💔 *TAK'ADDAMA....* 💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_*ASSALAMU ALAIKUM*
_masoyana ina godiya da adduoinku allah ya saka da alheri allah ya bar zumunci nasamu sauki slimzy na godiya sosai_
*45*
*Bayan sati biyu*
Cikin wata daya ba kwanaki da haihuwar hanan yara sunyi wayau sunyi bulbul kamar ba yan sati uku ba sosai sukai kubul kubul dasu hanan na zaune tana rugume da hilal jikinta dik ta dan rame tayi fari hilal yayi sallama cikin dakin da take zaune gefen gado hannunsa rike da manyan ledojin da yayi shopping yana sanye da shadda milk colour tai matukar karbarsa sajen fuskarsa yayi baki wuluk kasa daina kallonsa hanan tayi saboda wani kyau da yayi mata dikda ramewar da ya danyi,
Ganin ta kafesa da ido yasa ya sauke lallausan murmushi ya sunkuyo da kansa daidai fuskarta suna shakar numfashin juna ya hura mata iska sanan ya hade bakinsu waje daya yana dan kissing dinta a hankali,..
Janyewa tayi daga gareshi tana murmushi ta sunkuyar da kanta kasa haka kawai ta tsinci kanta cikin tsananin faduwar gaba wanda batasan daliliba hannu yasa ya dan ja hancinta ya zauna gefenta ya kalli gefensa na dama yana dan dube dube tana lura dashi su hanan yake nema tana cigaba da kallonsa tana murmushi idonta cike da kwalla wanda batasan dalilinsu ba,
Kamar zai tambayeta sai ya wayance ya mika hannu ya karbi lil hilal "anmmm dadys boy...iyye yaron dady yayi wayau yayi girma dubi har yafi su Hanan girma"yana cillasa sama yana masa wasa yana wangale baki yaro mai kama sak da mahaifinsa tamkar dan larabawa,
Kallonsu takeyi a zahiri amma cikin zuciyarta tayi nisa da tunanin yar uwarta wanda ya zame mata tamkar ibada babu dama data zauna sai janan ta fado mata a rai ganin yanata wasa batace komi ba yasa ya kwantar da yaron ya matso dafff da ita yadan bugi kafadarsa "ammiey yadai tunanin me kikeyi haka?inace tunanina kikeyi?kuma gani a kusa dake umm?"ya kashe mata do,
Lumshe ido tayi kwallar data makale a idonta ta sulalo "babu yadda zaayi zuciyata ta gushe ta mance da yar uwata jinin jikina ina sonta ina kaunarta mutuwa tai mana yankan kauna ya zaaiyi inyi rayuwa batare da na tunata ba?....idan banyi tunaninta ba wa zanyi?kai zanyi tunani kuma inada tabbacin nice farin cikin mijina yana sona fiye da komi a duniya to alhamdulillahi"mikewa tayi tsaye yabi ta da kallo sket da rigar atamfa ne jikinta sun matukar karbar jikinta tamkat bata haihu ba,tasa hannu ta share hawayenta kanta babu dan kwali tayi hanyar fita ya kira sunanta a kasale "hanan"juyowa tayi kamar bazatace wani abu ba sai tace "bari in duba abinci a kitchen dikda nace safiya ta duba amma nasan sunacan tare dasu afee da meenah suna wasa dasu hanan kuma naga afee ayshmah tazo shiyasa na kyaleta da ita zata duba"ta karashe maganar idonta cikin nasa yana hango kwalla cike, tausayinta ya kamasa ya gyada mata kai alamar taje,
Kallon agogo yayi yaga karfe biyar da rabi na yamma yw cire hular kansa ya aje gefen gado ya kwanta rigingine ya kurawa ceiling din dakin ido......murmushinta shine abinda yake gani ji yayi tamkar an bude kofar dakin da sauri ya juya janan ce tsaye sanye da doguwar rigarta blue kanta yasha kitso tana sakar masa murmushi....lunshe Ido yayi gabansa na faduwa ya bude idon xaiyi magana ta karaso kan gadon ta hayo saman gadon ya bude hannuwansa ya kai mata cafka yaga ta bace masa batttt zumbur ya mike yana waige waige bega kowa ba yayi saurin karasawa jikin kofar ko zai ganta harda lallekawa amma bega kowa ba hakan yasa ya bude kofar dakin ya fice direct sashin janan marigayiya ya nufa da sauri bayan ya wuce su afee a parlor suna gaidasa ko sauraronsu beyi ba ya shige dakin ya rufo kofa....
********
Tsaye take cikin kitchen tana zuzzuba abinci a flask tana gyarawa ta rufe ta ajiye a gefe ta juyo da nufin kai zobo fridge ta ganta tsaye jikin fridge din tana mata murmushi...rufe ido Hanan tayi gabanta ya tsananta faduwa zucuyarta yadda take bugawa tamkar zata fasa kirjinta ta fito lokacin baya ta tuna wata rana suna hada abinci tare a kirchen hanan je zobo janan ta mika hannu ta karbi rariyar da take tace zobon tana faraa tace "best sis kin manta kince kinfison in rinka hada miki zobo kinfi son nawa?"
YOU ARE READING
TAK'ADDAMA
Historical FictionHilal Ina fatan wanan fadace fadacen da mukeyi a tsakaninmu ya zamo iyakarsa cikin gidan iyayenmu,baa gidan aurenmu ba saboda Ina matukar tsoron wanan fadan da mukeyi Kar ya kawo sanadiyyar tarwatsewar farin cikin mu,kada hakan ya kasance sanadiyyar...