fadi sai Wanda ya gani.Alhamdulillah
Yauce 28 ga Wata December yau ne dimbu jama'a suka shaida aure Alhaji Abdullahi (Audu) berema da amarya sa Halima sulaima. Sai Rakiya da Salihu, Amina da Ahmad, sai nana Fatima da ibrahim, sai fati da musa, Aisha da auwal, sai Rahmatu da sha'ibu. Sai Rukaiya da Mohammad.
Masha Allah abin da Alhaji berema yake bafi
Mutane da dama suzo har gida yi mashi barka da kuma taya shi murna don duk garin Cameroon ba Wanda ya taba yin abin da yayi auran duk yaran shi mata a tare da babba dan shi daya na miji Wata Abdullahi Wanda a ka fi sani da Audu.
To Alhamdulillah an kai kowa garin da zai zauna
Inda aka Kai Halima gidan ango ta a garin Adamawa, Rakiya kuma garin kaduna, amin na gombe, nana kuma katsina, fati Adamawa, Aisha minna, Rahmatu kuma Abuja, Rukaiya taraba .
Sai ince Asuba ta gari Amare!!!! Bayan wata hudu da aure su halima Adda Amina ta haifi yan biyu ta maza masu kyau gaske inda suka ci sunan mahaifi Kabir wato muktar ana mai lakabi da (hassan inda hussain yaci sunan Abba su Amina wato sulaiman inda suke ce ma husain.
Bayan shekaru masu yawa Alh Audu.B Allah bai bashi haihuwa da wuri ba . Ga dukk yan'uwa shi ba Wanda a ka masu aure tare basu haihu ba. Kowa ya haihu wasu ma har yara su na primary school Masha Allah sai shi.
Ana ciki haka Allah ya ba Halima ciki ta haifi yarta kaman balarabiya Wanda ta ci sunan mama maman babba wato Bilkisu mai gado zinari. Ba abin da Bilkisu ta ba ma Alh Audu B. Don ko kaman su ta bace. Ga haske, ga fari, ga sayo gashi, ga uwa uba kunya da kawaici. Murna a dangi bata misultuwa .
Musan ma Alhaji Audu B. Ya dauke so duniya ya daura ma yarsa Bilkisu, da so da soyayya dangi bai sa Bilkisu ta rasa tarbiya ba. Don hajiya halima na iya kokari ta ta ba yarta tarbiya akan tsari da adini yasa. Har Allah yasa suka auran da ita ga AlhUsman Inuwa dan Adamawa ne shima . Kuma minister of finance .Allahji Usman inuwa ya hadu da hajiya Bilkisu a lokaci da ta gamaNYSC ta da haduwa su da aure su ba bata lokaci aka yi buki a ka kai amarya gidan ta na Abuja a unguwa life camp. Yan biyu Amina suma suyi aure su haiyaiyafa Hassan yaran shi biyu akwai Adnah da zulfa'u matan shi daya wato hajiya mairama yar Senegal ce mairama ba dai ibada ba tana da so mutane duk kudi Alh Hassan bai damu ta don itama Tana da nata kudi shi jini ta ya hadu da haj bilkisu suna abota na aminci Shisa suke business su ba Dubai ba London ba Allah kuma ya bukasa masu business nasu yanzu daga gida ma order suke yi .. Sai Husain yaran shi hudu don ko shi mata biyu gare shi , matan shi ta farko Hajiya shuwa yar Cairo ce wani aiki ya Kai shi Cairo suka hadu ya auro ta suka dawo Nigeria don duk su a abuja suke ai ki. Hajiya shuwa humaira itace yar ta na fari ba abin da humaira ta bar ma mamata da kama da hali. Sai mai biyi humaira benazir ita za a iya cewa da sauki don ita ba mai shiga harka mutane bace . Sai matan shi ta biyu wata hajiya karima yar jihar Ibadan ne yaran ta biyu Ahmadi da kamal tarbiya gidan Husain ba kanta don don rayuwa ne kawai ake na bature, kowa na abin da yaga dama don Alh Husain akwai wadatar arziki . Hajiya Bilkisu bata sha wuya haihuwa ba don Tana shiga ta samu ciki Aryan, tsakani Aryan da Arman wata biyu ne. Tun daga nan haihuwa ta saya mata sai da ta yi shekara 7 sanan ta haifi nasreen.
Wanan shine asali labari mummy Bilkisu da Alhaji Usman inuwa.*************************************************a guje Arman ya bar kitchen in yana cewa aiya mummy pls do quick and finish the food ciki Na na kuka.
Mummy tace da wasa ni Wallahi duk matan da ta aure Arman to fa ta sani ta aure kitchen. Ayi mutum baya iya rike yunwa.
Yauwa nasreen ina sako anty ku shuwa? Naga tun da kika dawo baki ce min komai ba.
Nasreen ya na ga kin bata fuska lafiya?
Wallahi mummy da na San gidan daddy Husain zaki ce bro ya kai ni da ban je ba.
Saboda ke ishashiya ko?
No mummy is not like that Ina shiga na ta sallama ba Wanda ya amsa min har sai da mummy shuwa ta sauko tayi min hug da peck but stil mummy bata ansa min sallama na ba. Am confuse ko bata so sallama ne.
C'mon bana so irin hiran nan ai don bata amsa maki sallama ba that doesn't mean wani abu for her
Ni Ina tsako na inji mummy?
Mummy cewa tayi ai order da kike so yi pls ki bar mata tunda ke naki business in ya bukasa ke da Anty mairama.
Ok abin da tace kenan ?
E sauri ki dauko min waya ai da ta fada min da wuri
Is not a big deal.Haba Aryan wai kasan yanda nake so ka kuma? Amma baka da aiki sai shareni pls ka saurare ni ka ji damuwa na inji humaira na bar gidan mu just for you .
Aryan ko kallo bata isheshi ba ya ce kin manta mai kika ce jiya? I don't know the meaning of elders.
Humaira for God sake shekara nawa ne tsakani mu,
?
I can't date my mate pls ya kama ta ki gane love tsakani mu ba zai faru bane don ko na aure ki baza ki bani respect da ya kama ta ba, gashi tun bayi accepting naki ba kina so na baki girma a haka zamu yi aure?
Haba Aryan mate da mate basu aure? Annabi bai auri bazauwara ba? So what d big deal muyi aure as mate? Sai tasa mai hannu a kai tana dan shafa shi
Auzubillahi !!! Humaira I can't believe what you're doing right now dama irin love da kike fadi muyi kenan ba na aure ba😳 am really surprise by you
Will you get out of my room!!! I hate you
Pls Aryan Wallahi ba laifi na bane so da nake ma ne ya kawo haka pls bazan sake ba.
Is ok naji but pls ki fita min kar mummy ta shigo.
Aryan zan tafi but pls think about us.
Mtssss ko zan yi aure you re not the type.