Shakuwa mai karfi ta kullu tsakani Arman da Zulfat Ko yaushe sai Arman yaje gun zulfat su sha hira ya dawo gida. Best shine sunan Arman da zulfat suke kira juna su dashi , best ya naga kayi shiru inji zulfat, Arman ya dan yi gyara murya ya ce best Wallahi wani abu ya ke damuna wanda na rasa yanda zanyi na fadi maki don Ina tunani yanda zaki dauki maganan.
Zulfat ta bata fuska Haba best yanzu Ashe akwai abin da zaka iya boye min da duk shakuwar mu
Gaskiya ni na yi fushi da kai .
Arman da sauri ya juyo yace no har my best Wallahi
Ba haka bane kawai na tuna kin taba cewa you don't believe in love.
Zulfat tace yes I don't believe in love don't yanda love ya wahalar min da kawa sai naji gaba ki daya
Duk maza hali su kenan, Arman yayi sauri cewa no
Best Wallahi da zaki San yanda nake so ki a ciki rai na da sai kince kowa da nashi irin love ne pls Arman yace tare da durkusawa kasa yana ce ma zulfat Wallahi Ina so ki kuma ni da aure nake so ki Zulfat ban San love ba ban taba yi love ba sai da na gan ki
Naji duniya in bar sameki ba zan iya rasha wani abu a rayuwa na.
Ajiya zuciya zulfat tayi tace don Allah best kayi hakuri but ni kam ka bani time naje nayi tunani
Don gaskiya I have to test you if ka ci jarabawa na
To gaskiya ba abin da zai hana ni aure ka sai Iko Allah.
Arman yace you're free to test me anything anytime
I have to go .
Zulfat tace you're free to go but put this on your mind you re on your test from now.
Arman yace mata bye.
Zulfat ta shige gida arman ya ja mota shi ya bar hara ba gidan.
Zulfat na shiga ta dauki waya ta ta kira frnd nata da take unguwa su tana dauka wa Zulfat ta ce hello Sumaya gashi nan ya fito pls ki yi komai yarda ba zai gane plan namu ba summy tace Haba Zulfat tun ba
Yau ba kike nuna min yanda kike so shi insha Allah I will do my best if you trust me? Zulfat tace yarda ce tasa har na sa ki a cikin yan gwaji abin so Na .
Summy tayi dariya tace Wallahi Zulfat don ke zanyi maki wanan Amma in ba ke ba Wallahi ba zan fara wanan ganganci ba don tsarai kin San kishi irin na Aminu Amma insha Allahu komai zai mana yanda muke so, Zulfat tace nagode kawa nagode Sosai Ina so ne ki taya ni zabi miji kaman yanda kika zabi Aminu ya zama aboki rayuwa ki , kiyi mana fatan muyi aure daya in har Arman yaci gwajin da zan mashi kin fito ne ? Summy tace na fito kaman gashi nan . tayi sauri ce ma summy ki fara aiki ki
Kuma ki bar waya a kunne don naji komai, summy
Tace to
Arman ya fito daga gidan su Zulfat yana tuki kaman
Mara lafiya yana tunani yarda yasa so Zulfat a zuciya shi yanzu in ya fadi jarabawa ta ya zai yi da so ta bai
Gaba tunani ba ya ga wata yariya fara saye da hijabi dogo har kasa ga ta da kyau ga haske duk da dare ne Amma yana iya gani haske ta da sauri Arman ya taka birki ya tsaya summy tayi sauri kwanta wa a gaban
Mota Arman tana kuka kaman wanda a ka turowa da mutuwa Arman yayi horn duniya Amma Zulfat taki matsawa da ya gaji sai ya fito a fusace yana shiri yi
Mata masifa sai yanda yaga tana kuka sai ta bashi tausayi Arman mutum ne mai tautsayi . Arman ne ya saya gefe yana cewa baiwar Allah lafiya? Mai ya faru? Baki da lafiya ne? Ko rasuwa a ka yi maku?
Duk summy na jin shi Amma taki ansawa da Arman ya gaji da tambaya ta sai ya juya zai wuce summy na gani haka sai ta sake daga murya ta sosai tana kuka da karfi ba shiri Arman ya dawo da sauri ya tsuguna a gefe ta yana cewa baiwar Allah don girma Allah ki fada min abin da yake damu ki?
