🏢GIDA BABBA🏢

635 17 0
                                    

Aryan bai samu ya ansa sallama fakhriya ba ta wuce
Ba tare da ta San ta manta da password na ta ba,ga shi tayi nisa don lifter ta hau ya kai ta kasa. Ko kafi
Aryan ya bi ta tayi nisa tsayawa kawai yayi yana kare
Ma password in kallo , sai yaga sunan ta da Full Details na ta. A nan ne ma yaga yau ta iso Dubai don
Ga stamp na allow nata. Sauri Aryan yake yi don dai kawai ya iso fakhriya Amma Ina kafi ya sauko tunda
Ga lifter ya hango fakhriya ta shiga txt ta tafi.
Kafi ya sauko ta wuce, ba shiri ya shiga moto shi yana
Bin hanya da yaga mota ta bi but stil bai gan fakhriya
Ba don ta bace mai. Haka ya ta yawo har ya gaji ya kama hanya gidan su.
Nasreen Na  palour tana kallo taji waya ta Na ringing ta dauka tana ce wa besty don't tell me kun iso? Fakhriya tace mu iso but bazan samu na zo fyn ki ba sai gobe ko jibi.  Nasreen tace Wallahi baki isa ba
Amma if baza ki zo yau ba ni bari na shirya nazo apartment na ku. Tunda  ai na taba zuwa lokaci summer. Fakhriya tace  ok sai na gan ki but now ki fito ga sako na tura maki.
Fakhriya na baki gate na su nasreen tana saye ita da
Security suna rike mata kato box da tazo dashi anyi
Rapping nashi da rapping sheet.
Nasreen na gama waya da fakhriya ta kira mai aiki so taje ta amsa sako, ko da grace ta fito waje sai fakhriya tace mata ta koma ta fada ma nasreen dole sai ita zata fito tayi signing before ta karba sako.
Ko da grace ta fadi ma nasreen sai ta tashi taje waje
Bude kofar da zata yi sai taji ance surprise..................
Nasreen tayi ihu ta yi hugging Na fakhriya Haba besty you really give me surprise ban tanani zaki gane gidan mu Na Dubai ba don na san so daya lokaci muka zo muka gaida dad lokaci da yazo shi daya kuma a ranan muka koma canada.
Gaskiya fakhree you surprise me kuma am so
Happy with the surprise mu shiga ciki.
Mu shiga ciki besty, Mum mummy nasreen ke kira
Mummy ba shiri mummy ta fito daga kitchen rike da
Apple da take yanka ma daddy ta ce nasreen lafiya da irin kiran nan? Mummy fakhriya ce tazo with surprise mummy tace masha Allah come here my daughter fakhriya na kokari tsugunawa ta gaida mummy, mummy tayi sauri dago ta tayi hugging nata tana cewa you're welcome my daughter am so
Here to see you. Fakhriya duk kunya ya kamata
Ta rasa dalili Haka kawai ta tsince kanta da jin kunya mummy nasreen. Bayan su gaisa Mum tace
Mata yasu Ammie ta da dad nata fakhriya tace
Suna lafiya su ce a gaida ku. Mum tace insha Allah before hutu ya Kare ya kama ta mu San juna zan je
Don kai masu ziyara ni da daddy nasreen. Fakhriya
Taji dadi tarba da mummy nasreen tayi mata don haka ta sake sosai suna hira da nasreen da mummy
Can sai ga Arman ya fito zai je kitchen bai ma lura da
Akwai bakuwa a palour ba yana cewa ni gaskiya am
Hungry, Mum ce tace magani mai tashi late duk danzu mutum ke barci sai kace mace what is the time now? Arman yace Mum is almost 5 fa I have nothing to do Shisa nayi ta kallo ball a daki na am thinking of ko sadiya za ta kawo min lunch but naji shiru, mummy tace to sadiya ta fita nasreen kuma frnd nata tazo Shisa ba Wanda yayi notice kana jin yunwa, Arman zai ce wani abu suka ji an bude kofar
Palour Aryan na fadi ita ce! Ita ce!! Ita ce!!!
Mummy ta juya da wuri ta na kallo aryan tace itace waye? Aryan yace itace na gani a wild wadi waterpark, itace ta dauke hankali na mum .
Sai mummy tace Iko Allah, mummy bata kare magana ba fakhriya tayi sauri bari palour har tana bugewa da kofar da gudu da sauri ta bar gidan su
Nasreen , aryan na bin ta tana gudu har ta tare wani
Txt ta bar wuri, Aryan na gani haka ya koma gida yaje ya dau mota gudu yake but stil ta sake bace mai
Ya rasa mai ya ke mai dadi don bai taba ji abin da yake ji ba yau, gaba ki daya in ya rufe ido shi fakhriya yake gani a fuska shi, ji yake yi in har bai fa da mata abin da yake ranshi ba zai iya mutuwa don
Ya tabbata ita yake so! Kuma za neme ta ko ta ina,
Aryan shiru yayi na min 30 yana tuki bai San inda yake zuwa ba can ya tuna mai ya kawo ta gidan su ?
