💔 *TAK'ADDAMA....* 💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33__Mutanena masoya_ _littafin_ *TAKADDAMA* _wanan_ _shafin nakune sakon gaisuwa da fatan alheri gareku_
*MUNAUWARAH*
*NASBAT GWANDU*
*TEELERH*
*TAEBAT ADAM*
*MAMAN* *KHALID* (masoyiyar janan😂)
*FATIMA ISMAIL* *MAAJI*
*UMMIE BELLO* (Ina yinku)
*UMMU SADEEK* (inlaw)
*REENS CAKES* *PASTRIES*
*JAMILA MUSA*
*PRETTY JIDDAH* *LURV*
*HAJIYA MARYAM* *SAKATARE*
*MOM SAEED.BILKISU* *KANKIA....* _wanan_ _shafin naku ne_*INNAH WURO* *NOVELS*
*TASKAR MRS.JMOON*
*AREWA DAMSEL*
*LATEST NOVELS*
*ZAUREN ZUMUNTA*
*MRS J.MOON* *PALACE*
*SOPHIE AND VC* *GROUP NOVELS*
*MURMUSHIN NOVELS*
*GROUP OF HAUSA NOVELS*
*DOCUMENTS HAUSA* *NOVELS* _da_ _sauransu._
_Nagode kwarai da kauna sakon fatan alherinku ya_ _iso gareni da dik Wanda ban ambaci sunansa ba_ *SLIMZY* _nayi muku son so fisabilillahi_*23*
Can kasan makoshin ta tayi sallamar Amma hakan be hanasu Jin sallamar tata ba,hajajju da afnan kadai suka amsa sallamarta,Banda ummu da ke breakfast a tsanake ko kallon sashen da take batayiba hakan yasa Hanan Jin kuka na kokarin taso Mata Amma sai ta danne dikda kallo daya zakayi Mata ka hango kwalla kwance a cikin fararen idanuwanta,..karasawa tayi cikin parlorn ta nemi gefe ta rakube ta hada kanta da gwiwa,
Afnan ce ta taba hajajju dake faman Kai doya da kwai cikinta, bakinta cike da doya ta kalli afnan da alamar tambaya a fuskarta,rau rau afnan tayi da Ido sanan Tai mata magana da ido ta nuna mata Hanan wadda ta hade Kai da gwiwa,..Saida hajajju ta hadiye doyar bakinta ta kora da tea sanan ta juyo gefen da Hanan ta kifa Kai "ke Hanan bazaki karya bane?ko kinci abinci a gidan faty matar kabiru ne?(maman samha)"Girgiza Kai Hanan tayi batare da ta d'ago Kai ba cikin rawar murya tace"nakoshi naci abinci"ta goge hawayenta sanan ta d'ago kai idonta jajir,
Aiko kamar hadin Baki suka hada Ido da ummu wadda dama a kule take da Hanan din tun da suka dawo kotu taji abinda tayi, a fusace ta Soma masifa "dama ya zaayi kici abinci tunda kina tunanin kanin ubanki hilal hankalinki gabaki daya na wajensa dubi dik yadda kika koma kika rasa natsuwarki kin koma kamar wata zautacciya ko zararriya,to wallahi ko zaki mutu Hanan bazaki koma hannun hilal ba matukar Nina haifeki nono na kikasha kika girma shasha Sha wadda batasan ciwon kanta ba tashi ki bacemun daga gani"...da sauri hanan ta Mike fuuuuu Tai hanyar barin parlon wajen fitane sukai arangama da sudais Wanda yake waje tuntuniyana amsa call ya shigo hannunsa rike da wayarsa idon Hanan gaba daya ya rufe ta turesa wayarsa iPhone x max ta fadi akan tiles ji kake tassssss ko ta kansa batayiba ta shige dakinta ta rufo kofar da karfi,
Hajajju kada Kai kawai tayi batare da tace komiba,....wanan wayar da ta fasawa sudais shi ya Kara tunzura ummu ta shiga surfa masifa kamar zata bugi Hanan takeji saboda takaici,Daukar wayar kawai yayi yasanya a aljihunsa yabi bayanta har kofar dakin ya tura kofar Amma Kash a rufe take tasa key shasshekar kukanta kawai yake iya juyowa daga inda yake zuciyarsa nayi Masa zafi.....
*********
Cikin kwarewa da hikima ta iya sarrafa magana irin na kwararrun Mata Yan bariki wadanda sukai yawo sukasan rayuwa kala kala Haka hajiya sabuwa ta Shiga yiwa janan huduba kala kala,ita kuwa janan zaune take kamar an dasata kamar wata kurma Haka take sauraren yadda hajiya sabuwa ke koya Mata kissa kala kala da salo irin na zama da kishiya Wanda Babu boka Babu malam shi kadai idan tayi yadda hajiya sabuwa tace ta tabbatar Komi taurin Kai irin na namiji sai ya sauka....tabbas wanan lokaci ne daya dace ta kwaci yancinta a wajen mijinta wanan ba kyauta ko wani abun duniya bane Wanda suka Saba sadaukarwa da juna itada Hanan,Dole ta danne kaunar da takewa Hanan itama tasamu gurbi a zuciyar mijinta kamar yadda Hanan din tasamu tunda ta rigada ta yada makaman yaki na ganin ta rasa Ahmad dinta,wanan karon hakuri zatayi ta rungumi kaddararta na kasantuwarta matar hilal....hilal namijine Wanda ko wace mace zataso kasancewa dashi Koda batajin sonsa Amma zuciyarta ta matukar sosuwa da abinda yayi Mata Akan Hanan,...babban matsalarta shine tanada matukar kishi,Kuma tasani Hanan ita kanta ba baya ba wajen kishintasan wacece Yar uwarta,..zamansu a karkashin Miji daya babban damuwa ne Dan Bata iya controlling kanta Akan kishi....
KAMU SEDANG MEMBACA
TAK'ADDAMA
Fiksi SejarahHilal Ina fatan wanan fadace fadacen da mukeyi a tsakaninmu ya zamo iyakarsa cikin gidan iyayenmu,baa gidan aurenmu ba saboda Ina matukar tsoron wanan fadan da mukeyi Kar ya kawo sanadiyyar tarwatsewar farin cikin mu,kada hakan ya kasance sanadiyyar...