Da kyar summy tace ni maraya ce bani da kowa iyaye mu su mutu su bar mu mu uku tsanadi haka yasa na shigo birni aikatau Sai Allah yasa gidan da nake aiki basu da kirki basu da imani na yini aiki Amma basu bani abinci rabo na da abinci tun shekaran jiya sai yau kuma da naci na yaro madam Na Wallahi ba laifi na bane ciki na ne ya kasa jumre yunwa shine madam na tayi min duka har da dauko wuka zata yanka ni shine na gudu muka hadu yanzu.
Arman ran shi ya bace Sosai yace Amma wasu sam
Basu da Imani Arman yace ki tashi ki goge hawaye ki
Zan baki kudi mota gobe ki wuce garin ku , kuma ai kin isa aure don Allah na roke ki in kin koma kauye ku ki samu wanda kika yarda da shi kuma kina so shi ki aure shi zan baki isheshen kudi da zai maki Ko mai na buki sanan kuma zan baki kudi da zaki ja jari
Wanda ko kina gidan mijin ki zaki taimaka ma kanne ki.
Summy ta goge hawaye ta tace nagode Sosai sai dai ban San Ina zan kwana yau ba don in na koma madam na zata kasheni. Arman yace muje sai na roke ta ko zata bar ki na yau kawai da safe kiyi wuce warki. Summy tayi sauri cewa Wallahi ko ta bar beni kana tafiya zata min abin da tayi niya kuma ta kwashe duk kudi da ka bani.
Arman yace kinga ba mutumci na bane na dauke ki
Nayi ta yawo da ke ina nema maki wurin kwana ,
Haka kuma bai dace na kai ki hotel ki kwana ba Kina
Matsayi mace, haka kuma bai dace na bar ki a nan ba don akwai bata gari Arman yayi shiru yana tunani
Sai chan yace yauwa Ina zuwa bari na kira matan da za aure don gidan su bai da nisa da nan sai na roke ta don nasan zata yarda ki kwana a wurin ta sai
Zulfat da jikin ta yayi sanyi har tana da ta sani gwada Arman data yi don duk abin da take so ga dan namiji
Ta samu a wurin Arman tana cikin tunani ta ji daya waya ta Na ringing Arman na kiran ta da sauri ta cire earphone na kunne ta da take jin su summy da shi.
Zulfat ta dauki waya Arman tace best har ka isa gida? Arman yace no best ban isa ba , Zulfat tayi sauri cewa lafiya best ? Arman yace best pls alfarma nake nema bai boye mata komai game da hali da summy take ciki ba har ya roke ta ko summy zata kwana a wurin ta sai gobe ta wuce garin su.
Zulfat tace ba komai ya kawo ta bari ta fadi ma mum nata. Arman yace ma ta ya gode sosai gashi nan zuwa. Kallo summy yayi yace Alhamdulillah matan da zan aura ta ce na kai ki yanzu muje sai na yi mata transfer kudi sai ta baki gobe kafi ki wuce don zan
Roke ta ta sa a kai ki park.
Summy ta ce nagode Sosai Allah tsaki da alheri Allah nuna maku Aure ku, Arman yace Amin suka wuce gidan su Zulfat.
Suna isa yaga Zulfat tsaye a harabar gidan ya yi parking mota yana sayawa yaga summy ta fito da gudu ta rumgume Zulfat suna dariya da hamdala
Arman ya cika da mamaki sai jin murya Zulfat yayi tana cewa best kana mamaki ne to congratulations ka cinye duk tests naka Na yi scoring naka 💯 .
Arman yace Kina nufi dama duk plan ne kuka shirya? Zulfat tace yes meet my best friend Sumaya.
Summy ta maso kusa tace da Arman sorry ba laifi na bane laifi gimbiya ka ce nasha ce mata ba lalle bane a samu masu cin Amana a rayuwa . Dama a ko da yaushe buri Zulfat ta samu miji mai so addini,
Mai ilimi , wayeyye, mai kishi abin da yake so, wanda yake so taimako, da Wanda abin hannu shi bai dame shi ba to Alhamdulillah kawata Na maki murna don Arman ya hada duk abin da kike nema har ma ya wuce.
Zulfat ta maso kusa da Arman tace am sorry love.
Ba shiri Arman ya washe baki yace you're forgiving.
A kwana a tashi ba wuya yau ce ranan da su Fakhriya da nasreen suka gama makaranta su murna da fari ci bata misiltuwa a wurin nasreen don burin ta bai wuce ta dawo gida ta sanan ma mummy da daddy ta soyayya ta da Ahmad.H