💔 *TAK'ADDAMA....* 💔
*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡*SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_5
Tana shigowa parkorn dik da suke zazzaune abban Hanan ya dubi ummi yace "muje mu tattauna mudawo"...share hawayenta tayi ta kada Kai tayi gaba,ya cewa mutanen dake zazzaune "a gafarceni inaso in tattauna da madam Ina zuwa minti goma Sha biyar"...abban hilal yace "habadai alhaji badamuwa kuje"...yabi bayan ummi ....can bedroom dinta inda babu mutane nan ya sameta zaune gefen gado Shima ya zauna jikin side drawers na gadon,shiru sukayi wajen minti biyu sanan ya furzar da iska yace "ummin Yara kinsan dalilin da yasa na kirawoki mu tattauna kafin mu Yankewa yaron nan hukunci?"
Kada Kai tayi "ah ah Abba sai ka fada"
"To a gaskiya kaina ya kulle ga wanan lamarin na rasuwar yarinyar nan Hanan domin dai ni banida abin cewa banaso kuma a tozarta zuriar gidan alhaji abbah kinsan yadda muke kuma kinsan yadda mutumin nan yake a garin nan"...
"Haka ne alhaji,kayi magana me kyau gaskiya dikda ni kaina dazun kanwata ta gama yimun magana akan kada mu yarda da kisan Hanan Amma jinta kawai nakeyi saboda Ina tunanin yadda zamu kwashe,Amma ni a ganina abbah mu hakura mubarwa Allah maganar mutuwar yarinyar nan saboda kaga dai alhaji abbah babban mutum ne a garin nan kaf garin nan babu Wanda besan shi ba ya taka mukamai daban daban sanan yanzun haka Yana kan takawa sanan babu Wanda zaija da shi kaf garin nan wajen dukiya ko mulki su kansu hukumar da zamu mikawa lamarin a karkashinsa yake,Banda wanan Kai kanka kasani komi namu a cikin dangi alhaji abbah ne hatta da karatun yaranmu shine Kai kanka a karkashinsa kake aika yake taimaka Mana yake rufa Mana asiri kaga mazamu saka Masa da hakan mu wulakantasa mu tozartasa a idon duniya ba kawai mu yafe ayi shiru da maganar"
Shiru abbah yayi Yana tunanin maganganun ummi masu dauke da tsananin hikima a cikinsu tabbas dik abinda ummi ta fada gaskiya ne Amma babban tashin hankalinsa ya zaayi ya fitowa da uwar yarinyar nan ainihin abinda ya sameta?....yanzun bashida matsala da mutanen gari Dan yasan bakowa yasan cewa ummi ba ita ta haifi Hanan ba to danginsu fa?"...ummi kallonsa tayi tana karantarsa tamkar tasan abinda yake tunani ta cigaba da magana "ka kwantar da hankalinka abbah inhar akan maganar jamaa da na jikinmu da sukaji labari ne,ni a ganina kawai yanzun tunda shi hilal din dama ya tafi nemanta zaa sanarwa da mutane cewar gigicewa ce tasa yace shi ya kasheta saboda dukan da yayi mata anga gawaarta asibiti tunda dama danginka babu Wanda yasani sai gidan alhaji abbah ni kuma Yan uwana ne kadai suka sani sai mu rufe bakin mutane cewar gobe zaa karbi gawaarta ayi mata sutura inyaso karka sanarwa da danginka mutuwarta sai bayan anyi mata sutura inaga hakan zaifi"tunda ta fara magana yake kallonta har ta gama mamaki yakeyi irin hikimarta da yadda take tsara magana lokaci daya batare da ta samu lokacin tunanin hakan ba,
.sai yanzun abbah yasamu kwanciyar hankali da kalaman ummi wata ajiyar zuciya ya sauke "Allah yayi miki albarka ummi hakan zaayi gaskiya naji dadin wanan shawarar taki kuma nagode kuma insha allahu bazamu fasa bibiyar neman gawar Hanan ba har nan da wani Dan lokaci Allah ya saka Miki da alheri""Ameeen "shine abinda tace tunda akai rasuwar nan hankalinta yake a tashe tunanin halin da zasu fada takeyi idan har sukace zasuyi takaddama da mahaifin hilal ita Bata shirya wata rayuwar kunci ba dikda ciwon da takeji na rashin Diya kamar Hanan ...
"Muje Koh"babu musu ta Mike tabi bayansa....
Shiru parkorn yayi kowa Yana sauraron hukuncin da abban Hanan zaiyi musamman alhaji abbah Wanda gabaki daya bashida wata natsuwa a tare dashi dauriya ce kawai da jarumta irin ta maza Amma a zahiri yafi hajiya Aisha tashin hankali....gyaran murya abban Hanan yayi ya Soma magana cikin natsuwa da hikima "farko saidai muce innalillahi wa innah ilaihi rajiun dangane da wanan mummunar kaddara data Fado Mana kuma Allah yafimu sanin dalilin da yasa ya sauko Mana da ita Dan haka dukkan musulmim kwarai Ana expecting dinsa da yayi Imani da kaddara mai kyau da Mara kyau"...duka parlon suka hada Baki "haka ne"...abbah ya cigaba da magana "Dan haka nayi shawara da uwar yarinyar nan akan abinda mu muka gani shine mu rufe maganar nan imu imu Dan kobabu komi hilal Dan mu ne halak malak Dan haka ko wani waje yaje wanan tsautsayin ya samesa sai inda karfinmu ya Kare balle kuma ni a matsayina na uba a gareshi in Mika shi hukuma badai niba tunda alamu sun nuna ba dagangan ya aikata hakan ba Dan haka ni uban Hanan a madadina Dana yan uwanta da mahaifiyarta min yafewa hilal kuma Wanda sukaji maganar zaa sanar musu da ansami gawaarta...Yan uwa da basu saniba zuwa gobe zaa sanar musu da ta rasu anyi Mata sutura shine hukuci da shawarar da muka yanke"....tsittttt parlorn yayi babu Wanda yayi magana na wani lokaci kafin abban hilal Wanda jikinsa yayi sanyi ya fada duniyar tunanin Anya akwai irin wadanan mutane a wanan duniyar masu cike da Imani da kaddara haka?wadanda sukasan halarci kamarsu?yar mutum suka rasa ba yar tsana ba ko wata dabba Amma sukai tawakkali da wanan babban rashi domin rufin asirin zuriarsu?shikam bashida wani Baki da zaiyi amfani dashi wajen godewa wadanan bayin Allah...hajiya Aisha mahaifiyar hilal wadda tunda abbah ya Soma magana ta Soma zubar hawaye har ya gama nan da nan kukanta ya tsananta jikinta yayi sanyi....
