39

906 64 34
                                    

💔 *TAK'ADDAMA....* 💔

*HASKE WRITERS ASSOCIATION*
( *Home of expert and perfect writers)*💡

   *SLIMZY✍🏼*
_Wattpad@slimzy33_

                   *39*

Murmushi kawai janan takeyi tana jin kanta cikin tsananin nishadin da bata tabajin irinsa ba tun bayan rayuwarta da ahmad yau ne rana ta farko da mijinta ya furta mata kalmar soyayya tun bayan aurensu....

Shi kansa hilal ya fahimci hakan,haka yasa yaja hancinta cikin sigar zolaya "sai wani smiling kikeyi kamar wadda akayiwa wata gagarumar kyauta" .dan zaro ido tayi tana yar dariya hannunta rike da wuka "ba dole inyi murmushi inyi smiling ba dan yau ji nakeyi kamar anyimun hajji da umara"

"Saboda mene jann"cikin mamaki yayi mata tambayar,

Ta dago fuskarta ido cikin ido tace"saboda mijina ya furta min kalmar so a karo na farko a rayuwa abinda naketa mafarkin samu kenan abinda zuciyata ke mararin ji daga bakin mijina kaga dole inyi farin ciki"....kifta mata ido yayo shima yana murmushi jikinsa yayi sanyi yana cigaba da kallonta,..

Ganin kallon yayi yawa tayi masa waving yayi saurin kifta idonsa hade da wayancewa,..

  "Bari in kira hanee ta fito muyi aikin nan tare dan ni zan hada coslow din nan a gabanta kartace baninayi ba"

Ruko rigarsa tayi "hilal dan allah ka kyaleta tahuta kaga bata jin dadi babyn mu ne a ciki ka barta dan allah"...

  "Toh naji zanbarta bani salad bowl din in hada"dariya tasa masa hade da mika masa salad bowl,

  Afee tana amfa waya a parlor take jiyo dariya daga kitchen ta dan daga kanta ta hangosu gaban sink suna aiki tare,...girgiza kai tayi cikin takaicin yar uwarta ta Mike tayi hanyar dakinta da sauri....

  Da sallama ta tura kofar tana kwance ta rike kanta tana fuskantar ceiling idonta a rufe tana sauke numfashi "yaya hanee ke kin zauna kina tunani kina kunci da bacin rai koh?"cikin hassala tayi maganar hakan yasa hanan n
Bude idonta a hankaki,ta kafe kanwarta dasu,

"Cikin second daya zaa kwacw miki miji idan har baki farka daga baccin da kikeyi ba yaya hanee wallahi bazan taba bari wata ta kwacemun ya sudais ba"..zumbur hanan tayi ta zauna tana kallon afnan cike da mamakin kalamanta kallonta takeyi daga sama har kasa shekararta goma sha takwas take furta baxata bari a kwace mata miji ba,wai yaushe afee tasan irin wadanan abubuwan?yaushe ma suka soma soyayya da ya sudais?"

Katse mata tunani tayi "ya hanee ki mike ki marzaye idonki kema kiyi ta yan duniya ki samesu kitchen ayi dake,dan me zakizo kiyita kwanciya kamar ruwa ranki na baci a banza?ai tunda yafurta mata kalmar so to mikewa zaki ki kwaci kanki tun yana da sauran sonki kafin ki zama yar kallo ni kinga tafiyata"afee ta fita cike da takaici ta bugo mata kofar ta bi ta da kallo,...kamar wacce aka tsinara tayi zumbur ta diro daga gadon ta fada toilet ta wanke fuskarta ta fito ta tsaya gaban madubi ta goge fuskarta sanan ta shafa hoda da lip glos ta fito dakin babu dankwali kanta yayo rasss da sabon kitso ta nufi kitchen din...

Dariya sosai suke kyalkyalawa itada hilal hannunsa dik bama wai yana hada salad "kai yaayah tabb gaskiya anya zamuci coslow din nan nida best sis dubi fa hannunka "..daidai nan hanan ta shigo fuskarta rasss kamar ba itaba ta washe baki "ya naji ana cewa bazamu ci coslow ba meyafaru?ina can ina jiran abinci ashe kuna nan komi bakuyi ba"...dariya sosai janan takeyi tana fadin "dubi hannunsa fa yadda yayi dumu dumu da bama inda haka akeyi da baaci ba ni anya zanci kuwa"

Mamayar su yayi duka su biyun ya shasshafa musu a fuskokinsu dukansu suka hau dariya a kitchen,

Shagwaba hanan ta saka "allah ni bazan yardaba sweet sai ka shafamun bama a fuska"ta turo baki,

TAK'ADDAMADonde viven las historias. Descúbrelo ahora