Tabbas akwai Wanda ya San ya a gidan su, ba shiri
Aryan ya taka burki ya juya kan mota shi hanya zuwa
Gidan su yana tuki ne a high speed sauri yake yi kawai ya isa gida tafiya yake ido shi a rufe bai an kare ba yaji wata mota ta buge shi Innalillahi!!!!
Haj Bilkisu ta juya tana tambaya nasreen dama aryan su San juna da fakhriya ne ? Nasreen a rikice
Tace no Mum I don't think so. Mum zata yi magana
Sai ga daddy su ya sauko yana Bilkisu!! Bilkisu!!!
Aryan yayi hatsari what!!! Mum ta fada innalillahi wa inna ilaihim raji'un yanzu nan yaro nan ya fita kam daddy ya tsayar da ita yace zo mu tafi an kai shi
Asibiti yanzu ba time na magana ba, Arman yace
Dad zan je, nasreen ma tace nima tana kuka , duk tare suka zo city hospital Dubai inda suka je suka taran da hali da Aryan yake ciki gaba ki daya ba'a cewa komai, mummy kuka Arman nasreen kowa kuka da kyar daddy ke basu hakuri zai warke insha
Ana ciki haka doctor yazo yace yana so gani daddy.
Daddy a office na dr nasif yana mai bayani dole za'a shiga da Aryan a mai surgery don ya samu deep cut a heart nashi.
Daddy yace ma doctor why surgery why?? Aryan dan
Zu nan yaron nan is fine Amma wai yanzu rai a hannu
Allah, ohh Allah ga Aryan a hannu ka, dr nasif ya kama shoulder daddy yana cewa it shall be well insha Allah fatan mu Allah yasa muyi a sa'a kaje kayi formalistic da signing Na surgery best of luck doctor
Ya fada, daddy jikin shi a sanye ya bar office Na doctor  yazo daki da Aryan yake kwance kaman kawa
An sa mai oxygen, bai fadi masu Haj Bilkisu komai ba hannu aryan ya rike yayi mai addu'a ya juya yana
Fadi masu mummy abin da doctor ya fada mai
Mummy tace surgery Alhaji!!! Innalillahi ohh Allah
Gamu gare ka tana ciki magana nurses suka zo suna cewa sir is time for the surgery......,
Ba Wanda ya iya ce masu komai suka tura gado aryan zuwa surgery room suna tafiya su daddy na bin su a baya har inda suka ga an rubuta out of bond
Suka saya kowa na ma Aryan fatan alheri.
*************************************************
Fakhriya na isa gida ta taren da Ammie a palour tace
Ammie yau nayi abin kunya. Ammie ta kama baki
Tana gani fakhriya tace mai kika yi?
Fakhriya ta kwashe komai ta fadi ma Ammie har inda Aryan yazo ya same ta gidan su Nasreen.
Ammie tace Amma a bayani ki kaman Aryan brother
Nasreen ko?
Fakhriya tace that's what am thinking but Ammie
Mai yasa zai ce na hauke hankali shi just yau muka
Hadu fa Ammie. Ammie tace go and fresh up zamu
Yi magana but ban ji dadi da kika tafi baku yi sallama da Mum na nasreen da nasreen ba.
Fakhriya tace Ammie I told you kunya ya bani
Wallahi Ammie baki ji yanda naji ba kaman kasa ya
Tsage na shiga don kunya Ammie ban San mai yake nufi da words nashi ba fakhriya ta fada a yayi ta take shiga daki ta , gado ta fadi ta kwanta tayi shiru kaman mai barci tafi 1hour a haka .Ammie da ta  leko taga fakhriya a kwance ta samma barci tayi ta fita ta ja mata kofa.
Fakhriya na kwance ita bata yi barci ba ita ba ta bude
Ido ta ba, ba abin da take tuna wa kaman inda aryan
Yake cewa ita ce!!! To mai yake nufi? Yau na gan shi
Ban sanshi ba koma tun da nake da nasreen ban taba
Cewa bari naga hoto brothers naki ba. Har ma kwara
Mum nata da dad nata sune a kan screen na waya ta
Kuma tana yawan hiran su brothers nata don duk yan gidan su ba sunan Wanda ban sani Ba, one mistake da nayi shine na rashin ce ma nasreen ta nuna min pictures Na family su. My dream man why
Ina ta gani fuska Wanda muka hadu a wild wadi park he has the quality's that I want from my dream
Man fakhriya ki raba kanki da wanan tunani haka naji zuciya na na fadi min bari na tashi na nemi nasreen nasan tana nan tana fushi dawo wa na ban
Mata sallama ba aiya my besty nasreen I will make up with her let me call her, fakhriya tama nasreen 4miss call Amma duk ba dauka ba I will call her back bari nayi wanka fakhriya ta shige toilet tana murmushi tana jin zuciya ta na bugawa daure wa kawai take yi .
Alhaji usman inuwa yana gaban kofar theatre  yana kallo signal light na kofar daki surgery har yaga wuta ta dawo green bai Kara step daya ba doctor ya fito
Yana cire hand groves yana murmushi har ya iso
Alh usman doctor ya mika ma Alh usman hannu ya ce mai congratulations the surgery was successful
Alhamdulillah inji Alh usman yace Allah nagode ma
Ba wayo mu ba ba dabara mu ba🙏 doctor yace mai
You can follow me to my office.
