page 1

1.1K 40 1
                                    

•••••••••••••••••••••••••••
             💐💐
                🐚
        🐚🐚🐚🐚
  🐚🐚 ༼۝༽🐚🐚
    💐༼۝༽༼۝༽💐
   *YAN' SARAUTA*
         💐 *1*💐
   🐚🐚🐚🐚🐚🐚
          🐚🐚🐚
               🐚
             💐💐
      ••••••••••••••••••••
*_BROUGHT TO YOU BY DANCING FINGER TEAMS_*

*🙋_NA HAJJARA MAMI NATTYGIRL_💃*

'''whattpad @ hajaramami20.'''
       
'''wordpress@ hajarafalalumuhammad.wordpress.com'''


******
Iya karshen motan ta Kai tana tsala gudu Bata San su kamo har ya Kai ga sun Sha gabanta Bata San komawa masarautar data auri *YARIMA KHALIL* gara ta gudu tabar Musu sarautar suba Wanda suke so,.
   Babban motan dake tahowa tana Mata horn tun daga nesa Amma Bata ji ba saboda tana juyawa baya tana duba masu binta sai ganin ta tayi dab da motan hakan yasa garin ta kaucewa motan ta fada jejin dake gefenta motan ta bugi da wata bishiya, motocin dake binta suka tsaya, wasu ne da Kaya irin na gidan SARAUTA suka fito hankalin su tashe sukai wajen motan,.
Wata wadda Naga kayanta yadan ban banta Dana sauran matan ta nufi gun bayan an bude motan suka dakko ta kanta na zubar da jini...........

    ******
Safa da marwa yake a Babban parlor shima baya San kanwarshi ta auri YARIMA KHALIL Allah yasa ta Samu ya tsere musu fatan shi kenan,.
  Wani dogarine ya Shiga parlor ya zube kasa ran sarki ya dade an Samu damar dakko *SARAUNIYA KAUSAR* Amma ta hadu da accident yanzu haka suna asibi, baice komai ba ya fice dogarin ya mike yabi bayanshi da gudu ,.

Yana fita Wanda suke waje suka zube suna kwasar gaisuwa ko ta kansu Bai bi ba ya nufi mota ko baa cewa driver Ina zaa je ba sun sani kawai gate suka nufa, motaci biyar suka bi bayan su, gates wajen bakwai suka bi sannan suka samu damar fita daga masarautar

YAN SARAUTAWhere stories live. Discover now