3

1.1K 86 1
                                    

💔 *TAK'ADDAMA....* 💔

*HASKE WRITERS* *ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)💡*

*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_

*Zuwaga masu tambayana littafina na kudi ne koba na kudi bane?ba littafin kudi bane....*😉
               
                   *3*
   Sumar tsaye tayi janan a jikin gate din ganin gilmawayar mutum dauke da mutum tamkar Babu Rai, gabanta ne ya tsananta faduwa dakyar ta iya daga kafafuwanta ta taka zuwa cikin gidan tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta karasa jiki Babu kwari bakinta dauke da sallama ta kutsa kanta cikin patlorn....

Cakkk ta tsaya bakin kofar Tana hangensa Yana famar hura masa iska a bakinsa hannunsa daya danne da kirjinsa,hilal dake kwance sai sauke numfashi yakeyi sama sama kusan minti goma sanan numfashinsa ya soma dawowa daidai,Muhammad dake Kansa ya dago Kansa fuskarsa jike da zufa,....dagowar da zaiyi sukai Ido hudu da janan wadda ke tsaye kamar mutum mutumi cike da fargaba,shi Kansa Saida ya tsinci Kansa cikin faduwar gaba dan be taba kawowa wani Dan uwan Hanan zaiyo musu dirar mikiyaba a wanan lokacin batare da sun yanke shawarar yadda zasuyiba,Dan haka murmushin karfin Hali yayi yana kallonta yace "ya kika tsaya a Nan?shigo Mana kin tsaya a kofar daki"...kalle kalle ta shigayi cikin patlorn Wanda yake hargitse tamkar anyi dambe ciki tana tafe tana juye juye kamar me neman wani Abu har ta karaso ciki,dakyar ta iya dofana duwawunta kan kujera kamar wadda zaa Kama ko zaayiwa wani Abu,

"Zauna da kyau Mana kin takure a hakan ai"...girgiza Kai tayi dakyar ta tattaro natsuwarta ta dubesa da kyau sanan ta gane koshi din waye Dan tasan shi a wajen bikin nasu Hanan sanan tayi ajiyar zuciya cikin sanyin murya tace "Ina yini"

"Lafiya kalau...janan ko idan ban mance ba"..yace Yana murmushi ta gyada Masa Kai itama tana murmushin karfin Hali,

"Meyasami yaayah hilal din?badai ciwonsa bane ya tashi"ta jeho Masa tambaya cike da rudani har gyalenta na zamewa...cije lebe Muhammad yayi "ehh ciwon nasa ne Amma ya samu sauki"....

"Ina matar gidan take na ga gidan haka?sanan Kuma na ganku ku biyu ga ya hilal Babu lafiya?".. ta karayi Masa wata tambayar a Karo na biyu..ya bude Baki zai Bata amsa kenan hilal ya Shiga mutsu mutsu dafe da gefen kirjinsa Yana sauke numfashi a hankali sanan bakinsa Yana motsawa can kasa kasa yake Kiran sunanta ".. Hanan...kina Ina?Ina kika Shiga ne?...kin boye kada in ganki koh?kardai kicemun kin mutu kin barni...."girgiza Kansa ya shigayi tamkar Mai tabin hankali lokaci daya hawaye na gudu a gefe da gefen fuskarsa "wallahi Baki mutu ba Hanan nasan bazaki mutu kibarni ba....kinsha fadamin mudin ruhi daya ne gangan jiki kowa da nasa"....zabura tsaye janan tayi Tana kallon hilal cike da mamaki da tsananin tsoro hade da furgici....bakinta na rawa ta Shiga nunasa da Dan yatsa "ya hilal me kake fada haka?naji kana wata magana ne tamkar Wanda ya zare ko ya samu dimuwa ka fadamin meke faruwa?me jikina yake fadamin me kunnena yake jiyowa daga bakinka?magana kakeyi tamkar Yar uwata batada Rai"...

Mikewa yayi tamkar wani zararre Wanda aka tsikara da allura cikin kuka ya soma magana "abinda kikeji gaskiya ne janan,ba mafarki kikeyi ba bakuma zarewa nayi ba cikin hankalina nake da hannuna na kashe matata Hanan"....wata juwa ce taji tana dibarta tamkar zata Fadi kasa da kyar ta dafa gefen kujera tana zaro Ido waje ta kasa magana...."TAK'ADDAMA ce ta Shiga tsakanina da ita a Daren jiya Wanda hakan yayi sanadiyyar da na kasheta da hannuna"

"Ya isahhhhhh"shine abinda janan tace jikinta na tsananin rawa Nan da Nan idanuwanta suka ciko da hawaye ta Shiga girgiza "Kai inhar abinda ka fada gaskiya ne to tabbas ka tafka babban kuskure Wanda zakayi danasani na harabada.....idan har dagaske kakeyi ka kashe Hanan Ina gawarta"ta kafesa da Ido hawaye na gudu a fuskarta tamkar an bude famfo..

Cikin kuka ya Shiga kada kansa dik ya fita hayyacinsa,"janan bansan inda gawar Hanan take ba ni kaina yanzun banida wani buri Wanda ya wuce insanya gawarta a idanuwana wallahi bansan inda gawarta take ba na yadda gawarta da hannuna na koma in dakkota bansan inda takeba janan Ina cikin bala'i"...ya Fadi kasa turus ya zauna Yana Rusa kuka wani irin kallon tuhuma janan take binsa dashi hawaye na cigaba da zuba a idanuwanta tabe Baki tayi "wanan maganar kanzon kurege ce ya hilal karya kakeyi wallahi Dole sai ka fito da Hanan sai ka fadamin inda Yar uwata take idan ba haka ba zaka fuskanci hukunci"... Tana Gama fadin haka ko gyalenta Bata dauka ba da Jakarta tayi hanyar waje idanuwanta sun rufe ko ganin gabanta batayi haka ta fice gidan da sauri....Mai gadi ne ya bita da kallo Yana girgiza Kai ko baa fadaba yasan cikin gidan Nan Babu lafiya.....

TAK'ADDAMAWhere stories live. Discover now