"Hakika alhaji banida wata kalma da zanyi amfani da ita wajen gode Maka na karemun martaba da mutumcina da zai zube daga idanun duniya,da kuma Kare mana zumunci da bacin suna da zuriarmu da danginmu da zatayi nagode Allah ubangiji ya saka Maka da alheri Allah ubangiji ya bayyana Mana gawar yarinyar nan da gaggawa alhaji nagode",cewar alhaji abbah Wanda ke magana jiki a sanyaye tamkar an zare Masa lakka dan be taba tunanin wanan halarcin zai sameshi cikin wanan duniyar ba...
Share hawaye hajiya Aisha tayi idanuwanta sunyi jajir "bansan da kalmar da zanyi amfani wajen godewa wanan halarci da kukai mana ba"...da sauri ummi ta karbe zancen "haba hajiya Dan Allah kubar wanan maganar jini daya muke tare daku bazamuso muga abinda zai taba mutumcinku da bacin sunan ku ba tamkar mu akayiwa kuma hilal inda dagangan ya kasheta bazai kawo kansa ya tonawa kansa asiri ba Dan haka Allah ya Kara rufa Mana asiri"...
Muhammad abokin hilal kansa jikinsa ya mutu da wanan halarci da aka nunawa abokinsa ..da kyar ya gyara zama yayi gyaran murya "zanyi amfani da bakin babban aminina wajen yin godiya akan wanan halarci da abbah da ummi sukai Mana Allah ya saka da alheri"...
"Ameeen suka hada Baki"...hilal kallon abin yakeyi tamkar a mafarki ganin dik abinda yake faruwa yakeyi tamkar wani Shirin film hatta da kalaman abbah gani yakeyi tamkar Wasa abbah yakeyi ba gaskiya bane ya kasa natsuwa dik ya firgice besan lokacin da ya saki wani kuka Mai ban tausayiba cikin parlorn Wanda shi kansa abban Hanan dik dauriyarsa Saida ya zubda hawaye na tausayin hilal...wani mugun kallo momyn hilal ta watsa Masa Mai cike da tsana da jin hashi,ji takeyi tamkar ta Mike ta shake shi Dan takaici Dan hilal yayi babban ganganci da wawta akan abinda ya aikata tamkar wani mahaukaci kuma ta kudiri aniyar sai sun nuna Masa kuskurensa Dan bazaici bulus ba,...Muhammad ne ya rukosa Yana lallashinsa ya kasa magana da zarar ya bude Baki zaiyi magana sai kuka ya taso Masa haka aka Gama zaman yaron wajen hilal ya kasa fadin komi har aka watse Muhammad ya kamasa ya nufi mota dashi Dan ya kaisa gida....
*********
A gida Muhammad ya saukesa ya nufi nasa gidan yasa Kai ya shiga cikin gidan...ta kofar kitchen ya tsaya cakkkk numfashinsa na kaiwa da komowa sakamakon hango Hanan da tayi sanyi da wando jeans ya kamata da jar Riga body hug ta Kama gashinta da Jan ribbom tana famar gugar sink din wanke wanke ...ya dade tsaye kafin ta juyo tana murmushi tace ",yaushe ka shigo?yau bakayi dare ba?ni dik na gama sa Rai da sai tsakar dare zaka shigo"tai maganar a shagwabe...a hankali yake takawa har cikin kitchen din inda take Koda ya karasa ya bude hannunsa ya Kai Mata runguma da karfi ya fadi kasa mummunar faduwar da ya buga hancinsa da bakinsa kasa....take yaga taurari nayi Masa yawo ya runtse idanuwansa saboda azabar da ke ratsa sa Yana ambatar sunan Allah kusan minti biyar sanan ya bude idonsa jini na diga daga hancinsa ga azabar da bakinsa keyi Wanda ko baa fada Masa ba bakinsa ya fashe...hannu yasa ya tabo bakinsa ya dubi hannun nasa nan ma yaga jini....besan lokacin da ya Soma kuka wiwi tamkar mace ba....fuskarsa jike da hawaye ya dago ta daidai kofar store din kitchen din nan ma Hanan ya gani tsaye tana kallonsa tana hawaye.....*Ku biyoni Dan ji ya turka turkar nan zata kasance...somin tabi kenan ko ya zata kasance oho...Allah sarki Hanan ko gawaarta na wata duniyar oho...😒*
*SLIMZY CE✍🏼*
YOU ARE READING
TAK'ADDAMA
Historical FictionHilal Ina fatan wanan fadace fadacen da mukeyi a tsakaninmu ya zamo iyakarsa cikin gidan iyayenmu,baa gidan aurenmu ba saboda Ina matukar tsoron wanan fadan da mukeyi Kar ya kawo sanadiyyar tarwatsewar farin cikin mu,kada hakan ya kasance sanadiyyar...