A office Na doctor Alh usman na jin jawabi doctor inda doctor yace the surgery is done but their is one
Problem!
Alh usman a zaune yake Amma sai da ya tashi tsaye
Yana cewa what is that doctor pls kar ka fada min
Aryan ya samu wani damuwa pls?
Doctor yayi gyaran murya yace no come down ba wani damuwa bane but if an kiyaye dokoki da za mu sa, na farko lokaci da yayi hatsari da ya tashi buge wa bai guge a ko ina ba sai a kan chest nashi Wanda
Tsanadi faruwa haka ya taba mai heart nashi Shisa
A kai mai surgery a heart don heart in ya dan tsaye kadan da taimako Allah ya bamu iko yi surgery successfully yanzu ba tsayewa ya hade. But condition in shine dole a guji baci rai shi, if yana da mata dole
Ta bishi a hankali, in bashi da shi before ya fara dating a fadi ma girlfriend nayi saboda hali rayuwa
Dole yanzu ko shiga treating nashi with love don ta
Haka nema zuciya zai hade sosai har ya zama normal
Sanan duk abin da yake so ku bashi in har bazai cutar dashi ba, but if aka samu akasi  haka gaskiya
Yaro ku zai wahala, kuka bata mai rai abin na farko da zai bata mana aiki shine if ya fara amai jini wanan shine signs Na surgery ya bace abin da bamu so kenan doctor yace in Alh na da abin cewa ya fadi.
Alh usman tace duk su ji kuma da yarda Allah zasu kiyaye.
Doctor yace fine muje nasa nurse su kai shi daki
Shi don he need to rest.
A nan ne Alh usman ya nema a ba aryan special room. Haka aka yi an Kai Aryan daki na musan ma
In kana ciki daki baza ka san ma a asibiti kake ba.
Alh usman ya je daki da Aryan ya fara zama ya je yace masu Haj Bilkisu an fito dashi dama sallah isha'i tayi ta idar tana ta addu'a nema ma Aryan sauki, a hankali ta tashi tace daddy yara ba nan zasu
Dawo dashi bane daddy yace mata ai na ce a chanza mai daki mummy ta ya dai akwai na sara a aiki?
Daddy ya gama hannu ta yace Alhamdulillah sai dai
Muje muga aryan zan maku bayani ya kama nasreen
Da tayi kuka har ido ta yayi ja, Arman ya rike Mum
Suka bar daki suka je new daki da Aryan yake.
Tunda da aka yi surgery Aryan bai bude ido ba sai
Gobe ya dan mosa kafa shi da wuri Haj Bilkisu ta je
Kusa dashi tana shafa mai kai tana cewa sorry my
Son insha Allah zaka ji sauki, Aryan ya dan samu
Ya bude ido yace Mum Ina take? Mummy juya wa
Tayi suka hada ido da daddy sai hawaye mummy tace aryan ya kake ji jiki ka in? Aryan yasa ke cewa
Ina ta ke? Wanan karo daddy ne ya samo kasa da shi
Ya kama hannu shi yace aryan wa kake nufi? Ba mu
San ta ba , ya kake ji karfi ji ki k*** kafi daddy kara
Sa magana aryan ya fara cewa Shi kenan na rasa ta
For the 3rd time Mum mutuwa zanyi mum ki nemo
Min ita son ta nake yi itace Wanda na dade Ina nema
Gashi ta sake gudu min daddy aina za samo t
Ah aaah ah tayi aryan ya fara ba shi daddy y fara cewa aryan kar kamin haka don Allah kasa ma ranka
Zan nemo ma ita pls, Aryan sai tari ya fara ana ciki
Haka doctor ya shigo check up what!!! Doctor ya fada but I told you Sir kar ku bar patient nan ya fara
Abinda yake yi yanzu do u wan to lost your son?
Mummy tace no daddy mai doctor yace akan aryan
Ohh ni Bilkisu yau baga ta kai Na doctor daddy ko min bayani ? Arman kuku nasreen kuka daddy ne
Ke claiming nasu a nan ne sama sama doctor ya ma Haj Bilkisu bayani hali da Aryan yake ciki yana gama fadi ya je office nashi ba shiri ya shigo da nurses sai dube dube yake ma Aryan can kuma ya fara ma Aryan allura a heart ya sake sa mai wani a drip ya yi mai wani a vein kafi kace mai aryan ya daina tari yayi barci.
A nan ne doctor yayi gyaran murya sosai yace yana
So duka su su bashi hankali su a nan har dasu nasreen doctor yace Aryan is not the Aryan da kuka sani da Aryan yanzu ya dawo mai rauni a zuciya shi
In kuka kiyaye sai ya dawo normal Aryan kaman
Da but if kuka ci gaba da yanda kuka mai now
Am sorry to say zaku iya rasa shi doctor ya juya yaga
Alh usman yace sir danzu muka gama magana mai
Sa haka ya faru? Sai a nan mummy tace ba laifi shi bane don shima Alh bai San mai ya faru ba sai
Hatsari ya sani a nan mummy ta kwashe komai ta bada masu har da mood na aryan har tasa shi ya fita
Don yaji dan dadi a ranshi.
