💔 *TAK'ADDAMA....* 💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_Albishirinku masoya Ina kuke ku fito ga wata Dama ta Kara samuwa kungiyar nan Mai albarka *HASKE WRITERS ASSO* ta kara yunkuro muku da sababbin littafai Wanda tayi wa lakabi da DA D'UMI D'UMINSU SHIDA GARABASA AKAN NAIRA DARI BIYAR KACAL TARE DA HAZIKAN SHAHARARRUN MARUBUTAN NAN DA KUKA SANI KO KUKEJIN LABARINSU ZASU ZO MUKU DA LABARAI CIKE DA NISHADANTARWA DA FADAKARWA SUNE KAMAR HAKA,
JIDDAH ALIYU👉🏻 *GIDAN RINA*
AISHA DAN SABO👉🏻 *BURIN ZUCIYA*
KHADIJA AHMAD KDEEY👉🏻 *DA* *CIWO A ZUCIYATA*
RAHMA NALELE👉🏻RAYUWATA
SLIMZY👉🏻 *IZZA TA*
SAFIYYA GALADANCI👉🏻 *TANA K'ASA TANA DABO* GA MAI NEMAN KARIN BAYANI YA NEMI WANAN NUMBERS DIN 08166177830 KO 07084161619.....Ina muku fatan alheri masoya.... *SLIMZY CE* ✍🏼*29*
Rike take da carbi bayan sallar laasar tana lazumi taji motsin shigowarsu abiey da iyalan gidansa shafa adduar tayi ta Mike ta ninke daddumar sallar ta dire Akan gado ta bude kofa ta fito direct inda take jiyo hayaniyar ta nufa babban parlorn gidan inda kowa yake zama idan yazo da sauri afrah kanwar sudais Yar budurwa girman afnan ta Mike da gudu ta rungume ummu tana dariya,itama dariyar takeyi ta shafa bayanta "afrah mutanen London yaushe a gari?"
"Ummu jiya nadawo munyi hutu nace ni gaskiya inaso inzo inganku Ina afee?"shafa kanta tayi "kinyiwa afee wayau ai kin rigata tafiya makaranta itama yau kwana hudu kenan da tafiyarta tana kaduna"sakinta tayi ta ruko hannunta suka karaso cikin parlorn inda ake zazzaune and Hira,
Kallon da abiey keyiwa ummu yasata Shan jinin jikinta musamman yadda taga yasha mur tamkar Bai taba dariya ba dikda tana jiyo sautin muryarsa daga daki,
"Barkanku da zuwa yaayah..yau"zatayi magana ya daga Mata hannu "rike gaisuwarki bana bukata da nasan cewar afrah zata gaisheki Dana hanata tunda bake kika haifar min ita ba"....tsittttt parlorn yayi Jin abinda abiey yace ,jikinta yayi matukar sanyi dakyar ta hadiyi miyaun bakinta saboda takaicin abinda abiey yayi mata cikin Yara "abiey meyayi zafi Haka da har zaka furta irin wanan maganar"
"Dakata mun ba wurinki nazoba wajen uwata nazo induba lafiyarta Dan ita kadai gareni babu abinda ya shafeni da huruminki tunda abinda kika zaba kenan kin zabarwa yarinya zaman gida itaba bazawara ba ita ba matar aure ba ko Allah akayiwa laifi Yana yafe Mana balle ke banza a banza"...da sudais da ya Umar mikewa sukayi sukabar parlorn saboda rashin dacewar zamansu anayiwa ummu fada a matsayinta na mahaifiya a garesu tunda kanwar babansu ce,
"Kayi hakuri Dan Allah ka gafarceni kayafemun"
"Wallahi sai kin sauke kambun da kika daura zamu yafe Miki tunda ke kafaffiya ce shasha Sha".itadai hajajju tunda ya Soma magana batace komiba Saida ya dire itama ta karba "in bandake shasha Sha ce wake wulakanta Dan uwansa a gaban wani?wanin ma surukinsu ki watsa musu kasa a ido ki nuna Basu Isa dake ba?...Nima shiyasa nasa Miki Ido ki yanka Hanan kisa a tukunya ki dafata tunda ke kika haifeta Babu me hanaki " sunkuyar da Kai ummi tayi batare da tace komiba uncle nasir ya Mike ya ruko hannun afrah saboda haushin ummu da yakeji ya fice ko kala bece musu ba,
Shima abiey hirarsa ya cigaba da Yi da hajiya sanan sukai sallama ya tafi ko ta Kan ummu be sake bi ba,..hajajju ma mikewa tayi Tai dakinta akabarta ita kadai a parlor....
