💔 *TAK'ADDAMA....* 💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33__Wanan shafin kyautane ga daukakin masoya littafin_ *TAKADDAMA*... _ina jin dadin comments da sharhi da yake zuwamun ta ko ina allah yabar kaina ....masu comments suke takaddamar_ _yanzun... masoya hanan da janan kullum kamar zaa dambace😂😂..._ *SLIMZY* _na godiya...i luv u all_🥰😍❤💥
_wanan shafin sadaukarwa ne gareki diyar albarka_ *UMMULKHAIRI.S.USMAN* ( *AFEE)* 👱🏼♀ _....best daughter ever i cant luv u less_
*38*
Kauda kansa yayi gefe yanajin wani abu a zuciyarsa dangane da janan saidai ya kasa amincewa da hakan ya Kuma kasa bawa zucuyarsa dama...juice ta kawo me sanyi da cups ta dire tanata faraa "afee zokisha lemo bari in zuba miki autar ummu...keman best sis gidanku ne sai ki zuba da kanki"...yi tayi tamkar bata jita ba itako ta zubawa afee juice ta mika mata ta karba ta soma sha hilal so yakeyi tai masa magana amma ta share sai kawai yayi gyaran murya "kin zubawa kanwarki juice amma kin kasa zubawa mijinki koh?ta wani fannin kuma yayanki to zubamin tunda ni an wareni ba gidanmu bane?"cikin sigar zolaya yayi maganar,..Kayataccen murmushin nan nata da ya zame mata jiki shi tayi sai ta dan hararesa "shirin zuba maka nakeyi fa amma kace wai na ware ka kataba ganin inda mata ta ware mijinta?"..tai maganar tana dariya ta kalli sashen hanan wadda tai kamar batasan dasu ba "best sis ko Zaki shigar ma mijinki ne ni kanwata ta shigarmun"
Yatsina fuska tayi ta kauda kai sanan tace "babu ruwana tsakaninku ne..."hilal yana lura da yanayin hanan yasan ta shaka a zuciyarsa kuwa be damuba dan yaune rana ta farko da yajisa a sake tare da janan kuma ya kudurtawa zucuyarsa faranta mata itama tun kafin allah ya kamasa,
Dariya sukeyi suna kallon hanan suna tsokanarta abbah yayi sallama...yana bude labulen parlorn yayi tozali da yaran dan uwansa ya washe baki nan da nan farin ciki ya kullube abbah "ah ah ummulk khairi yau kece a gidan?"afee ta sadda kanta tana dariya ta zamo daga kujera ta rusuna cikin ladabi ta gaida abbah...ya amsa cike da kulawa hanan kuwa tana ganin abbah ta turo baki akai saa ita yake kallo yana faraa "yar abbah yadai ya akayi ne kiketa bata rai kina daura fuska waya tabamun ke?"..kara narkewa tayi "abbah kanaganin ya hilal da janee suna tsokanata ko?"
.zaro ido hilal da janan sukai a tare "yaushe muka tsokaneki kai best sister rigimarki ce dai kawai kikeson hadamu da abbah yayi mana fada"..."Komadai menene abar tsokanar yar abbah"abbah sai faraa yakeyi yana binsu da kalo lukutan can baya ya tuna haka suke bajewa a parlor duka su ukun suyita tsokanar juna aitasa hanan kuka saboda saurin kuka sa shak'a da allah yayi mata ko tsokanar akeyi janan daurewa take kada aga lagonta koda ranta ya baci,
.ummi ce ta fito daki ganin abbah yasa itama ta fadada faraarta "abban yara ashe ka shigo""Na shigo naga suna tsokanar yarki gatanan tana nema tai kuka Hanan dubi dan allah ashe har yau bata girma ba'ya nuna hanan da yatsa yana dariya,
Faraar Dole ummi ra kirkiro "ai hanan sakarya ce ke meyasa Baki rama fada ne wai?ki rinka ramawa"..daga kai hanan tayi fuskarnan a cunkushe can kasan zuciyarta kishi ne dankare kamar zai kama da wuta shiko hilal gabaki daya dik juyin da janan zatayi akan idonsa takeyi so yakeyi ya hada ido da ita amma taki bashi dama yasani yana hada ido da ita zai kashe boss din...
Kallon agogo ummi tayi biyar da rabi "a tashi a tafi gida nima mijina ya dawo maza ku shirya kada yamma tayi ga hadari na haduwa"
.
"Akwai hadari Nima ganinsa yasa nataho dan idan ruwa ya tsareka a waje saidai ka kwana"Hanan ta amshe zancen da "abbah saimu kwana ai"...ummi ta kalleta da sauri "baa gidana ba kun wuce da zaman nan oya a tashi"..hanan ta turo baki harga allah batason tafiyar tanajin dadin ganin abbah ji takeyi tamkar mahaifinta ne tana missing dinsa sosai kuma tana missing din ummu saidai tasan ummu tana fushi da ita amma zata kira hajajju da ya umar tayi magana dasu su rokar mata ummu gafara....a tare suka mike suka dauki mayafinsu,..
YOU ARE READING
TAK'ADDAMA
Historical FictionHilal Ina fatan wanan fadace fadacen da mukeyi a tsakaninmu ya zamo iyakarsa cikin gidan iyayenmu,baa gidan aurenmu ba saboda Ina matukar tsoron wanan fadan da mukeyi Kar ya kawo sanadiyyar tarwatsewar farin cikin mu,kada hakan ya kasance sanadiyyar...