15

787 57 2
                                    

💔 *TAK'ADDAMA....* 💔

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡

   *SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_

   _Wanan shafin naki ne_ *BADIYYA* *ABDULSAMAD* ( *bissamard* ).. _d'iya ta inayinki nagode sosai da kauna...._ 😍🌹

                   *15*

Abie ne ya sako Kai cikin parlorn bakinsa dauke da sallama,abinda ya ganine ya sashi tsayawa Yana Kare musu kallo Yana cigaba da Bata abinci ita kuma tana karba tamkar wata Yar goye,wata irin razananniyar tsawa abie ya daka musu daga inda yake tsaye ya Kira sunan sudais cikin daga murya hakan yasa suka juyo a razane a tare suka zubawa abie iso hantar cikin Hanan gabaki daya ta kada a furgice take jikinta ya Kama rawa da kyar ta lalubo kalmar "barka da zuwa abie",
Ko ta Kan gaisuwarta be bi ba ya Soma masifa "wani irin rashin hankali ne wanan sudais?zaka zauna da girmanka da komi da hankalinka kana bawa matar aure abinci a Baki?baka da hankali ne?ko an fada muku shariah ta Baku damar yin hakan ne?ai ba muharraminta kake ba balle kayi hakan ba huruminka bane Dan haka kar insake ganin wanan Barnar a cikin gidan nan yanzun da badan Allah ya jeho ni ba shikenan haka zaka tasa matar mutane kana Bata abinci a baki,ke kuma da yake sokuwa ce yarinta na yawo a kanki kika saki Baki kina karba ko?Koda yake Baki da laifi ko kadan game laifin nan shugaban marasa hankali,to insake ganin hakan"shafa kansa sudais yayi kalaman mahaifinsa sun matukar taba Masa zuciya Amma yasan gaskiya ya fada,shi sammm mantawa yakeyi da Hanan tana da wani aure akanta...Dan tsaki yayi ya dire cokalin dake hannunsa ya dubi ya Umar dake ta zare ido Yana jiran nashi fadan daga abie,"muje side Dinka man"abinda sudais yace kenan yayi gaba Umar ya take Masa baya abie ya watsa Masa muguwar harara...

Muryar abie ce ta fito da ummu daga daki hannunta rike da carbi tana sanye da hijabi blue da Alama sallah ta idar ta fito parlorn,"yayah muryarka naji sama sama fa meke faruwa?Allah Allah nakeyi infito inji abinda ya faru naji kamar da Yara kake fadan".

"Nida sudais ne Mana na shigo na taddashi Yana bawa Hanan abinci a Baki saikace muharraminta bayan da aurenta saboda rashin hankali,mtseww karki Kuma barinsu tare da ita plsss saboda tana da aure kar suyi abinda zaa raba Mana zunubin Basu kadai ba Dan Naga alamar basuda hankali ko kadan"

"Kayi hakuri yaayah Dan Naga yayyinta ne shiyasa Kuma Hanan din Babu yadda banyi da itaba Taki karbar abincin taci to ganin Umar da sudais din yasa na bar musu su lallabeta su Bata"

"Kardai ki Kuma Dan ba muharramanta bane na fada Miki,....Ina hajajju ne?wlhy daga cikin gari nake na tsaya phermacy na karbi Mata maganinta dik a gajiye nake ga yunwa. Da nakeji wlhy dakyar nayi driving zuwa gidan nan wallahi nayi danasanin kin daukar driver ya kaini",

Zama tayi kujerar dake fuskantar tasa "Aiko hajajju ka manta ita da afnan sunje Zaria bikin Yar kaninta autansu?sunacan jiya suka tafi sabiu driver ya kaisu gobe zasu dawo Wai ,...Amma akwai abinci Bari insa zubaida ta kawo maka farar shinkafa ce da miyar kaza da zobo mukayi"...kwantar da kansa yayi jikin kujera "a zubomun kadan inci sudais ya bar motarsa a nan ya ja tawa mutafi gida",

Kallon inda Hanan tayi tsumu tamkar kazar da ruwa yayi Mata duka kanta na kasa tana Wasa da yatsunta kamar daga sama taji muryar ummu nayi Mata magana "Hanan jeki zubaidah ta hadawa abie abinci ki kawo Masa yi sauri wucewa zasuyi yanzun",.

"Toh ummu"tace ta Mike cikin sauri har tana hardewa tayi hanyar kitchen....

*********
Cikin kankanin lokaci Muhammad ya iso asibitin garkuwa ya Parker motarsa da sauri ya fito ya Kira securities dake gate ya ce "ku taimakeni mu kamashi mukaisa emergency bana bukatar akawo wani Abu don gungurasa saboda Bata lokaci ne"Aiko take wani security da ke da kiba ya sunkuci hilal yayi cikin asibiti dashi Babu alamar numfashi a tattare dashi nurses na ganin haka suka rufa mishi baya daya daga cikinsu ta ruga Kiran likita..ko kafin Muhammad ya karaso likita ya Shiga emergency ya rufo kofar ,Muhammad ya Shiga tura kofar Amma inaaaa ya datse kofar ,durkushewa yayi a wajen ya dafe kansa Yana ambatar innalillahi wa innah ilaihi rajiun..."hilal kada kayi sanadin rayuwarka ka taimaki kanka da iyayenka"ya runtse idanuwansa Yana adduoi kala kala,ganin zaman bazaiyi Masa ba ya Mike tsaye ya Shiga sintiri cikin ward din kusan minti talatin sanan yaji alamar zaa bude kofar da sauri ya karasa  jikin kofar ya tsaya likita ne ya fito dik yayi zufa "yadai likita yanada Rai ko?"..kallonsa likitan yayi jimm kadan yace "biyoni office Dina"...Babu musu yabi bayan likitan....

TAK'ADDAMAOù les histoires vivent. Découvrez maintenant