**********
"Ki daure kici abincin nan Hanan kada yunwa da damuwa da mugun kishi irin naki ya kada ke a banza ita tanacan tana walwala ke kina nan Hanan wallahi yarintarki tayi yawa na rasa yadda zanyi dake"Shesshekar kuka Hanan keyi "maman samha bazaki Gane yadda nakeji a zuciyata ba baza Kuma kigane yadda na tsani kishiyaba,bazaki Gane yadda nakejin radadin ciwo a cikin zuciyata ba dangane da kishiya da hilal yayimun kishiyar ma da kanwata wadda muka taso gida daya gado daya muke kwana,abinci kwano daya mukeci,tare muke zuwa makaranta,tare muke Komi hatta Kaya iri daya muke sawa kamar Yan biyu yanxun in wayi gari nida ita muna gogayya a gida daya a matsayin kishiyoyi?dik wani sirri nawa janan tasanshi Zan iya fada Mata Komi dangane da rayuwata...maman samha ya bazanyi kuka ba?kuka ya zamemun wajibi a cikin wanan karnin Dana tsinci kaina Mafi kaskanci"...da sauri maman samha ta rufe bakinta tausayin Hanan ya lullubeta ta rungumeta jikinta tana jijjigata ga wani zafi da jikinta yayi tamkar wuta..."nasani Hanan akwai zafi da ciwo Amma ya zama Dole ki koyi juriya da tawakkali ki koma koyi jajircewa ki kwaci kanki wajen Miji idan ba Haka ba Zaki zama Yar kallo....Hanan zama da kishiya abune me wahala musamman wadda kika sani tasan sirrinki Dole Zaki fuskanci kalubale kala kala,idan kin daure kin iya siyasa kin iya makirci shikenan idan Baki iya kissa da makirci ba to kullum sai kinyi hawaye"d'ago Hanan tayi ta share Mata hawaye "ki bude kunnuwanki da kyau ki saurareni kiji abinda Zan fada Miki Hanan idan kinji zaiyi Miki amfani za Kuma ki zauna lafiya ke da kanki Zaki kirani kiyimun godiya"gyada Mata Kai tayi hade da zuba Mata fararen idanuwanta da sukai zuru zuru...numfasawa maman samha tayi sanan ta daura da "babban abinda kesaka kishiya ta Raina mutum shine idan tayi Abu a gabanki Dan kiji haushi sai kika nuna kinji haushi kika nuna kishi to ta gama dake harabada idan har zatayi Abu ki basar ki kamar bakisani ba toh kin zauna lafiya sanan ki tabbatar da kin iya kwarkwasa kin iya yanga a gaban Miji uwa uba shagwaba Babu abinda namiji yakeso sama da shagwaba to kin Gama dashi ta wanan fannin ta fannin kwanciya Kuma ki tabbatar kinsan sirrin da idan kika Masa zai haukace ki rinkayi Masa shi hakan zaisa ya kaunaceki yaji dik duniya kece on top idan kikace Komi ke zaiyi Miki a kwance to tabbas zai gundura dake ki iya shagwaba sanan ki zama maabociyar Kai harshenki cikin kunnensa kinayi Masa Wasa Koda zaune kuna Hira wallahi sai yaji wani Abu ya taso Masa...Dan Allah Hanan ki rike aurenki da kyau"...Kiran wayar hilal yasa maman samha dakatawa da magana ta kalli Hanan yadda ta furgice ganin Mai Kiran,..daga Mata gira maman samha tayi alamar ta dauka ba musu ta dauka ta Kara a kunne ya sanar Mata da ya shigo Amma be karaso ba Yana Kan hanya sanan ya kashe wayar,
YOU ARE READING
TAK'ADDAMA
Historical FictionHilal Ina fatan wanan fadace fadacen da mukeyi a tsakaninmu ya zamo iyakarsa cikin gidan iyayenmu,baa gidan aurenmu ba saboda Ina matukar tsoron wanan fadan da mukeyi Kar ya kawo sanadiyyar tarwatsewar farin cikin mu,kada hakan ya kasance sanadiyyar...