💔 *TAK'ADDAMA....* 💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*24*
Zama yayi bakin gadon Yana furzar da iska daga bakinsa,tana cikin toilet tana hada Masa ruwan wanka,shiko minti minti yakan kalli agogon hannunsa Wanda yake ganin tamkar gudu yakeyi ki yake tamkar ita zaije ya gani a zahiri ba labarinta ba,...tana fitowa daga toilet din kmr Wanda aka tsikara ya Mike tsaye be jira cewarta ba ya zare jallabiyar jikinsa,ya Shiga kici kicin cire agogon hannunsa ya ajiye a gefen madubi,ta karaso cikin dakin da niyyar ce Masa ga ruwan wankan sa nan ko kafin tayi magana ya ratsa ta gefenta da sauri ya fada toilet ya rufo kofar da karfi,kallo kawai ta bishi dashi ta wuce abinta batare da ta jirasa ba,.....cikin minti goma ya watsa ruwa ya fito daure da towel a kugunsa,tana sawo Kai cikin dakin sanye da milk colour din rigar bacci iya gwiwa Mai hannun vest ta daure kanta da milk colour din siririn mayafi,samm ta manta yadda ta shigo dakin sai da taga ya tsaya cakkkk da abinda yakeyi Yana bin ta da kallo daga sama har kasa da shanyayyun idanuwansa yasa Tai saurin kallon jikinta,boobs dinta sun ciko fammmm a cikin rigar baccin wadda take da gidan braa a ciki ko bra din babu a jikinta,da sauri tasa hannu ta rufe kirjinta ta sunkuyar da kanta jikinta na tsananin rawa,kunya kuwa kamar kasa ta bude ta Shiga,
Jin tsigar jikinsa ta Soma tashi yasa shi saurin kauda idonsa daga gareta ya nufi gefen madubi ya Soma shafa mayuka kala kala da oil na gyaran gashi,...karar fesa turarensa ce ya ankarar da ita da yabar kallonta yasa ta d'ago Ido dai dai ya juyo da nufin saka jallabiyarsa sukai ido hudu,...yadda takeyi ma dariya ta basa Yana zura jallabiyarsa ya karaso inda take ya tsaya dafff da ita Yana jiyo iskar dake fita daga hancinta "janan ya dai...."ya lakaci hancinta hade da zuba Mata idanuwansa dake rudar da dik macen da ta gansa ,bakinta na karkarwa tace "ummm ummm babukomi dama cewa nayi ko zakaci abinci kafin ka fita"..a sanyaye Tai maganar,..
Ruko hannunta yayi cikin nasa Yana murzawa a hankali Yana cigaba da kallonta,tausayi janan take basa Dan yasan tabbas Bata sonsa biyayya ce kawai tayi ta iyaye,yasa take Masa wanan kyautatawar Amma insha allahu shima zai kyautata Mata Yana jin zai sakarwa Ahmad ita kawai ya aureta itama taji dadin rayuwa....ta bangarenta kuwa nan da nan salon da yakeyi Mata yasa Jin jikinta na canjawa ta lumshe idanuwanta tanajin wani Abu na rasa jinin jikinta dangane dashi,...ganin yadda take Shirin faduwa yasa ya rungumota jikinsa ta fada,"so kikeyi ki fadi kasa ki jamun ko?"ya d'ago kanta Tai saurin sunkuyar da Kai cike da kunya da faduwar gaba,..
Jikinta dumi tamkar wadda kejin zazzabi yasa shi saurin ce Mata "Baki da lafiya ne naji jikin naki da zafi?"...girgiza Masa Kai tayi "Haka jikina take normal temperature Dina kenan"cikin siririyar murya ta bashi amsa,..
Shafa gefen wuyanta yayi hade da zareta daga jikinsa "Bari inje wajen Muhammad in dawo kinji?ki kula da kanki sai na dawo"bejira cewarta ba ya fice a dakin ya barta nan tsaye dik jikinta ya saki wani irin Abu takeji sabon yanayi dangane da mijinta....dakyar ta motsa daga inda take ta fada gefen gado ta zauna tana sauke numfashi...runtse idonta tayi tana tuna irin rungumar da yayi Mata da yadda yake Wasa da lallausan hannunta...sanan tasa hannu ta shafo gefen wuyanta inda yasa hannunsa a wajen ta sauke ajiyar zuciya hade da wani irin murmushi Wanda ya subuce Mata...kwanciya tayi Tai rigingine ta fada duniyar tunani....
********
"Jiya nida zainab mukaje sahad store Abuja siyayya saboda inajin yanzun cikin ta seven month kenan to can nace Mata muje shine Naga mutuniyar Hanan"...wani irin sanyi ne ya ratsa zuciyar hilal har yasa ya washe Baki Yana faraa,Wanda rabonsa da yin faraa ko dariya Haka har ya mance,...cikin zumudi ya dubi Muhammad cike da kosawa yace "umhmmm Ina sauraronka bani labari friend""To sarki me Hanan,da faraata ta taremu nida zainab tamkar wani Abu Bai faru ba,ni banma ganeta ba zainab ta ganeta saboda ta rame Amma tayi fari sosai fiye da tunaninka ita da kanwar nan tata afnan wadda suke Kama sosai,shine bayan mugaisa take ta tsokanar zainab yaushe zata haihu,shine fa na sako Baki nake ce Mata aimu ta gujemu balle muma ta juye Mana baby,sai kawai Tai murmushi...shine bayan mungaisa nake tambayarta siyayya sukazo yi ne?shine take cemin ai siyayya sukazo yiwa afnan Wai tasamu admission a kaduna state University kadsu sun Bata phermacy,to dai nayi Mata maganar ka saidai tayi murmushi kawai kasan ni akwai Yar kunya tsakanina da Hanan Dan yayanta ta daukeni,to dai tacemun tare zasu shigo gobe zasu fara registration ".
YOU ARE READING
TAK'ADDAMA
Historical FictionHilal Ina fatan wanan fadace fadacen da mukeyi a tsakaninmu ya zamo iyakarsa cikin gidan iyayenmu,baa gidan aurenmu ba saboda Ina matukar tsoron wanan fadan da mukeyi Kar ya kawo sanadiyyar tarwatsewar farin cikin mu,kada hakan ya kasance sanadiyyar...