Doctor ya saukar da numfashi tace gaskiya you have
To fine this girl don yaro ku na so ta kuma ba da wasa ba. Ya fita a daki, mummy ta juya ta kalli nasreen tace nasreen ki taimake dan'uwa ki ki nemo
Mai Fakhriya kar mu rasa aryan kin ji da kunne ki
Abinda doctor yace, nasreen tazo ta rugume mummy
Suna kuka Arman ya zo shima ya rugume su duk ka
Su uku kuka suke tayi.
Arman yace mummy kije gida ki yi wanka sai mu
Dauko sadiya kafi kin huta. Mummy tace Arman
Ba zan iya zuwa gida ba don ko naje hankali na
Ba zai kwanta ba in har ba naga aryan ya bude ido
Yana min magana ba.
Daddy yace nasreen ta tashi taje Arman ya kai ta suzo da fakhriya don kar aryan ya kuma tashi.
Jiki a muce nasreen ta shi ta ce ma daddy da mummy sai su dawo mummy ta kalle ta yara ta duk
Abin tausayi don basu taba shiga irin hali nan ba
Sai jiya.
A mota ma ba Wanda yace ma dan'uwa shi kala sai
Arman da yake ce ma nasreen aina ne inda fakhriya ta ke nasreen ta kalli Arman tace dole sai mu je gida
Don na bar waya na a gida Arman yace to .
Suna isa gida sadiya ta tare su da kuka tace jiya banyi ban ci ba duk hankali na a tashe da Maigadi
Yace min aryan yayi hatsari duk baku nan kuna asibiti sai da daddy ya kirani yace kar na damu na
Kwanta baza ku samu dawowa ba don Allah ya jiki shi nasreen ta ce hmm sai kuka sadiya ta juya wurin
Arman tace kai min magana ya jiki shi? Arman yace
Tauko mayafi kizo muje.
Nasreen ta dauko waya ta taga miss cal kacha kacha
Ta shiga kiran fakhriya a lokaci fakhriya na sa rani
Hannu ta ko da taga kiran sai tace su nasreen an
Sauko daga fushi, tayi picking tasa a kunne ta ta ce
Assalamu'alaikum nasreen shine sai yanzu zaki ki
Rani don jiya na kira in baki hakuri kika ki dauka
Na dawo ba tare da na maku sallama ba. Fakhriya tace nasreen lafiya Ina ta magana kin mi shiru
Kaman ba ke ba, nasreen tace fakhriya kimin kwatance inda kuka sauka gani nan zuwa dadi kaman fakhriya zata yi ihu a take ta mata kwanta
Nasreen tace ta gani wurin.
Nasreen ta juya ta kalli Arman tace ya Arman deira
Suke kusa da city center Arman yace ok
Tafiya 43 min suka yi suka isa apartment na su fakhriya inda suka same ta a palour da rani a hannu
Ta tayi murna gani nasreen sai dai ta lura kaman
Nasreen na ciki damuwa, fakhriya tace besty lafiya?
Haba kaman nasreen na jira ta fashe da kuka ta rugume fakhriya ta bata labari duk abin da ya faru
Ba shiri fakhriya ita ma ta fara kuka Arman ne yayi
Gyara murya yace pls we don't have much time
Don aryan zai iya tashi kuma bamu isa ba.
Ammie da take jiki kofar kitchen taji komai don
Ita tun da fakhriya ta bata labari ta San Sarai Aryan
So fakhriya yake yi itace dai bata gane ba.
Ammie ta kuyi maza ku je ku duba shi nima insha
Allah daddy fakhriya na dawowa zamu zo,
Nasreen na kokafi gaishe da Ammie tace yanzu ba
Lokaci gaisawa bane su je ta yafe,  basu bar gidan su fakhriya ba Haj Bilkisu ta kira su tace aryan ya tashi jiki shi yafi na da worst in basu iso da wuri ba zasu iya rasa shi inji doctor .a gurguje sauri Sauri Arman ke tuki suna iso wa asibiti
Ko parking Arman bai yi ba Fakhriya ta bude mota
Tana gudu tana ce nasreen wani room ne? Nasreen
Tace Vip room 2 2nd floor . Gudu fakhriya tace ta hau lifter ji take lifter baya sauri kaman ta fi re haka
Kawai take ji in ta rasa aryan kaman ta yi asara a rayuwa ta. Lifter na saya wa ta ga an sa vip room 2
Sai da zuciya ta ta buga Wanda bata San dalili ba
Kai tsaye kofa ta bude da sallamata da murya ta mai dadi sauraro.
Aryan na gani ta ya bude ido shi ya kuma rufe wa ya bude, fakhriya tace ba mafarki kake yi ba da gaske nice tsaye a gaban ka, abu mafi tasiri Dagula lissafi
Shine jayayya da zuciya! Matukar zuciya ta na so abu bai kama ta kayi kokari  hana ta nema  cima wanan a bu.
Aryan yace ta yaya?
Fakhriya tace Ina tsane da kai a ciki kankani lokaci na ci karo da soyayya ka, ta hanya tafi ka , kallo ka ,motsi ka da duk abin da ta dangance ka.
Aryan yace ta yaya?
