32

1.2K 73 21
                                    

💔 *TAK'ADDAMA...💔*

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( _Home of expert and perfect writers)_

          *SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_

  _Assalamu alaikum zuwa ga readers makaranta_ *TAK'ADDAMA*... _jiya page Dina na kasa nayi magana Akan me son ya_ _siyi_ *DA D'UMI D'UMINSU* _ya bi number da na rubuta sai mutane suke tunanin na_ _maidashi na kudi ne akai ta biyoni to ni ban maida_ *TAKADDAMA* _na kudi ba littafan mu shida Akan 500 nake magana Wanda nasan kunga advert_ _dinsa...nagode._ *SLIMZY✍🏼*

                  *32*

Rungumarta yayi sosai ya matseta jikinsa Yana shafa bayanta tana cigaba da hawaye,jikinta yayi Sanyi matuka da kalaman ummu ta tabbatar cewar dik abinda mahaifiyarta tayi Mata tayi ne badan Bata Sonta ba Ashe tanayi ne don ta kwatar Mata yancinta yadda bazai wulakanta ta ba,

Kukanta ne ya tsananta yasa hilal sassauta rukon da yayi Mata ya d'ago fuskarta Yana kallonta Yana kada Kai alamar ta daina kuka,cikin shasshekar kuka ta Soma magana "hilal dik biye maka da nayi na sabawa mahaifiyata bawai nayi hakan bane don banajin maganarta,...giyar soyayyarka ce ta jawo hakan da tausasan kalamanka da sukai tasiri a zuciyata su sukai tasiri wajen karyamun zuciya...Abu daya Zan rokeka shine Dan Allah kada ka wulakantani hilal"toshe Mata baki yayi ya rungumeta jikinsa tausayinta ya kamashi ya Shiga shafa bayanta a hankali cikin tattausar murya "is ok hanee kiyi shiru banaso in sakejin kalmar wulakanci a bakinki inhar nine Wanda ya faru a baya kaddara ce ta Riga fata ta sa mukai nisa da juna wanan karon bazamu taba rabuwa ba sai mutuwa insha allahu Babu abinda zai Shiga tsakanina dake umm?ki kwantar da hankalinki"ya d'ago fuskarta har yanzun hawaye ke gudu a idanuwanta yasa harshe Yana lashe hawayenta a hankali Yana shafa kanta,...ajiyar zuciya ta sauke ya kwantar da kanta  a kafadarsa Yana shafata.....

   Misalin karfe uku da minti arbain suka shigo garin kaduna inda motocinsu sukai jerin gwano a titi alamar hayaniya yasa Hanan farkawa daga baccin daya dauketa a kafadar hilal ta d'ago Kai ta ce "mun iso kaduna ne?"gyada Mata Kai yayi,

Wata faduwar gaba ta tsinci kanta ciki wadda batasan dalilinta ba batasan meya haifar mata da hakan ba zuciyarta ta Shiga harbawa sauri da sauri...kwantar da Kai tayi tana ambatar sunayen Allah a zuciyarta idonta na Kan glass tana kallon waje,dik inda sukabi sai taga Komi ya canja mata,watanni tayi Amma sai taga tankar shekara d'aya tayi rabonta da garin....satar kallonta yayi yadda take kallon waje yasashi murmushi kawai ya maida kansa gefe,

  Karya kwanar Yan majalisu sukayi hanyar gidansu abbah gabaki daya taji ranta beso ba batasan yadda zatayi ba da momy idan sun hadu watakila ma ko gaisuwarta bazata amsa ba Haka Tai zurfi cikin tunani sai tabata yayi "oya muje Yar kauye sai kalle kalle kikeyi"harararsa tayi batare da tace komiba ta sako kafarta waje excort na rike da murfin motar daya bude , rusunawa yayi ya gaidata Tai murmushi hade da daga Masa hannu,

Kamar Koda yaushe gidan cike yake da mutane shigarsu Abba sashen sa yayi dasu alhaji Mansoor ita kuwa cikin gida tayi tana takawa a hankali tamkar wadda kwai ya fashewa a ciki, maaikatan gidan suka dauki Murna da ihu "oyoyo anty hanee oyoyo anty hanee abinda yajawo hankalin momy da ummi kenan da suke parlor take momy ta Mike cike da faraa tana fadin "Bari inje tarbo diyata Allah sarki haneee tsaye tayi a bakin kofar ganin yadda momy ke washe Baki Babu zato Babu tsammani Bata taba tunanin wanan tarbar ba ruko hannun Hanan tayi wadda Tai tsaye kamar an dasata "haneeen abbah barka barka"sai kawai Hanan ta fada jikinta ta saki wani kuka hade da kankame surukar tata...bubbuga Mata baya momy keyi tana murmushi "ya Isa ya Isa Yi shiru"

Ummi kuwa network din kanta gabaki daya ya dauke Dan tunda taji labarin dawowar Hanan tayi gidan taga yadda zata kasance wani irin kishin diyarta ne ya taso ya tokare Mata makoshi Amma gudun kada a fahimci wani Abu yasa ta kakalo murmushi tana tafa hannu "yanzun hajiya Aisha ai nima kyabarni in rungumi diyar tawa Koh?Kara fa nai Miki sai Kuma kika zarce kika kanainayeta"dariya suka sa gabaki daya dik tunanin momy mgnr ummi ai Wasa ce itako daga kasan zuciyarta tayi,
.share hawaye Hanan tayi ta karasa gaban ummi ta zube kasa da sauri ta d'ago ta tana murmushi "lale barka da zuwa hananuwa Yar abbah....Kai Masha allahu alhamdulillahi nayi matukar farin ciki"ta zaunar da Hanan wadda gabaki daya takejin wani irin nishadi na ratsata na dawowarta cikin mahaifarta cikin dangin mahaifinta wadanda suka riketa da gaskiya da Amana,

TAK'ADDAMAWhere stories live. Discover now