[1/11, 11:43 PM] 😍SLIMZY😍: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HfYlzcMbch1C2MY5GXliZ8
[1/11, 11:44 PM] 😍SLIMZY😍: 💔 *TAK'ADDAMA....* 💔*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33__Wanan shafin nakune_ _kacokan_ *TAK'ADDAMA* *FANS* *GROUP...* _nagode da kauna son so fisabilillah🌹_
*11*
Washe gari....
Tana kwance a daki inda ya kasance dama masaukinta ne inhar taje gidan nan take sauka Dan haka a nan aka sauketa tana kwance ta kifa ciki tana fuskantar kofar shigowa ta kafe wajen da ido tayi zurfi cikin tunani...wani irin d'aci ne yake tasowa daga cikinta zuwa bakinta dakyar ta iya hadiye miyon bakinta tunaninta yayi nisa wajen hilal...mamaki ne kawai takeyi yadda ya iya yadda gangan jikinta batare da wani tunani ba sanan ko a radiyo beyi yunkurin sawa ai cigiyarta ba ta gasgata hakan ne saboda tunda taje gidansu gwaggo kullum a jikin radiyo take ko zataji Ana sanarwa na nemanta Amma shiru shi ya Kara tabbatar Mata da cewar hilal baya kaunarta dama neman maraba yakeyi da ita kenan?...juyi tayi ta gyara kwanciyarta hade da sauke ajiyar zuciya ta runtse idanuwanta tana Jin wani irn ciwo a zuciyarta...Abu daya ne zuciyarta batayi Mata adalci ba shine yadda ta kasa cire hilal cikin zuciyarta Babu minti ko second din da zai buga batare da ya Fado Mata a Rai ba....kamata yayi tunda ya mance da ita a tunaninsa ya yadda gawarta why not itama tasashi cikin kwandon shara ta mance da lamarinsa?....ajiyar zuciya ta sauke daidai nan aka turo kofar dakin hade da Yar sallama batare da ta bude idanuwanta ba ta amsa sallamar Jin muryar wadda Tai sallamar....Yar yarinya ce Yar shekara Sha hudu ta shigo "ya hanee kizo inji ummu Wai su uncle sunzo da abie zakuyi magana"..batare da ta bude idonba ta bude Baki a sanyaye tace "afnan ganinan zuwa"..."to ya hanee"..ta juya abinta ta rufo kofar...karar rufe kofarta yasa ta bude idanuwanta da suka canja kala ta janyo gyalen rigar dake jikinta wadda ummu ta Bata ta yafa ta bude kofa ta nufi parlorn...
Can gefe ta zauna cike da ladabi kanta a kasa zuciyarta na tsananta bugawa...uncle Nasir ya Kira sunanta a kausashe "Hanan"..
"Naam abbah"
"Abinda yasa muka kiraki nan shine mun yanke shawarar bi Miki hakkinki Akan abinda akayi Miki sanan Ina Mai tabbatar Miki da kin Gama zama da hilal harabada Dan Wanda zai dakeka ka suma ya dau gawarka ya yadda batare da wani tunani ba ba masoyin gaskiya bane kinji"
Ta gyadawa Uncle Nasir Kai idonta ya kawo ruwa ta cije lebenta zuciyarta nayi Mata zafi ..abie ya karbe zancen "jiya nasa ayimun bincike akansa a can garin dik wani mitsinsa nasa asa mishi ido cikin sati daya kafin mugama shirye shiryen da zamuyi Akan lamarin Dan bazamu Bari a ci zarafinki ba a keta Miki haddi Dan haka ki kwantar da hankalinki dubi dik yadda kika rame kika lalace Hanan ki cire tunanin Dan isaka a ranki ki kwantar da hankalinki ki dawo da jikinki ki kuma saki jikinki kinji?"
. "Toh abie insha allahu inaso inzo in gaida ammiey inyi Mata kwana biyu"..murmushi ummu tayi na Jin dadin abinda Hanan tace koba komi tasan idan taje can din zata saki jikinta "to ki shirya anjima yayanku Umar dama zaizo ya kaiki sahad kiyi siyayya ki sai kayan sawa tunda bakizo dashi ba da dik wani abinda kike bukata kafin sati me zuwa zanje Dubai Zan dubo Miki wasu can yanzun uncle dinki ya bada 300k a Baki""Nagode uncle"tace cike da ladabi muryarta na rawa tamkar zata fashe da kuka...cike da tausayi suke binta da kallo Abbie ne ya sauke numfashi ya nisa ya ce "tashi kije Allah yayi miki albarka"
"Ameen"ta karba ta Mike tamkar wadda kwai ya fashewa ciki ta nufi dakin hajajju inda take jiyo muryarsu da afnan suna dramer...
Ummu ta dubi abie fuskarta babu walwala "wallahi yaayah bazan taba Bari Hanan ta koma gidan wanan Dan iskan yaron ba Dan ta Gama zama dashi harabada kuma wallahi sai yaci prison yadda ya wulakanta Hanan sai mubi Mata hakkinta tunda iyayenta sun kasa bi Mata hakki yanzun kar muce komi dan banaso tun yanzun su fahimci cewar Hanan din tanada Rai".. girgiza Kai kawai abie yayi batare da yace komi ba Dan shi kansa tun jiya yake cikin alhini shidai be cika magana bane....uncle Nasir ya fishi zafi....
ŞİMDİ OKUDUĞUN
TAK'ADDAMA
Tarihi KurguHilal Ina fatan wanan fadace fadacen da mukeyi a tsakaninmu ya zamo iyakarsa cikin gidan iyayenmu,baa gidan aurenmu ba saboda Ina matukar tsoron wanan fadan da mukeyi Kar ya kawo sanadiyyar tarwatsewar farin cikin mu,kada hakan ya kasance sanadiyyar...