Fakhriya tace ta hanyar farko da ka fara gani na a
Wild wadi park a ciki Dubai mall bibiya ta da kayi har na shiga muta na bar ka a ciki lifter , muka sake haduwa a gidan ku
Aryan yace haka ne.
Fakhriya tace kai rago ne ka bani mamaki ka bani kunya da na ganka a kwance a gado asibiti a kan  so na! Kuma kai ma kasan kana so na shi ne
kake so ka cuce kan ka , kuma ka cuce ni na samu mai min irin wanan soyayya aryan na baka soyayya
Na Duniya da lahira.
Ba shiri aryan ya mike tsaye yace kin bani so?
Fakhriya ta ce na baka so aryan ta fita a daki da gudu ta nemi wuri ta zauna a waje asibiti tana ji so aryan
Na shigen ta ta ko ina....,,
Mummy tace Alhamdulillah!!!
Doctor nasif was very surprise da ya duba heart beats da duk wasu damuwa na aryan yaga komai ya dawo normal ya juya ga daddy yace this girl was a miracle the boy was very ok ba damuwa for now
Ina fata haka zaku ci gaba da bashi kulawa.
Sati Aryan 2 a asibiti soyayya shi da fakhriya ba'a cewa komai don a gaban kowa aryan yana nuna ma
Fakhriya sosai in ba barci ba ba abin da ke raba su
Hankali Haj Bilkisu ya kwanta taga yaro ta bai da damuwa yanzu kuma ta lura fakhriya bata sakewa sosai Haj Bilkisu ta dawo gida ta bar masu asibiti.  Aryan ya samu abin da yake so don shi ba kunya su
Sadiya da nasreen da Arman yake yi ba a gaban su yake nuna ma fakhriya soyayya itama fakhriya tun tana ji kunya su ta sake sosai suke soyayya su abin
Sha'awa Arman ne ya ce anty fakhriya don Allah nima ki min addu'a na samu girlfriend kama ke.
Aryan ne yayi dariya yace sai ka kwanta a asibiti  if
Stil kana so , fakhriya ta yi sauri cewa laaa an Gaya ma kowa ragone a kan soyyaya, Aryan yace in dai a kan ki ne na yarda.
Kowa dariya suka basu a tare suka ce Allah bar love.
Aryan yace amin.
Yau ne ranan da doctor ya sallame Aryan don yaga
Jiki shi is well ok ba wani damuwa a tare dashi
Sanan duk important magani da suke so ya sha ya sha su, doctor ya ce pls aryan you know your condition pls help your self nobody will help you
Better than yourself kar ka sa kan ka a damuwa be
Happy almost daga karshe doctor yace masu all the
Best ya Mika ma dad hannu ya fita.
Ammie ne ta iso da daddy fakhriya tace ya dai yaga
Kaman an sallame ku? Haj Bilkisu tace Wallahi bismillah ku kara so Alh usman ya Mika ma dad na
Fakhriya hunnu suka gaisa daga nan suka fita waje suna dan tautaunawa game da ciwo Aryan.
Dad Na Aryan ne yace ma dad Na fakhriya wato Alh
mahmud lamari yaran nan ya tsora ta ni Mu San ma
Aryan bai taba soyayya ba bai ma da Wanda yake so
Har nake mai tsiya nace ya fito da mata gaskiya na
Tsorata da lamari nan.
Alh mahmud yace haka Allah yake tsara abin shi ta yanda yaso, Ni ban kawowa fakhriya aure nan kusa ba koma yarinya nan ko da wasa bata taba nuna min
Bata ra'ayi na ba don kullu buri ta tayi min biyayya ita daya Allah ya bani Shi sa na sa mata buri yin karatu mai zurfi Amma tun da naga ciwo Aryan na
Janye kudiri na alfarma nake nema da Aryan kar yace ayi aure nan ba tare da fakhriya ta hada degreen
Nata ba tunda naga shekara biyu ya rage itama lokaci she will be 18 kaga sai a fara shiri buki.
Alh usman yayi hamdala da Allah ya hada shi da Alh mahmud mutumi da ya San daraja dan Adam, a duniya nan wa zai ma irin abin da yayi mai a yau ba
Shiri Alh usman yayi ma Alh mahmud godiya da har
Alh mahmud ya ji kunya yace ya isa haka Allah ya
Tabbatar mana da alheri shi a tare suka ce amin.
Daga asibiti suka wuce dukkan su gidan Alh usman
A babba palour suka zauna inda cooks suka shiga fito da su drinks , snacks da abinci don dama su San
Da zuwa su.
Anci ansha kowa kagan shi kasan a ciki fari ciki yake
Anan ne Alh usman yace yana so zai yi magana.
Kowa ya nutsu  ya bashi duk kan hankali su.
Palour yayi shiru ba kaji motsi komai sai tv da Ac da ke palour. Alh usman yayi gyara murya ya fara fadi
Alhamdulillah ala kulli hai, duk godiya ta tabba ga
Allah maukaki sarki mai kowa mai Komi . A yau ni
Da family na bamu da baki da zamu gode ma Alh mahmud da family shi sai dai muce Allah tsaka da karamci da ka nuna mana ni Alhaji usman inuwa Ina nema ma yaro Na Aryan usman inuwa aure yarka fakhriya .
