7

840 60 2
                                    

💔 *TAK'ADDAMA....* 💔

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡

   *SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_

*Wanan shafi na sadaukar dashi kacokan gareku* *BILLY GALADANCI,AYUSHER MUH'D ,UMMI AISHA* *DA MASOYIYATA SOFFY GALADANCI...* *inayi* *muku sonso* *fisabilillahi musamman mommah na...💞💋*

                *7*

gefe guda suka samu wajen karbar gaisuwa inda Yan uwa da abokan arziki sukai tururuwar zuwa wajen hilal Wanda baya iya magana saboda tsantsar damuwa da tashin hankali da yake ciki gefe guda wutar son Hanan na ruruwa cikin zuciyarsa,zuwa yanzun ya sawa ransa cewar Hanan ta tafi ta barsa Dan dik inda ya waiga a wajen karbar gaisuwar mutuwar Hanan akeyi tun Yana ganin abun tamkar almara har yasawa zuciyarsa rasa Hanan harabada ....

  Alhaji abbah mahaifin hilal Yana daga rumfar gefe Yana hangen Dan nasa zuciyarsa ta cika da tsananin tausayinsa cikin kwana uku hilal ya rame yayi Baki tamkar Wanda yayi cutar shekara guda wani abokin alhaji abbah ne yace "ranka ya dade lallai hilal Yana cikin radadin rashin matarsa dubi dik yadda ya rame yayi Baki daka kallesa kasan Yana cikin tsananin tashin hankali allahu akhbar Allah ya jikan Hanan"..kada Kai alhaji abbah yayi tare da amsawa da Amin sanan yayi gyaran murya ya Soma magana "wato wanan lamari na rashi da hilal yayi bashi kadai bane yayi rashi har mu munyi Rashi babba domin kuwa kowa yasan yadda Hanan take ga zuciyoyin jamaa a cikin dangin nan saidai shi zai fimu Jim radadi saboda matarsa ce da yadda suke matukar kaunar juna kaga Dole abun ya damesa"

"Gaskiyane ranka ya dade Allah ya jikan Hanan yasa ta huta"

  "Ameeen alhaji Ibrahim nagode"...

********
Zaune take a kofar dakin gwaggo habiba na zaune gefenta tana ta faman hadin nono da aka tatso suna Shirin fita talla minti minti takan dubi sashen da Hanan ke zaune ta rafka uban tagumi ta kurawa sashe daya ido tana kallo da busasshen hawaye dake kwance a fuskarta tayi zurfi cikin tunani minti minti takan sauke ajiyar zuciya ta runtse idanuwanta da Alama tanajim radadin wani Abu a ranta sosai take tunanin hilal saidai bawani tunani takeyi na tana son ganinsa ba tunani takeyi na yadda ya iya daukar gawaarta ya yadda a tunaninsa cewar ta mutu...dik soyayyar da yake ikirarin yanayi Mata?ko a mafarki Bata taba kawowa cewar hilal zai aikata hakan Akan wani ba balle ita da kullum yake fada Mata cewar bazai iya rayuwa Babu ita ba ,Ashe karya yakeyi tunda ya Sanya hannunsa ya dauketa ya wurgar da ita yayi tafiyarsa ya barta cikin dajin Allah...cije lebenta tayi hawaye na zuba a idanuwanta wata irin tsana ce ta hilal ta dasu cikin zuciyarta lokaci kankani zuciyarta ke Raya Mata ya kamata ta dauki fansa akansa kodan abinda yayi Mata ya kamata ta hanasa zaman lafiyar da sai yayi danasanin zuwansa duniya....zuwa yanzun kukan Hanan ya tsananta harda shassheka....

Gwaggo habiba itace ta taso daga inda take ta karaso Kan tabarmar da Hanan ke zaune ta zauna a gefenta ta dafa kafadarta "yarinya kiyi shiru kidaina kuka kinji?kada wani Abu yazo ya sameki ya zamana mu bamu da maganinsa saboda Kinga dai inda muke rayuwa Koh?"cikin sigar lallashi takewa Hanan magana wadda fuskarta ta jike da hawaye tasa hannu ta goge "gwaggo na rasa yadda zanyi in mance dashi cikin zuciyata?meyasa ya aikatamun hakan bayan dumbin kaunar da yake nunamin ya daukeni da hannunsa yaje ya yasar Dani a bayan gari inda Babu gida gaba Babu gida baya?....gwaggo ada Ina tsananin kaunarsa fiye da kaina Amma yanzun na tsanesa tsana me tsanani sai na haddasa Masa danasani a rayuwarsa"tana Gama fadin haka ta fada jikin gwaggo tana kuka Mai tsanani...itadai gwaggo dik mutuwar zaune tayi tana sauraron Hanan Dan ba hausa ta cikaji sosai sosai ba saidai a kalaman Hanan ya nunar Mata da cewar akwai wani Abu Wanda akayi Mata yasa take wadanan maganganun masu Kama da tabin hankali kuma dik inda Wanda yayi Mata yake to namiji ne kuma na jikinta ne,Dan haka gwaggo taja numfashi ta sauke ta rungume Hanan sosai tana shafa bayanta cike da tausayawa ga jikin Hanan din yayi zafi sosai kamar an Hura Mata wuta "ya Isa kiyi shiru kidaina fadin wanan maganganun dikda ban fahinci me kike nufi ba d'iyata Amma nasan cewar akwai wani mummunan Abu da wani yayi Miki Wanda yasa kike wadanan maganganun me Kama da zarewa kuma dik inda Wanda yayi Miki yake to makusancinki ne"

TAK'ADDAMADove le storie prendono vita. Scoprilo ora