16

744 56 2
                                    

💔 *TAK'ADDAMA....* 💔

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡

*SLIMZY✍🏼*
__Wattpad@slimzy33_

*Sakon taaziyya ga Yar uwarmu hafsat miss xoxo data rasa mahaifinta Allah yayi Masa rahma ya gafarta masa*

*16*

Kiran sallar farko na masallacin cikin asibitin kamar a kunnen janan akayishi,a furgice ta zabura da niyyar tashi samm ta mance cewar hilal a jikinta yayi bacci,nauyin da taji ne ya fargar da ita cewar akwai mutum a jikinta,kallonshi takeyi yadda akai har ta rungumesa tsammm a jikinta bacci ya daukesu dagashi har ita bacci sukai me nauyi ta gane hakan ne ganin yadda hilal ke faman sauke numfashi Yana barcinsa Mai lafiya,tunanin yadda zata janyesa daga jikinta takeyi saboda wani mugun takaici da ya taso Mata na haushinsa da tsanarsa da takeji a cikin ranta dikda jiya zuwa yau akwai sassauci cikin tsanar da takeyi Masa zuciyarta ke ayyana Mata why not ta ingujeshi kawai ya wani kwanta ya lafe Mata a saman kirjinta inda rigarta ta zame ta baya ya Dora kansa a saman kirjinta Yana gogan boobs dinta...Dan tsaki tayi da niyyar turesa a jikinta ga wani ciwo da wuyanta keyi na ta kwanta ba daidai ba wata zuciyar ce tace ke musulma ce kodan ciwon da yakeyi ki tausaya Masa Mana Allah zai Baki Lada ko babukomi ai mijinki ne kuma aljannarki tana karkashin kafarsa Dan haka ki bishi a hankali har ya warke kome zakiyi kiyi Masa...da wanan shawarar ta Shiga kici kicin daukeshi daga jikinta a hankali batare da ya tashi ba ta kwantar da kanta ta zamo kasa garin zamewar ne karfen gado ya bugi bayan kafarta Tai Yar Kara "ashhhhhh"ta rike wajen tanajin radadin azaba,...shiko hilal baccinsa yakeyi lakadan sai Dan juyi da yayi saboda karar da tayi Amma ba tashi yayi ba hannunsa na makale da side din zuciyarsa...

Da kyar take dingisa kafarta ta Shiga toilet ta kunna ruwan zafi ta ga akwai zafi sosai sai kawai ta rufe bayin da niyyar yin wanka ta dauro alwala,...cikin minti talatin tayi wanka ta dauro alwala ta fito ta kalli gefen gadon ta gefen idonta taga bacci yakeyi har yanzun,ta watsa Masa wata uwar harara...sanan ta sunkuci dadduma ta nufi waje ta rufo Masa kofa....

*********
Ummi ce zaune a sitting room misalin karfe goma na safe ita da wata Mata wadda zasuyi saani ita da ita ,gwauron numfashi ummi ta sauke "hajiya sabuwa kinji dalilin kiranki da nakeyi abun ya isheni tun jiya nakeson kiranki insanar dake babban jarabawar dake Shirin tunkaro mu"

Murmushi hajiya sabuwa ta sauke "nikam hajiya inhar wanan matsalar ce me sauki ce tunda kince janan batada wayau Kuma tana daukan shawara tunda kece da kanki kikabata shawara kika lallashi abinki har ta yarda ta auri hilal din?to ai ta inda aka hau tanan ake sauka yanzun ma kece zakiyi amfani da dabararki wajen koya Mata yadda zata saci zuciyar mijinta kafin a Gama shariar Dan na tabbatar alkali zai iya cewa saidai a Raba auren daya daga cikinsu,Kinga idan tayi nasarar samun Kan mijinta mantawa zaiyi da soyayyar wata Hanan ko ya ganta a kotun bazatayi wani tasiri a zuciyarsa ba da alkali ya bukaci ya bawa daya takadda ita zaibawa wallahi"

"Hajiya sabuwa Anya janan zata yarda ta wani saki jiki da hilal?kinsan fa yadda takeson Yar uwarta kinsan yadda suka shaku ko ni ban da nake uwarsu wallahi ban Isa ince nasan tsakanin janan da Hanan ba tsakaninsu sai Allah wallahi nasan zaiyi wuya ta yarda cewa zatayi taci amanar Yar uwarta wallahi Ina cikin damuwa da tashin hankali ko baccin korki banayi daurewa kawai nakeyi saboda kada alhaji ya harbo jirgina Dan ba karamin sabamin zaiyi ba,ai ko maganar hakura da mutuwar yarsa da yayi ni nayi amfani da kissarmu ta mata saboda nasan plan b Dina inba hakan ba ke kinsan yadda abbansu yakeson Hanan nunar Masa nayi kawai a rufawa zumunci asiri"ta karashe maganar cikin tsananin damuwa,

Dariya sosai hajiya sabuwa tayi "shegiya naira,nasan saboda ita dik kika shirya wanan tuggun da yake shi kuma alhaji kabiru yanason Yan uwansa da zumunci sai kawai ya afka ciki,...to idan haka ne ke kina tsoron Kar janan ta ganoki kibar Komi a hannuna inhar aka sallami mijin nata a asibiti zanje gidanta nida farha da niyyar munje ganin daki to insha allahu a nan zanyi mata famfo aminiyata nasan ta inda Zan bullo Mata ai ta yaro kyau take Bata karko hajiya ki kwantar da hankalinki wanan daular mu zamuci ta ni wallahi kinsan dama bawai jinina ya hadu da Hanan bane saboda shegen miskilancinta"...dariya sukasa a tare hade da tafawa ummi tace "Allah ko hajiya"

TAK'ADDAMADove le storie prendono vita. Scoprilo ora