Alhaji mahmud yace na baka yata fakhriya ,ma dan
Ka Aryan Amma sai ta hada degree ta nan da shekara biyu masu zuwa in ta gama makaranta sai a yi aure in mijin ta na da Iko ko buri bari ta ta ci gaba wanan kuma ya rage nasu fatan mu Allah ya shige mana gaba yasa maku Albarka .kowa yace amin.
Masha Allah abin da kowa yake fadi murna wurin
Aryan da fakhriya ba a cewa komai  Arman ne yace
Nima Allah kawo min nawa. Kowa sai dariya yace yi
Don yan da yayi magana nasreen ne ta ja hannu fakhriya muka wuce daki ta suna shiga ta rufe kofa
Tace besty yanzu kam kin dawo anty na
Fakhriya tace you better know don yanzu anty zaki na ce min,  sai kuma tayi dariya tace Haba besty ba
Wani anty you're stil my best friend nasreen tayi dariya tace stil anty ce don matan babba yaya ai
Sai da anty.
Nasreen tayi shiru na dan mintina ta ce am very greatful fakhriya ban taba tunani zaki yi accepting na
Brother na ba Duk da ba dream ma naki ba...ne
Kafi nasreen ta gama fadi magana ta fakhriya ta rufe
Mata baki tace Aryan is my dream man don duk abin
Da nake so a gun dan na miji aryan nada shi har ya
Wuce ta ce ke ba zaki gani ba because he is your bother don tun a wild wadi waterpack da muka hadu
Da Aryan na gane ya kamu da so na nima I feel the same . Aryan da tun da fakhriya ta so ma magana yana manne a jiki kofar daki nasreen wanda ba su San yana wurin ba yana jin duk hiran su.
Fakhriya ta ci gaba da cewa kawai na gargade zuciya ta ne da kar ta fada ma abin da ba zai yi ba don buri
Dad Na shine yaga nayi ilimi sosai kafi ya auran da ni don shi a gani shi ni daya ya mallaka , lokaci da
Aryan yake bi na ban so na guje mai ba sai don bana
So ya wahala da kanshi a kai na Shisa nace ma mai
Cab ya nemi wani wuri ya tsaya don naga ta inda Aryan zai bi, Ina wani road side har Aryan ya Wuce mu San nan muka tafi hanya zuwa gidan ku , ganin
Aryan a gidan ku ba karami kunya naji ba don ni
A tunani na ya biyo ni ne Shisa nayi sauri bari
Gidan ku don kar yace yana so na a gaban ko,
Da na ji yana asibiti hankali na ya tashi sai nayi
Tunani mai ne zan ta boye mai so da nake mai if har
Yana so na ina so shi I see no reason ta zan ta boye mai Shisa na biku asibiti don ceto dream man na.
Suna ciki hiran su suka ji aryan ya tura kofar yace
I didn't have the mouth to say thank you my love
You're really my type I love you unconditional my love for you is pure and everlasting love pls promise to stay with me this enternity.Fakhriya ta rufe ido ta tace ma Aryan I promise you my heart nasreen baki ta bude tana gani masoya ebiyu da suke ta fadi ma juna sirri zuciya su abin sha'awa.
dAryan ya fito da password Na fakhriya yace ga abin uki fakhriya tayi dariya tace dama yana wurin ka?
B
Aryan yace tun ranan ya fadi na anje shi a wuri na
Da Ganga na ki baki a asibiti don shi nake kallo in
Kin koma gida, murmushi tayi tace thank you love.
Yace you wlcm. Sadiya ne ta shigo tace anty amarya
Ammie wai kizo ku wuce , Aryan yace tell her zan
Dawo da ita fakhriya tayi sauri cewa no love yaushe
Ka tashi daga gado asibiti pls not today in ka warke
You can drive but now is not ok. Aryan yace is ok tunda haka kika ce. Har mota suka rakasu Ammie aryan na daga ma fakhriya hannu yayi mata kiss a iska ya hura mata, fakhriya ta rufe ido ta ita ma tayi
Mai a iska duk Ammie na kallo ta bata sani ba sai
Da ta yi mata dan Mari wasa a bayan ta sai tayi sauri
Bude ido tana sunkuyar da Kai lokaci har su bace ma
Gidan su Aryan.
*************************************************
                                   PARIS
haj shuwa tana zaune a Paris ita da benezir a wani restaurant suna ci a bin ci, benezir hankali ta sam ba
Ya ga haj shuwa da take ta waya business nata benezir hankali na kan wani yaro da ka kan shi kaga
Dan duniya don duk hakuri shi golds ne a ka jera ga tattoo ta ko ina a jiki shi har da fuska shi benezir sai
Yi tayi yi suyi eye contact da saurayi matashi nan
An ma bai ma gan ta ba ana ciki haka sai taga ya tashi ya bar inda suke yana hanya zuwa male room don gyara jiki shi da drink ya dan zube mai.
Ba shiri benezir ta shi ta bishi ko da tazo ita female room ta shiga tayi timing fito wa shi suka fito tare
Ko da mike ya ga benezir ya rikice don benezir ba
Karami kyau ta ke dashi ba don Tana da hips da diri
Tafi humaira abin da humaira zata nuna mata sai
Haske, mike na kallo ta ya ce hello angel!!!  Haba
Benezir na ji haka ta kashe murya ta ce hi!!
Mike yace pls if baza ta damu ba tayi mai kyau ko
Za ta iya zama girlfriend nashi, a take benezir tace
Sure why not.
Ko da Hajiya shuwa ta gama waya ta taga ba benezir
Sai ta kira ta tace ita ta wuce in ta gama ta same a gida .
Benezir tare da mike suna hira yana tambaya ta abin
Da tafi so da Wanda bata so tana amsa mai a shagwabe . Har yake tambaya ta tana sha giya ko taba? Benezir tace bata sha duka , mike ya yi sauri cewa what! Wai gaskiya ta bashi kunya a duniya a duniya ba abin da benezir ta tsana kaman a ce  kaman ita ta kasa yin abu sai tayi murmushi tace
Ma mike wasa take mai tana  sha kuma ita karshe ne a duk kayan maye  sai mike yace ok why not su kwada don shi guru ne a harka don shi har allura
Yana ma kan shi. Stil benezir bata tsorata ba don kar taji kunya ya Raina ta sai tace su kwada but ba a nan
Ba ya nema masu silent wuri. Mike yace ok fine
Bari yayi masu booking na hotel sai su je a take yayi
Call ya kira daya daga ciki hotels na babba shi da ke cikin paris yace su tafi. A hanya tafiya su ne yabi
Ta shops da ake sayar da Kayan maye ya sayo masu
Duk Wanda zasu buka don ya tambaye benezir mai
Tayi so tace wanda yafi nashi karfi sai mike yace
Wow queen you're really giving me surprise I love you haka nake so budurwa na ta kasance wayyo dadi
Wurin benezir ita a dole mai aji.
Benezir suna isa daki da mike ya kama masu ya fara
Bude masu duk abin da ya sayo na maye suka sha suka bugu har basu San inda suke ba musanma ma
Benezir ita da ba harka ta ba mike na kallo benezir a buge ya dauko wani kayan maye ya nuna ma benezir ya ce kinga wanan ya daga kwalba yace ba'a hada shi da wanan don duk iya buguwa ka baza ka iya ba ka hada su wuri daya kuma ka sha a tare don tsinkajijiya mutum yake ka mutu.
Benezir tayi dariya tace ni zaka tsorata I will surprise you now, mike a buge yace shi ba ruwa shi don ta fara bashi tsoro, ko a jiki benezir ta karba kwalba a
Hannu mike ta hada su wuri taya tace zata rike
Mai bai ce komai ba yace tunda su gama bari ya kai
Ta gida benezir tace no zata zauna da shi mike ya shiga toilet ya fito ya taran da benezir a gado ta hada
Masu giya tace ga nashi ga nata suyi composition a ga wa zai fi buguwa Duk da dama a buge suke mike
Bai San benezir ta hada masu da Wanda ya Hana ta
Ba danzu tama fi sa ma kanta ita a tunani ta mike
Karya yake mata a tare suka shanye cup daya mike ya cire ma benezir kaya yaga baya sauri ya shiga yaga kayan jiki ta haka itama don dama benezir ba yau ta
Saba harka da maza ba ido ta a bude shaye shaye ne
Dama ba aiki ta ba gashi yau tayi a haka a buge suka
Biya ma kansu sha'awa kaman dabbobi don har ta baya mike ya nemi benezir. Suna ciki aikata haram
Benezir taji kanta na mata mugu ciwo bata dawo ba
A tunani ta giyace tayi mata yawa haka suka ci gaba
Har kusan rabi hour mike yaji benezir bata motsi
Bai saya ba yaci gaba da yin jima'i da ita bai ma San ba rai a tare da ita ba.
Shima yana haka har rai tayi hali shi.**********************************************
Innalillahi wa Ina ilaihim raji'un  Ina amfani irin wa
Nan rayuwa Allah ya baka Amanar yara mai zaka je ka fadi mai ya ka tarbiyan tar da Amana da Allah ya baka iyaye Ina so jawo hankali mu a kan rayuwa yara mu Amana ne Allah ya bamu su kuma ranan gobe sai
Allah ya tambaye mu ya muka yi da Amanan da ya bamu.
Haj shuwa na zuwa gida ta ciki gaba da  rayuwa ta ko a jiki ta bata damu da rayuwa miji ta ba bata damu da na yara ta ba sai business da tasa a gaba ita damuwa ta ta tara dukiya taji dadi duniya.
Akwai rayuwa da Haj shuwa take yi Wanda ba kowa ya sani ba sai Allah da kuma aboki yin ta Haj shuwa ta dade tana zalita miji ta Alh Husain  Wanda shima
Bai ma San tana harka ba, Amma yasan tabbas har da maza a ciki abokane kasuwa ci Haj shuwa Amma
Alh Husain bai taba zargi ta da zata ci Amana shi ba
Don shi yasan irin so da take mai tunda ta bar kasan
Haihuwa ta ta biyo shi Nigeria kuma ta Haifa mashi yara Shisa bai taba tunani komai daga wurin ta ba.
Kwance take jiki wata kujera mai ado kaman
Fari glass tana Shafa wuya wani matashi saurayi
Wanda bai wuce shekara 20 a duniya ba don ko daga
Irin shigar sa zaka gane haka yana ce mata baby  baki gudu benezir tazo ta same mu a haka inji yasir
Yaro da Hajiya shuwa take rayuwa dashi kaman mijin da don duk inda zata je dashi take fita don
Bata ji zata iya rabuwa da yasir. Haj shuwa tayi wani
Irin dariya tace mtsss aiya yasir kana gani benezir za
Ta dawo kusa? Ai tun da nake waya na lura da ita sai
Kallo wani saurayi take yi Wanda ya dauke mata Hankali Ina gani ya tashi tabi shi da Gangan na kira ta a waya nace na wuce don kawai mu ji dadi mu yanda ya kama ta, yasir yayi dariya ya dada shige jiki
Haj shuwa yace mata Shisa nake so ki mummy Haj shuwa tace ai baby na fi so ka Shisa don inda zanje
Da kai nake zuwa don bana so kana kula yan mata
Yasir yace Ina da sugar mummy na mai zanyi da wasu mata daga ke sai ke a haka Haj shuwa da yasir suka ta aika ta haramu ko a jiki su da dare ne yayi
Yasir ya sake tambaya ko benezir zata dawo shine
Haj shuwa tace ko ta dawo ai tana da daki ta don haka kar yasir a nan yasir ya kwana suna abu daya
Don yasir baya gaji da bukatar Haj shuwa don jarabebiya ce .
A Dubai Alhaji Husain na kallo new na safe yaga
Inda ake new yaro senate president na paris ya mutu
Da Wata yariya yar Nigeria mai suna benezir Husain (sulaiman) sai ga hoto benezir da mike a tsirara haihuwa uwa su sai wani fari abu da aka rufe masu
Gaban su dashi ita benezir aka rufe mata nono ta
Alh Husain bai San lokaci da yayi salati ya tashi
Tsaye yana innalillahi wa inna ilaihim raji'un a yau
Ya fara nadama aure Haj shuwa don bai ga amfani ta
A rayuwa yara shi ba ya dauki waya ya kira ta da
Number na paris yafi a kirga Amma bata dauka wa
Har ya gaji don kanshi bai San a lokaci Haj shuwa na more rayuwa ta ita da rabin ranta yasir.
Alh Husain ya shirya ya wuce paris a ranan.
Alh usman na ganin news yaga su benezir ba abin da
Yake cewa sai innalillahi wa inna ilaihim raji'un
Haj Bilkisu Na innalillahi tana sauko wa garo suka ce
Da Alh usman yana tambaya ta kema kin gani tace
Naga Alh. Yau wace irin rayuwa ne wanan Wanda
Husain ya zaba ma yaran shi ko kafi na zo Dubai sai
Da muka yi da Haj shuwa a kan zata bar humaira a
Gida su su taho Paris da benezir Ashe a jali ke kiran
Ta ya salam Haj Bilkisu ta ce tasa kuka a hankali
Alh usman ke rarrashi ta har tayi shiru ta fara nema
Number Husain shima bata same shi ba chan ta ce
Bari ta nema Hassan kira daya ya dauka yace Bilkisu ke ma kin gani ko ? Yace Husain baya ji magana
Tun yaushe muke fada dashi a kan yanda yake ma yara shi tarbiya Amma sai yayi fushi yace kowa baya
So shuwa Shisa aka sa ma yaran ta ido to gashi
Wanan abin kunya da mai yayi kama Addu'a na daya
Allah sa mama bata gani ba Haj Bilkisu tayi sauri cewa ai tana gani Shi kenan don dama tun aure shi da shuwa tace mai ba ita ba shi Alh Husain yace ya
Kira ni wai ya isa paris yanzu haka yana hanya zuwa
Asibiti da a ka anje gawar benezir in wai na samu
Na taho a ta sallah a chan in ba sai ta dawo Nigeria  ba Haj Bilkisu tace haka ma yayi da muna sai muzo
Alh Hassan yace kuyi zaman ku Ina zasu zo Dubai in
Ai kawai kuyi zaman ku don nima ba zuwa zanyi ba
Shi da ya Debo ma kanshi ya karata Haj Bilkisu ta bashi hakuri daga karshe suka yi sallama yace zai taso gobe.
Alhaji Husain na isa paris ma sauki su Haj shuwa ya wuce don dama shine mai musu booking kafi ma su
Iso haka ya Saba a ko wani gari yake dole shi yayi
Don shuwa bata wasa da kudi ta duk business bata saya ma kanta zani bere Alh Husain yasa ma ranshi
Zata taimaka mai da komai kudi ta a account nata yake ba Wanda yasan pin nata sai yasir don ta yarda da shi sosai. Kai saye masauki su ya isa yana zuwa ya
Nuna card nashi ya wuce don karami apartment
Yayi masu booking a cewar shi su biyu ne zasu zauna
Kai saye daki ya nufa yana isa yaji kaman ana kuka
Shi a tunani shi ko shuwa ta samu labari sai ya sa kai
Da niyar bata hakuri haka Allah yaso dasu
Amma mai zai gani???????????????????????????????

GIDA BABBA by mrs MZWhere stories live. Discover now